Daga Mazhun Idris
Wasan paintball ko kuma na na harba kwanson fenti na kara samun karbuwa a manyan biranen Nijeriya inda mutane da dama ke ci gaba da sanya tufafin kariya domin gudanar da wannan wasan.
A hankali wasan na paintball yana kara shahara a matsayin wasan motsa jiki na nishadantarwa ga mazauna Najeriya, daga babban birnin tarayya Abuja, zuwa manyan birane kamar Legas da Kano.
“Ba zan iya cewa ga lokacin da paintball ya zo Nijeriya ba,” in ji Aliyu Abubakar, mataimakin shugaban kungiyar kwararru masu wasan paintball, wato PPPAN, “sai dai zan iya cewa wasan ya soma bayyana a Abuja a shekarun 2000.
A halin yanzu Abuja na da wuraren gudanar da wannan wasan shida Micah Sunday Joshua, wanda masoyin wasan ne na paintball ya shaida wa TRT Afrika cewa “Paintball wasa ne wanda abokan ‘yan uwa da abokai za su yi nishadi a tare. A shekarun da suka gabata, paintball ya samu karbuwa sosai duk da cewa mutane da dama ba su da masaniya kan mene ne shi.”
Wasan Paintball a Abuja
Paintball dai wasa ne wanda ke kunshe da rukunin ‘yan wasa wadanda ake ba su wata kwarya-kwaryar bindiga wanda ake kira ‘paintball gun’, wadda ke harba wani kwanso da ke cike da fenti. Idan aka harba, fentin na fallatsa a jikin wanda aka harbamawa.
Aliyu Abubakar mai horas da ‘yan wasan paintball ne kuma shi ne ya kirkiro Shooters Paintball Arena, wanda wuri ne wanda ake wasan paintball a unguwar Wuse da ke Abuja.
“Paintball wasa ne wanda ya dogara kan dubaru. Hanya ce mai dadi ta kwarewa wurin koyon yadda ake tsira wadda ke da dadi,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Ade Abike, wanda shi ne manajan Rabby Recreation Park da ke Life Camp Abuja, wuri ne da ke da akwai wani tsohon wurin wasan na paintball, ya ce “mazauna Abuja suna kaunar wasan paintball inda suke hada kungiyoyi da gasanni”.
“Paintball na taimaka wa mazauna birnin Abuja wurin kara yin atisaye, da kulla kawance. Mutane daga sassa daban-daban suna haduwa domin yin wannan wasan a tare a filin wasa”, kamar yadda Aliyu ya amince.
Filin da ake yin wasan paintball yana bambanta dangane da girmansa, za a iya yinsa a cikin daki ko a waje. Domin kwaikwayon fagen yaki na gaske, filin da ake wasan zai iya kasancewa wuri da ke da akwai bishiyoyi da tsaunuka da ramuka da kuma wasu abubuwan da za a iya ajiyewa kamar su tsofaffin tayoyi da tsofaffin motoci da manyan duro na mai.
Yadda ake wasan paintball
A wasan na paintball, rukuni biyu ko sama da haka na ‘yan wasa suna rufe fuskokinsu da kuma saka kaya masu kama da na soja inda ko wane rukuni ke kokarin ganin bayan dan uwansa ta hanyar harba bindiga.
Wasan wanda ake kira yakin paintball, wasa ne mai dadi sosai inda ake fitar da dan wasa bayan an harbe shi da kwanson fenti, ana bukatar wanda aka harba ya daga hannunsa domin tabbatar da an harbe shi don ya fita ya bar filin.
“Ana jin harbin, sai dai babu zafi sai dai yana barin alamun fenti a jiki”, kamar yadda Aliyu ya shaida wa TRT Afrika.
“Matsakaicin gudun harsashin bindigar na tafiya ne kan gudun kilomita 300 a duk awa daya, ko a ce mita 90 a duk dakika daya, wanda gudunsa bai kai na asalin bindiga mara sauri ba.”
Dokokin wasan sun ta’allaka ne kan yanayin wasan, sai dai ana yinsa ne karkashin ka’idoji masu tsauri dangane da yadda ‘yan wasan ke wasan da kuma amfani da kayayyakin wasan.
A karkashin umarnin mai bayar da umarni a wasan, manufar wasan za ta iya kasancewa kai hari ko kuma kawarwa ko kama sansanin abokan gaba ko wasu boyayyun abubuwa kamar tuta da amfani da taswira da gurneti wanda ke da hayaki mai launi ko kuma bayar da kariya ga wani wuri wanda aka killace.
Lokacin da ake shafewa ana wasan ya danganci irin wasan da ake yi, wanda yake daukar mintoci zuwa awowi, a wani lokacin ma da ake yin wasan a cikin daji akan iya daukar ranaku.
Dokokin wasan
Sakamakon bindigogin paintball na kama da bindigogin gaske, Ade Abike ta bayyana wa TRT Afrika cewa : “Idan ana shirya wurin wasan paintball, ma’aikatan tsaro suna gudanar da bincike saboda tsaro.”
“Paintball wasa ne mai aminci muddun ka bi ka’idojin wasan da kuma amfani da kayayyakin da suka dace,” in ji Aliyu.
“Wasan paintball zai iya zama mai tsada ga wasu mutanen,” kamar yadda wani dan wasan Micah Joshua ya shaida wa TRT Afrika.
“Akasarin kayayyakin wasan paintball ana shigo da su ne. Shi ya sa ake ganin paintball wasa ne na ‘yan boko,” in ji Ade.