Barebari, wadanda suka fi yawa a jihohin Borno da Yobe, sun fara yin kwalliya da hula saƙar hannu tun kafin zuwan injinan zamani. Hoto/Reuters

Saka hula wani bangare ne na al'ada mai daɗaɗɗen tarihi da ta samo asali tun zamanin wayewa ta dubban shekaru da ta samo asali daga Masar.

Asali an samar da ita ne don ta kare mai sawa daga abubuwa, sai dai bayan da zamani ya ja, sai ta zamo wata alama da ke nuna matsayi da aikin mutum a cikin al'umma.

Hulunan gargajiya a arewacin Nijeriya, musamman wadanda Barebari ke sawa, suna da tushen al'adu da tarihi.

Barebari, wadanda suka fi yawa a jihohin Borno da Yobe, sun fara yin kwalliya da hula saƙar hannu tun kafin zuwan injinan zamani.

Musa Kasimu, mazaunin karamar hukumar Tarauni a jihar Kano, ya kwashe sama da shekaru goma yana sana’ar sana’ar “wankin hula”. Hoto/TRT Afrika

Kamar dai yadda aka shafe lokaci ana bin al’adar sanya huluna masu nau'i daban-daban, haka ma aka dauki lokaci ana sana'ar wanke su da kyau su zama kamar sabbi.

Wannan tushe na al'adun gargajiya, a haƙiƙa, ya haɓaka kasuwancin saƙa da ma wankin huluna - waɗanda ke da sunaye daban-daban - kamar Kube, Zanna Bukar da Damanga, da sauransu.

Kasuwanci mai riba

Musa Kasimu, mazaunin karamar hukumar Tarauni a jihar Kano, ya kwashe sama da shekaru goma yana sana’ar sana’ar “wankin hula”.

"Na kasance ina yawan zuwa wurin wankin kaya da suka ƙware sosai a wankin huluna don na haɗu da abokain. Sun karfafa mini gwiwa na koyi wannan sana'ar kuma ta haka ne tafiya ta fara," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Tun da saka hula ya zama wani bangare na al'adunmu, to suna bukatar a dinga kula da su sosai. Marasa ƙarin cikinsu kuwa ana adana su sai a lokuta na musamman, saboda suna son a kula da su sosai.

Huluna kan yi tas su yi ta sheƙi idan an wanke su. Hoto/TRT Afrika

Ana neman masu wankin hula da gogewa sosai. Musa yana cajin tsakanin naira 200 zuwa 500 a wankin duk huka daya, ya danganta da abin da mai shi ke da shi da kuma bambancin hula.

"Ubangidana, Malam Aminu Gyadi-Gyadi ne ya koya min duk yadda ake wanke hula da kyau cikin ƙwarewa. Ya koya min duk wani salo na wankinta da kyau da zai sa a gan ta kamar sabuwa.

A garuruwa irin su Abuja, masu wankin hula suna samun Naira 500 ko sama da haka a kan duk guda daya. “Idan ka samu aiki da yawa, za ka iya samun kudi har N30,000 a mako,” Musa ya shaida wa TRT Afrika.

Haduwa da "mutanen arziki"

Bayan yuwuwar samun kudin shiga, abin da Musa ke so game da tsarin aikinsa shi ne damar saduwa da mutane daga sassa daban-daban.

"Al'adar saka hula da ta muka daɗe da ita, ba ruwanta da mawadaci ko talaka," in ji shi.

Abin ban dariya na kasuwancin wankin hula shi ne yadda mutane da yawa sai ka yi ta tuna musu su zo su dauki kayansu an kammala wankewa.

Wasu sun fi saka hula idan za su wani muhimmin taro. Hoto/Reuters

“Ina da hulunan mutane da aka kawo min wankinsu tun shekara biyar ko shida da suka wuce kuma ba a karba ba. Ban ƙirga su ba amma za su iya kai wa 100," in ji Musa.

"Wasu mutanen ba sa tuna cewa sun kawo wankin hula sai an shafe lokaci idan ka haɗu da su kwatsam sai ka tuna musu sannan suke tunowa. Sannan akwai masu su da suka ƙaura ko suka mutu.

Don haka, idan nan gaba za ku ga wata hula da aka yi mata ado da launuka iri-iri a kan wani a arewacin Nijeriya ko wasu sassan Gabas da Yammacin Afirka, to ku tuna cewa akwai mai wanke ta ya goge tas, a wani wuri daban.

TRT Afrika