Daga Abdulwasiu Hassan
“Gaskiya na kidime sosai saboda wannan ne karo na farko da na fuskanci ambaliyar ruwa a gona,” in ji manomin na wucin gadi a lokacin da yake zanta wa da TRT Afrika.
Ambaliyar ruwan 2022 ta yi ajalin mutum 665, ta jikkata 3,181, ta shafi mutum miliyan 4.4, ta raba miliyan 2.4 da matsugunansu, ta lalata gonaki sama da 944,000 da illata gidaje 355,000, kamar yadda alkaluman gwamnati suka bayyana.
Jihar Adamawa da Abubakar ke rayuwa na daya daga cikin jihohin Nijeriya 32 da Hukumar Binciken Kimiyyar Ruwa ta bayyana za su iya fuskantar ambaliya a 2023.
Daga cikin jihohin kasar 36, wasu yankuna a jihohi 32 na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa sosai, yayin da wasu yankunan a jihohi 32 za su dan fuskanci ambaliyar kadan, in ji Rahoton Shekara-Shekara Kan Ambaliyar da Hukumar Binciken Kimiyyar Ruwa ta kasar ta tattara.
A kowacce shekara ana samun ambaliyar ruwa a Nijeriya idan aka samu mamakon ruwan sama a lokacin damuna, da kuma idan Kamaru da ke makotaka da Nijeriyar ta saki ruwan madatsar ruwanta ta Ladgo don tsoron kar ta karye.
Duk da cewar ana sakin ruwan madatsar ruwan ne bayan an gargadi jama’a, yana janyo ambaliyar ruwa da barnatar da dukiyoyi a Nijeriya.
Ambaliyar ruwan na iya munana sosai
Ambaliyar ruwan da aka fuskanta a Nijeriya a 2022 ce mafi muni a kasar wadda ta fi ta 2012.
“Maganar gaskiya wannan shekarar ma za a fuskanci ambaliyar ruwa irin ta shekarar da ta gabata ko ma sama da ita”, in ji Mustapha Habib Ahmed, shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya (NEMA) a wajen wani taro kan shirin da ya kamata a yi don tunkarar ibtila’o’in da sauyin yanayi ke janyowa.
A kokarin hana sake afkuwar irin wannan ibtila’i, jama’a da gwamnati sun tashi tsaye suna ayyuka.
Hakan ya sanya a shekarar da ta gabata aka kaddamar da Kwamitin Shugaban Kasa Kan Samar da Babban Shirin Riga-Kafi ga afkuwar ambaliyar ruwa.
Tun wancan lokaci, Kwamitin na Shugaban Kasa ya dinga fadi-tashi a fadin kasar inda yake bai wa mutane shawarwari kan yadda za su hana afkuwar ambaliyar ruwan.
Hukumomin gwamnati irin su na Hukumar Bincike Kan Kimiyyar Ruwa, Hasashen Yanayi da Bayar da Agajin Gaggawa na ta shiri don takaita irin asara da illar da ambaliyar ruwan kan iya janyo wa ga ‘yan Nijeriya a 2023.
Manzo Ezekiel, kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya ya shaida wa TRT Afrika cewa Hukumar na aiki da shawarwarin kwararru kan hanyar da ta fi dacewa don tunkarar ibtila’o’i ta yadda za a rage irin illoli da barnar da za ta janyo.
Ya ce ”Mun rubuta wa dukkan jihohi kan batun illar da ambaliyar ruwan za ta janyo, kuma muna kai ziyarar wayar da kan jama’a a yankunan da aka yi hasashen za a samu ambaliyar ruwan.”
Amma, ba dukkan bayanan wayar da kai na wasu hukumomin gwamnati ba ne suka isa ga kowa.
Kokarin al’ummu na yaki da ambaliyar ruwa
Muhammad Abdulazeez, mazaunin yankin da ke yawan fuskantar ambaliyar ruwa a jihar Kaduna da ke arewa maso-yammacin Nijeriya ya shaida mana yana sauraren rediyo, amma har yanzu bai ji wani bayanin wayar da kan jama’a game da barazanar ambaliyar ruwan ba.
Muhammad ya ce da zarar an fara samun ambaliyar ruwa ne sai jama’ar yankinsa na Kaduna su fara share magudanan ruwa don hana ambaliyar yin barna.
Jama’ar garuruwa kamar Amir Muhammad Hardo da ke rayuwa a jihar Jigawan arewa maso-yammacin Nijeriya da ambaliyar ruwa ta illata a 2022, ya bayyana cewa a yanzu jama’a sun fara kaurace wa yin noma da damuna don gudun ambaliyar da za ta sanya su asarar amfanin gona.
Ba manoman arewa maso-yammacin Nijeriya ne kadai ke da irin wannan tunanin ba, ‘yan uwansu na arewa maso-gabas ma na yin hakan.
Abubakar manomin shinkafa ya shaida wa TRT Afrika cewa “Ba za mu fasa noma ba saboda ambaliyar ruwa, kawai dai muna neman hanyar kalubalantar ambaliyar ko kuma neman wani wajen na daban, ko yin shukar kafin ruwa ya zo ta yadda za mu yi girbi kafin afkuwar ambaliyar.”
Ya ce manoma a yankunansu na Adamawa sun gano yadda ambaliyar ke afkuwa a tsakanin watannin Agusta da farkon Disamba. Hakan ya sanya suka daina shuka a wannan lokaci.
Ya ce ”Abun da muka kudiri niyyar yi ga manoma shi ne a dinga shuka da wuri yadda kafin Agusta, kamar a karshen watan Yuli ko farkon Agusta za a yi girbin shinkafa.”
Ya kara da cewa “Manoman masara, dawa da gero ba sa shuka gaba daya, abun da suke yi shi ne suna jira sai an gama ambaliyar ruwan. Kamar a Nuwamba sai su je gonaki su yi shuka. Suna amfani da yadda ake da ruwa kwance a gonaki a wannan lokaci.”
Manzo Ezekiel ya ce wannan na daga cikin abubuwan da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ke fada wa jama’a a lokacin da suke gana wa da su.
Ya ce suna shawartar mutanen da ke zaune a yankunan da ke fuskantar ambaliyar ruwa da kar su yi shuka da wuri don kar ambaliya ta yi musu asarar amfanin gona, hakan zai sanya su amfana da takin da ruwa zai kawo ya ajiye a gonakinsu.
Muhammad mazaunin Kaduna ya ce ya yi murna da jin rahotannin da gwamnatin jihar ta bayar da kwangilar gina magudanan ruwa da kara girman hanyoyi a yankinsa.
Ana fatan wadannan matakai da gwamnatoci, kungiyoyi da daidaikun mutane ke dauka za su taimaki mutane a kasar da ke Yammacin Afirka ta magance afkuwar mummunar ambaliyar ruwa irin wadda aka samu a shekarar bara.