Daga Mazhun Idris
A matsayinsa na ƙwararren mai ɗaukar hoto, Balarabe uba Abdullahi ya yi suna wajen solon ɗaukar hotunan mutane da abubuwa. Yana nuna fuskokin mutane masu fara'a, annashuwa, kumari, har da masu damuwa, waɗanda ke ba da labaru daban-daban.
Balarabe, wanda aka fi sani da Balancy ya yi shuhura a Nijeriya da wasu ƙasashe maƙwabta, sakamakon aikinsa na ɗaukar hoto. Amma kuma ba abin da yake ƙayatar da shi kamar bibiyar yadda yanayi ke sauyawa a duniya, da kuma alaƙar hakan da rayuwar jama'a.
"Da yawan kwastomomina sukan yi mamaki idan na ce musu ni masanin kimiyyar dabbobi ne," in ji Balarabe, wanda ke da kamfanin Balancy Photography a birnin Kano na Nijeriya, a zantawarsa da TRT Afrika.
Balarabe mai shekaru 43, ya samu gurbin karatu daga gwamnatin Kano a shekarar 1997, inda ya je Masar don koyon aikin ɗaukar hoto. Ya buɗe shagonsa na farko na ɗaukar hoto na ƙwararru a farkon ƙarnin 2000, inda ya samu tarin kwastomomi.
"Ina cikin na farko-farkon waɗanda suka rungumi fasahar ɗaukar hoto ta dijital a arewacin Nijeriya. Na yi zarra a kasuwar arewacin ƙasar tsawon shekaru," in ji Balarabe.
Duk da yana jin daɗin gudanar da aikinsa a matsayin ƙwararre, ciki har da saka amarya ta yi murmushi, ko gyara rawanin basarake, ko saka yaro ya natsu don a ɗauke su a hoto, aikin Balarabe ba a nan ya tsaya ba.
Balarabe ya fi samun farin ciki yayin da yake ɗaukar kyamara a wuyansa, yana ɗaukar hotunan yadda ɗan-adam ke mu'amala da muhallinsa, sama da yadda yake ji yayin ɗaukar hotunan bukukuwan aure ko al'adu.
Kyamara don ceton duniya
Balarabe ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "An haife ni a ƙauyen Bagadawa na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano. Na yi yawo a ƙasashen Yammacin Afrika kuma na ga yadda muhalli ke da tasiri a rayuwar mutane. Ɗaukan hoton muhalli abu ne da nake matuƙar ƙauna".
Balarabe ya gwanance wajen ɗaukar hoton yadda mutane ke rayuwa, da wahalhalun gamagarin mutane a yankin Sahel, da yadda suke fama da matsalar sauyin yanayi. Talauci da rasa matsuguni yana cikin labarun da yake isarwa.
Ɗaya cikin hotunan da Balarabe ya ɗauka ya nuna wata yarinya na ƙoƙarin saka jarkar ruwa cikin kura, bayan ta cika ta a wani rafi. Hoton ya nuna ƙarara yadda al'umma ke fama a yankin da fari ke shafa a Sahel, inda mutane ke tafiya mai nisa don samo ruwa don amfanin gida.
Kyamararsa tana ɗauko hotunan irin yadda al'umma ke rayuwa a ƙasashen Nijeriya, Nijar, Chadi, Kamaru, Burkina Faso, Mali, da Senegal.
Balarabe yana da digiri na farko a kimiyyar dabbobi da kiwo, sa kuma digiri na biyu a fannin kiwon dabbobi daga jami'ar Maryam Abacha American University a Nijar. Yana amfani da iliminsa da ƙwarewarsa wajen ɗaukar hotunan muhalli.
"Ina mayar da hankali kan duk abin da na gani na yadda mutane da dabbobi ke rayuwa. Rayuwar zamani cike take da yadda ɗan-adam ya samu nasarori kan muhalli, kamar gine-ginen tituna da filin fayafayen sola", in ji shi.
Samun shuhura
Balarabe yana samun gamsuwa daga sanin cewa aikinsa yana samun karɓuwa sama da sauran gamagarin masu ɗaukar hoto.
Ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "Lokacin da na ga wani hotona da ke da alaƙa da muhalli an kalle shi sama da sau 10,000 a shafin Google Maps a 2022, na gamsu cewa irin wannan aikin zai iya wayar da kai game da matsalolin muhalli kamar ƙarancin ruwa, tsaftar muhalli, da gurɓatar yanayi".
An nuna hotunansa da ke nuna sauyin muhalli a bukukuwan nune-nune a faɗin duniya, da mujallu, da littattafai, da fina-finai.