Al’ummar Kenya sun gudanar da wani gagarumin gangamin dashen itatuwa a ranar Juma’a domin alhinin wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a baya-bayan nan da ta yi sanadin mutuwar mutane kusan 230 inda aƙalla mutum 200,000 suka rasa muhallansu.
Shugaba William Ruto ya jagoranci wani shiri mai muhimmanci na dasa itatuwa miliyan 200 domin bikin ranar makoki na kasa da kuma daukar matakan kare muhalli.
Hakan na zuwa ne bayan da ya dora alhakin mamakon ruwan sama da aka yi a baya-bayan nan kan sauyin yanayi, inda ruwan saman ya jawo guguwar da ta afka wa makwabciyar kasar Tanzaniya.
Jami’ai da suka hada da ministocin gwamnati da kuma manyan ma’aikatan gwamnati, sun jagoranci kamfe ɗin dasa itatuwan domin gyara dazuzzukan da ayyukan bil’adama suka lalata a baya.
Ruto da uwargidansa Rachel Ruto ne suka jagoranci kamfe ɗin a fadin kasar a dajin Kiambicho da ke gundumar Mùrang'a. Ya ce za a ci gaba da wannan kamfe ɗin na tsawon watanni shida masu zuwa.
“Sauyin yanayi lamari ne na gaskiya da muke rayuwa da shi a kowace rana. Wannan ne ya sa a yau muka dakatar da duk wasu harkokin kasuwanci don dasa itatuwa,” in ji Ruto.
"Dole ne mu nemo mafita dangane da sauyin yanayi kuma mafitar ita ce shuka itatuwa."
Hukumar Tsaro ta Kenya ta ce sojoji sun yi hutu inda suka shuka bishiyoyi sama da 10,000 a barikinsu da ke Nairobi babban birnin ƙasar.
A baya dai gwamnatin kasar ta gudanar da gangamin dashen itatuwa domin kara wayar da kan jama'a game da bunkasa dazuzzukan Kenya da ke fama da ƙarancin itatuwa. Amma ba a taɓa sanin ainihin adadin bishiyoyin da aka dasa ba.
Ministan cikin gida Kithure Kindiki a ranar Juma'a ya ce za a saka sauyin yanayi a cikin jerin abubuwan da ke barazana ga tsaron kasar da suka hada da ta'addanci.
"Muna kallon sauyin yanayi a matsayin ɗaya daga cikin barazanar tsaro ta ƙasa. Dole ne mu sake dawo da martabar muhallinmu ta hanyar dasa isassun itatuwa domin ci gaban muhalli," kamar yadda ya bayyana a lokacin da yake jagorantar dasa itatuwa a Marsabit da ke arewacin Kenya.
Ya ƙara da cewa: " A cikin wata guda, ƙasar ta rasa mutum 258 sakamakon ambaliyar ruwa, wanda hakan ya kusan kai adadin mutanen da suka rasu sakamakon ta'addanci a ƙasar."
Ofishin kula da harkokin Afirka na Amurka ya yaba wa Ruto saboda ayyana hutun dashen bishiyu don karrama wadanda ambaliyar ta shafa tare da sanar da bada tallafin dala miliyan $1m domin samar da agajin ambaliyar ruwa.
A baya gwamnati ta sanar da shirin kara yawan gandun daji zuwa kashi 30 cikin 100 nan da shekarar 2032 domin dakile sauyin yanayi.