Shugaba William Ruto a tsakiyar sanye da hula, ya kasance babban bako a bikin al'adu na Tobong'u Lore na bana.  

Daga Millicent Akeyo

Turkana, ya kasanace lardi mafi girma a cikin larduna 47 da ke ƙasar Kenya wanda ya kunshi faɗin ƙasa da ruwa da ya kai murabba'in kilomita 77,597.8 kuma ya yi fice da abubuwa iri daban-daban.

A shekarar 1984, wata tawaga ƙarkashin jagorancin masanin bincike kan gawarwakin da suka rayu kafin zuwan bil'adama a Kenya Richard Leakey, sun gudanar da bincike a yankin Nariokotome da ke lardin.

Sun yi nasarar gano wani abu da ya zama abin alfahari - ''Turkana Boy'', kwarangwal ɗin wata halitta mai kama da ɗan'adam ta wani matashi wanda ya yi shakaru miliyan 1.6.

Binciken kimiyya kan rayuwa da shekarun da ''Turkana Boy'' ya yi, sun yi karin haske game da lardin Turkana a matsayin jigon wanzuwar ɗan'adam.

Baya ga abubuwan mamakin da suka faru a baya, Turkana wuri ne mai cike da arzikin ƙasa da al'adu mai yawa da ke kewaye da duwatsu da yanayin hamada da kuma tafkin Turkana mai kyalli wanda aka fi sani da "Tekun Jade".

Sunan "Turkana" yana nufin al'ummar makiyaya da ke zaune a wani yanki mai yanayin hadama da ruwa a arewa maso yammacin Kenya.

Wannan al'ummar tana gudanar da ɗaya daga cikin bukukuwan da suka shahara a al'adun Kenya, wato Tobong'u Lore da ke nufin ''zuwa ta haɗuwar mutane'' a harshen gida na Turkana.

Ga waɗanda ke neman kai ziyarar buɗe ido Kenya baya ga wuraren shakatawa da aka saba zuwa, Tobong'u Lore biki ne da ke ƙarin haske kan al'ummar Turkana, yana cike da tarihi, da al'adu, da kuma yanayi mai kyau .

Leah Audan Lokaala, na ɗaya daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na bikin a lardin Turkana, ta ce bikin Tobong'u Lore ba kawai yana matsayin cibiyar nuna al'adun lardin ba ne, har da kira ga al'ummar duniya su zo yawon buɗe ido yankin.

''Muna cewa ''a dawo gida'' ga dukkan al'ummar duniya saboda mun yi imani- kuma kimiyya ta tabbatar da cewa mu ne asalin kafin bil'adama,'' kamar yadda Leah ta shaida wa TRT Afirka.

Girman bikin Tobong'u Lore na bana ya nuna irin tasirin da yake da shi wajen  jan hankali duniya zuwa yawon bude ido.

Bincike na tarihi

A kowace shekara, masu yawon bude ido daga ko'ina a faɗin duniya suna zuwa lardin Turkana don ganin wani bangare na baje kolin al'adu da tarihi da kuma karban baki daga 'yan yankin.

Taron bikin na 2024, wanda aka gudanar na tsawon kwanaki huɗu daga ranar 23 ga watan Oktoba a garin Lodwar, shi ne karo na takwas a jere da aka soma tun daga shekarar 2008.

Shugaba William Ruto na daga cikin baƙin da suka halarci bikin, wanda ya nuna baje kolin abubuwan al'adu na musamman kamar noman kwari a matsayin wata hanya da ba a saba da ita ba wadda ka iya samar da mafitar magance matsalar ƙarancin abinci da sauyin yanayi ke haifarwa.

Lusema Machanja, wani mazaunin Kukama ɗan asalin ƙasar Kongo da ke gudun hijira kana ɗan kasuwa da tawagarsa sun yi nasarar baje kolin kiwon da suka yi na bakaken kuda da kwaron gyare don ciyar da dabbobi da kuma amfanin mutane.

Girman bikin Tobong'u Lore na bana da kuma taron jama'ar da ya samu, ya tabbatar da cewa bikin na iya kara bunƙasa anan gaba.

"Muna son maraba da kowa," a cewar Leah. “Ba wani abu bane mai wahala mu yi wa 'yan' uwanmu maza da mata makiyaya 'yan Pokots da Nyangatom daga Habasha da kuma na Sudan ta Kudu maraba ba, shi ya sa idan aka dubi yadda aka tsara bikin Tobong’u Lore a wannan karon, za a ga cewa na musamman ne.''

Rawar gargajiyar Turkana na daga cikin manyan abubuwan da suka dau hankali a bikin Tobong'u Lore na bana.

Ɗaɗaɗɗun al'adu

Rawar gargajiya ta Turkana, wacce aka fi sani da Edonga a harshen gida na yankin na daga cikin abubuwan da suka ja hankali a bikin na bana.

Raye-rayen na samar da yanayi na nishaɗi da kuma tarihi, wanda ya samo asali daga al'ummomin baya da tare da hada ire-iren al'adun mayaka da bukukuwan girbi da dai sauransu.

"Yana taimaka mana mu tuna daga inda muka fito da inda kakanninmu suka fito," kamar yadda Rose Lomanat, 'yar asalin lardin Turkana ta shaida wa TRT Afrika.

“Muhimmancin wannan biki shi ne a tuna da yadda Turkawan suke rayuwa. mutane sun daina sanya tufafi irin na Turkana na da, amma idan aka zo bikin Tobong’u Lore, sai mu tuna yadda muke a baya, kuma muna baje kolin al’adunmu a gaban wadanda ba Turkana ba."

Kamar dai irin al'adar 'yan Maasai da Samburu, al'ummar Turkana suna sa tufafi masu launi mai kyau da kayan ado. Ana hada tufafin ne daga fatar dabbobi da kuma sanya wasu kayan ado, wanda ke nuna mahimmancin al'adun yankin.

"Ana kiran tufafin da Ebelok a al'adar Turkana kuma mata ne suke fi amfani kayan," a cewar Rosy Loshata.

Bikin na Tobong'u Lore ya ja hankalin al'ummomin makwabta

Sakon bikin na bana

Baya ga faretin al'adu da aka gudanar, bikin Tobong'u Lore na bana ya mayar da hankali wajen karfafa bukatar sakon samar da zaman lafiya da tsaro a Turkana da makwabtanta.

Shekaru da dama kawo yanzu, an wargaza yankunan arewacin Kenya sakamakon masu yunkurin raba ƙasa da kuma yaƙin basasa.

"Muna so mu tabbatar da cewa mun sami zaman lafiya a faɗin ƙasarmu da kan iyakokinmu...Wadannan iyakokin da muke da su da ke sa mu rikici, mu dauke su a matsayin iyakoki da ba na gaske ba," in ji Rosy.

Taron ya kuma kunshi tattaunawa kan sauyin yanayi.

Shugaba Ruto ya yi amfani da wannan dama wajen karfafa hanyoyin tattaunawa kan yadda yankin Turkana zai yi amfani da albarkatun ƙasa don samar da mafita mai dorewa kan illolin sauyin yanayi.

"Sauyin yanayi ya yi wa lardin Turkana mummunar illa.

"Sashen sauyin yanayi, wanda ni nake shugabanta, na kokarin tabbatar da cewa mun sami isasshen ruwa mai tsafta ga dabbobinmu, da ciyayi, har ma da na amfanin ɗan' adam," kamar yadda Lead ta shaida wa TRT Afrika.

TRT Afrika