Dahlia: Ƴar ƙasar Gabon da ke bayar da labarai ta hanyar kwalliya

Dahlia: Ƴar ƙasar Gabon da ke bayar da labarai ta hanyar kwalliya

Tun a 2020 mai kwalliyar ta soma nuna sha'awarta bayan ta kalli wani fim wanda ya burge ta.
Dahlia sfx ta yi fice wurin zane-zanen. / Hoto: TRT Afrika

Daga Firmain Eric Mbadinga

Hannu na jini ba tare da rauni ba, da ɗinke baki da gashi ba tare da an huda bakin ba misalai ne na irin kwalliyar da ƴar ƙasar Gabon ɗin Dahlia ke yi .

Dahilia sfx, sunanta na asali shi ne Ngondo Tessa Clelia Tirolle, tana cikin shekarunta na 20, inda tuni ta samu damar nuna irin baiwar da take da ita dangane da kwalliya a gajerun bidiyon da ta yi wa mawaƙa a ƙasarta waɗanda suka haɗa da Nicole Amogho da kuma Styll Awax.

Dahilia ta ƙara ƙwarewa a baiwar da take da ita tun tana yarinya tsawon shekaru.

"Na ƙware wurin samar da rauni na bogi da fenti a jiki," kamar yadda matashiytar mai shekara 24 ta shaida wa TRT Afrika.

Tun a 2020 mai kwalliyar ta soma nuna sha'awarta bayan ta kalli wani fim wanda ya burge ta.

Dahlia ta ce tana tafiya da abin da take ji idan tana aikinta. Buroshinta da fentinta sun isa su zayyanar da duk wani abu da ya faɗo mata a rai.

Dahlia sfx ta ce tana son ta bayar da ƙwarin gwiwa ga yara masu tasowa da ke son irin wannan kwalliyar. / Hoto: TRT Afrika

Ya dogara ne da irin mutanen da za ta yi wa aiki, Dahlia sfx za ta iya shafe minti biyu zuwa awa ɗaya tana kwalliyar.

"A taƙaice ina da mutum biyu waɗanda suka zama allon kwaikwayona. Ɗaya a Gabon da ake kira Biligui de l'Or, wadda ita ƴar gargajiya ce matuƙa. Bayan ita ina son aikin Makeuppbyruthie da ke Amurka. Tana ba ni ƙwarin gwiwa matuƙa," in ji Dahlia sfx.

Duk da cewa mai zanen tana da digiri, ta samu kyaututtuka da dama ta hanyar sana'arta ta, ba ta da niyyar mayar da ita sana'arta, ko kuma aƙalla hanyar samun kuɗinta a masana'antar Gabon wadda a halin yanzu ke ƙoƙarin kafa kanta.

Sakamakon an san irin baiwar da take ta ita, Dahlia sfx ta ce tana da tsada idan aka zo ta fannin neman ta yi aiki. Kuɗin da Clélia Tirolle's da ke karɓa zuwa yanzu sun kai CFA 30,000 zuwa 250,000.

Dahlia sfx, wacce ke ƙoƙarin daidaita biyan bukatun abokan cinikinta a Libreville da Port-Gentil, babban birnin tattalin arzikin ƙasarta, tana da sha'awar yin koyi da wasu waɗanda ta ce a shirye koya abin da ta iya.

Kamar yadda UNESCO ta bayyana, Masana’antar fina-finai a Afirka na samun ci gaba, inda Najeriya ke kan gaba, inda aka yi kiyasin shirya fina-finai 2,500 a duk shekara.

TRT Afrika