Bikin Guérouwal yana ba da dama ga Fulani su daukaka al'adunsu.

Daga Kudra Maliro

An soke bikin Guérouwal da ake yi kasar Nijar duk shekara. Bikin ya saba hado kan al'ummomin Fulani, kuma ya yadu zuwa kasashen Afirka da suka hada da Burkina Faso, da Nijeriya, da Chadi, da Kamaru, da Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Al'ummar kabilun Fulani wadanda aka fi sani da kiwon shanu sun watsu a sassan nahiyar Afirka, tun daga Tekun Atalantika daga yammaci, har zuwa Gabar Tafkin Chadi, a yankin Tsakiyar Afirka.

Amma kabilar Wodaabé ta Fulani su suka fi rike al'adar yawon kiwo da fatauci.

Su ne suke jagorancin bikin Guérouwal, wanda a Fulatanci yake nufin "bikin maza matasa na nuna kyau da kwalliya".

Maza matasa sukan yi layi suna waka a bikin Fulani na Guérouwal.

Shagalin na gargajiya don nuna kyau da kwalliya da al'ada, ana yin sa duk shekara a farkon damina. Bukukuwan sun hada da sukuwar rakuma, da wake-wake, da raye-raye.

Sai dai kuma a wannan shekara an soke duk wani babban biki a kasar Nijar.

Aboubacar Yacouba Maiga, shugaban sashen biki da baje-koli a Ma'aikatar Al'adu ta kasar ya fada wa TRT Afrika cewa, "Ba za a yi bikin Guérouwal ba wannan shekara saboda matsalolin kudi. Amma kananan al'ummomi za su yi nasu a yankunansu."

A lokacin bikin, kabilar Fulani suna gasar neman aure, inda maza matasa suke shigar bajinta da kyawawan tufafi, su saka kwalliyar fuska, sannan su yi layi a gaban mata, wadanda za su yi zaben saurayi.

Saka kwallaiyar fuska da sanya tufafin gargajiya su ne babban bangaren bikin.

Mr Yacouba Maiga ya kara da cewa, "Su ma mata sukan samu samarin da za su zabe su, amma sai idan matar ta amshi manemin. Saboda a wajen Bororo (wata kabilar Fulani), ba a yin auren dole, kuma ba a auren hadi. Alhakin macen ne ta zabi namijin da ya yi mata".

Wanda ya yi nasara shi zai samu damar auran matar da ya zaba, tare da amincewar danginsa.

Wannan shagali wata dama ce ta tarayya da juna, da musayar tunani da karfafa dankon zumunci da zamantakewa.

Bikin yana janyo hankalin 'yan yawon bude-ido, wadanda ke fatan kallon wannan biki mai cike da tarihi.

Bikin Guérouwal yana hado kan al'umma bayan makiyaya sun sha fama da lokacin rashin ruwa.

Kamfanonin shirya tafiye-tafiye suna shirya tsarin tafiya ga mutanen da ke son halartar bikin mai kayatarwa.

Ma'aikatar al'adu ta Nijar tana tallafawa bikin kuma tana tallata shi don nuna nau'in al'adun kasar da hada-kan al'umma.

Yacouba ya kara da cewa, "Bikin Guérouwal biki ne na shekara-shekara wanda makiyaya suke yi, kuma aka saba gudanar da shi kusa da mashayar ruwa.

Duk da bambancin da ke tsakanin kabilar Fulanin Bororo da Wadaabe, yana birge ni idan na ga har yanzu ana yin wannan bikin".

TRT Afrika