Dag Firmain Eric Mbadinga
Burin dan kasuwa Nick Tshikwat na Congo shi ne sarrafawa tare da inganta amfanin gonar da ake nomawa a yankinsu irin su dankalin Turawa da ayaba da doya da sauransu, sannan ya isar da su zuwa ga kasuwannin duniya.
Wannan burin ne ya sa ya assasa kamfanin Nutrimeal NTM, kamfanin sarrafa amfanin gona da suke yin akalla shekara 1 ba su lalace ba.
Kamfanin ya samu karbuwa matuka a garin na Lumbumbashi, wanda shi ne gari na biyu mafi girma a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo. Da farko Nick ya fara aikin jin kai ne da koyarwa, amma a shekarar 2019, sai ya koma bangaren da ya dade yana sha'awa.
A cewarsa, sarrafa abinci wani kasuwanci ne da a gane shi ba sosai, musamman saboda rashin iya kawata shi a cikin leda.
Ya fara aiki ne a wani kamfanin sarrafa amfanin gona, inda ya koyi makamar harkar, da burin ya assasa na shi, domin ingantawa da sarrafa amfanin gonar da aka girbe a yankin.
Annobar COVID-19 ce ta zama silar daukakar kamfanin, lokacin da farashin abinci ya tashi.
"Na dade ina sha'awar bude kamfanin sarrafa kayan abinci. Amma saboda rashin jari, ban fara ba sai a shekarar 2019 lokacin da na samu tallafi daga wani shirin Bankin Duniya.
"Da kayan marmari na fara, musamman strawberry,"inji dan shekara 25 din a zantawarsa da TRT Afrika. Tun lokacin da ya fara, kullum Nick kara samun nasara yake yi saboda kara sanin makamar kasuwancin da yake yi.
Tun a shekarar 2021, kwarewarsa da shirinsa sun isa kai kayan shi zuwa kasuwannin duniya. Sai ya fara sarrafa dankalin Turawa zuwa fulawa domin yin biredi da shi.
"A garinmu na Lumbumbashi, farashin fulawar alkama ya yi sama, wanda hakan ya sa nau'ukan abinci da ake hadawa da ita suka yi tsada. A daidai lokacin kuma, sai ya kasance masu noma dankalin Turawa da ayaba suna takfa asara domin ba su san yadda za su adana su ba," inji shi.
"Don haka sai na gudanar da bincike a YouTube, na hada da ilimin da nake da na samu a kwasa-kwasan da na halarta, inda na fara tunanin mayar da dankalin Turawa ya zama fulawa," inji Nick.
Domin zama na daban, sai matashin ya yanke shawarar sarrafa kayan abincin ba tare da sinadarai masu illa ga lafiya ba, ya kuma kulla alaka mai kyau da manoma.
Ya sa wa kamfaninsa suna Nutrimeal - wanda kalma biyu aka hada da suke nufin abinci mai inganta lafiya. "Taken kamfanina shi ne 'asalin dandano mai dadi," inji Nick cikin farin cikin nasarar da yake samu. Fitaccen marubucin nan na Faransa, François Rabelais ya taba cewa, " Kana jin dandanon abinci ne idan kana cin abincin."
A wajen Nick kuwa, shaukin sarrafa abincin ne ya kai shi ga bude bangaren tande-tande a kamfanin. "Ina hada abinci irin su biskit da biredi da sauran kayayyakin da ake hadawa da fulawa, amma da fulawar dankalin Turawa nake amfani.
Da 'yan kudadensa ya fara kamfanin, sai kuma gudunmuwa daga abokai da 'yan uwa, sannan kuma tun yanzu ya fara cin gajiyar kasuwancin a garinsu mai sama da mutum miliyan 5, inda kuma ake matukar kaunar kayayyakin da ake hadawa da fulawa.
Kananan kayan aikin da ya fara da su ne suka bude masa kofar da zai sayo manyan kayan aiki a yanzu.
Sannan odar kilo 20 na dankalin Turawa da ya sarrafa da aka yi a farkon fara kasuwancin ne ya karfafa masa gwiwa, inda yanzu yake samun odar dubunnan kiloli a duk shekara. Yanzu yana da kwararrun ma'aikata guda gudu.
"Kilo 20 da aka fara saya a wajena an hada wani nau'in abinci ne mai suna waffles, wanda mutanena dama suke jin dadinsa.
Tun lokacin ne mutane suke tambayar ko akwai ko babu," inji dan kasuwar a cikin murnushi. Kamfanin ya raba wa kowane ma'aikaci aikinsa - wani yana kula da tsare-tsare, wani kwararren masanin noma ne da kuma wanda yake kuka da sashin tabbatar da inganci.
Akwai kuma wakilin kasuwanci, wanda ke lura da harkokin ciniki. Akwai kuma wani ma'aikacin komai da ruwanka kamar Nick, wanda yake aiki a sashin tsare-tsare. Haka kuma amfani da fasahar zamani wajen tallata kayayyakin ya taimaka wajen tallata kamfanin a kasashen wajen.
Ma'aikatan kamfanin na dindindin suna samun sauki ne daga ma''aikata na wucin gadi masu yawa.
"Wani lokacin nakan samu tan daya ko biyu na dankalin Turawa. Dole in fere, sannan in mayar da shi fulawa. Wani lokacin dole nake daukar leburori da za su yi aikin wucin gadi.
Na fi daukar mutane marasa karfi a irin wannan aikin," inji Nick. Burin Nick shi ne ya fada kasuwancinsa, ya inganta kamfaninsa da kayan aiki na zamani, sannan ya samar da aiki ga mutanen garinsu.
A shirye yake ya fara sarrafawa fulawa mara sinadarin gluten domin marasa lafiya fa suke bukatar kayansa..