Shirin Iwaju mai dogon zango na cigaba da samun karbuwa bisa amfani da cigaban zamani wajen fayyace labarin gwagwarmayar bakaken fata a ciki. Hoto: Disney      

Daga Charles Mgbolu

Wasu matasa guda uku 'yan asalin Afirka sun samu daukaka a duniya a sanadiyar fim dinsu mai dogon zango wanda ake nunawa a manhajar haska finafinan Amurka, Disney Studio, wanda aka yi amfani da zayyana a matsayin jarumai.

Toluwalakin Olowofoyeku da Olufikayo Ziki Adeola, da Hamid Ibrahim abokai ne daga Nijeriya da Uganda, wadanda suka yi amfani da zayyana da hotuna a finafinan kamfaninsu da zummar ba da labarin Afirka cikin nishadi, wanda kuma suka samun hadin gwiwar kamfanin Disney na Amurka.

Abokan uku sun hadu wajen shirya wani fim mai suna Iwaju, wanda aka tsara shi a bisa kirkararren labari ta hanyar amfani da cigaban zamani wajen shirya shi, wanda aka yi a Legas da ke Nijeriya.

An tsara labarin ne a kan wata yarinya wadda take fafutikar bankado gungun masu garkuwa da mutane.

Fim din ya daga martabar birnin na Legas, inda aka nuna yadda ake amfani da manyan motoci na alfarma da gidajen da suke amfani da kwamfuta da kuma amfani da mutum- mutumi a matsayin abin wasa.

Adeola, wanda ya tsara labarin ya ce dole a koma amfani da kirkirarriyar basira wato AI wajen ba da labarin Afirka nan gaba.

Kamfanin Disney ne ya dauki nauyin shirya fim din tare da hadin gwiwar kamfaninsu na Kugali. Hoto: Disney

"Yanzu da ake samun cigaba wajen amfani da kirkirarriyar basira ta AI a duniya, akwai bukatar masu shirya finafinai da masu zayyana su fara neman labaranmu na gaskiya, domin su ne suka sa muka bambanta, muka zama daban. Wannan ne zai sa duniyar ta kara saninmu a wannan yanayin da ake ciki na cigaban zamani," inji Adeola.

Tsarin amfani da kimiyya wajen ba da labarin fafutikar bakaken fafa na kara samun karbuwa musamman a yanzu da ake kara neman labaran nahiyar Afirka.

Nasarar da fim din Amurka na Black Panther ya samu ta kara jawo hankalin masu shirya finafinai zuwa neman labarin nahiyar.

Adeola wanda ya hada hannu ne da abokansa da suka taso tare masu suna Tolu Olowofoyeku da Hamid Ibrahim, ya ce burinsu shi ne su samar da wani dandamali da za su rika fahimtar da miliyoyin mutane a game da al'adun Afirka ta hanyar amfani da finafinan zayyana da amfani da fasaha da kuma kokarin mayar da shi tamkar zahiri.

"Abin da ake bukata shi ne inganci. Idan labari na asali ya samu aiki mai inganci, za a sha mamaki. Ina tunanin wannan hanyar da muka dauko za ta bude wani sabon babin finafinan zayyana a Afirka," in ji shi.

Inganci na da matukar muhimmanci kasancewar matasan masu shirya finafinan sun dauko wani salo da ba a saba da shi ba, wanda yake ba da labarin al'adu ta hanyar amfani da kimiyya da tarihi da zancen zuci.

Adeola (a hagu) ya yi aiki tare da Tolu Olowofoyeku da Hamid Ibrahim. Hoto: Kugali

Masana sun ce shirin zai fahimtar da bakaken mutane mazauna kasashen waje tarihinsu da suka manta.

Adeola ya ce sun dauko wannan tsarin ne domin su nuna basirar yaran Afirka, kamar yadda aka nuna basirar wata 'yar shekara 10 a shirin.

"Yawanci ba 'yan Afirka ba ne suke taka rawa a finafinan da suka shafi nahiyar, ko kuma sai a rika nuna nahiyar da bakin fenti. Wani abu mai muhimmanci da muka nuna a jarumanmu shi ne basira da nuna abu tamkar zahiri.

"Ina so in nuna cewa kowa na da basira daidai gwargwado. Ina ganin duk wanda ya kalla wannan shirin zai gane cewa muna da basirarmu, muna kara wa al'adunmu haske sannan muna da irin tamu kafiyar."

Ministar Al'adu ta Nijeriya, Hannatu Musawa ta yaba da shirin a lokacin da aka kaddamar da shi a Legas, inda ta ce, "Wannna wata babbar nasara ce ga Nijeriya, domin ko ba komai, mun samu masu ba da labarinmu na asali a yadda yake."

A shirin mai dogon zango an yi amfani da karyayyyen Ingilishi na Nijeriya da wasu yaruka na kasar, sannan dukkan wadanda aka daura muryarsu 'yan asalin yankin ne na Afirka ta Yamma.

TRT Afrika