Wasu daga cikin matasan suna takaicin irin rayuwar banza da suka yi a baya amma yanzu suna neman sauya halayensu. Hoto: TRT Afrika.

Daga Coletta Wanjohi

A kauyen Kibagare da ke Nairobi, wani matashi George Ekombe da yake kokarin rufe shago, ya rika fada wa kwastomominsa cewa su yi sauri domin yana so ya tafi filin kwallo.

Mai shekara 24, yana da wani karamin shago da ake buga wasannin kwallon kafa na talabijin, inda matasa suke biyan kudi suna bugawa.

A kullum, yakan yi cinikin dala biyu, wanda ya yi kadan matuka idan aka kwatanta da abin da yake samu a sace-sace.

"Yanzu haka nake tafiyar da rayuwata," in ji George, a hirarsa da TRT Afirka.

"Ina fama sosai saboda wani lokacin ma ba na samun kudi. Amma haka zan hakura saboda ba na son komawa aikata laifuka."

Labarin George yana kama da labarin dubban matasan Nijeriya da suke son canja rayuwarsu bayan sun kasance 'yan jagaliya- wadanda a lokuta da dama suke shiga aikata miyagun laifuka saboda talauci, a wasu lokutan kuma gaggawar neman arziki tana jan matasan shiga aikata laifuka.

A wata kididdigar kwanan baya da Hukumar Kididdigar Kenya ta fitar, ta nuna cewa an aikata laifuka 82,200 a 2021. Hakan ya nuna cewa an samu raguwa sosai da abin da aka samu a shekarar da ta gabace ta.

Jami'an tsaro sun ce matasa maza ne suke aikata yawancin laifukan nan.

Wasu tubabbun masu aikata laifi da TRT Afirka ta zanta da su a kauyen Kibagare, sun ce tasowa a kananan kauyuka irin nasu Tana takaita wa matasa samun damarmaki.

Matasan sun ce kwallon kafa na debe musu kewa da hana su aikata laifuka. Hoto: TRT Afrika. 

Matasan, wadanda yawancinsu ko dai sun gudu daga makaranta, ko kuma marasa aikin yi ne, suna amfani da aikata miyagun laifuka a matsayin hanyar samun arziki cikin sauri. Amma maimakon arzikin, yawancinsu sai suka kare a gidan yari, ko kuma a kashe su.

George ya gudu ne daga gida yana da shekara 7, lokacin da ya yi tunanin cewa, "Na girma na zama mutum."

"Bayan na yi shekara biyu a titi, sai na koyi kwacen waya da jakunkuna. A matsayina na karamin yaro, samun tsakanin Dala 30 zuwa Dala 100 a kullum a lokacin ba karamin kudi ba ne a wajena."

Sai dai duk kudaden da yake samu yana kashewa ne wajen shan giya da "morewa."

"Babban tashin hankali da na shiga shi ne lokacin da wasu abokaina guda biyu suke fada min sun shirya wata babbar harkalla da za ta yanke mana talauci na har abada. Mun zata satar talabijin ko rediyo ce," in ji shi.

A cewarsa, rayuwarsa ta sauya ne "Lokacin da muka kai wa wani mutum farmaki."

George ya ce ya fara sauya tunani game da aikata miyagun laifuka lokacin da ya gane cewa abokansa sun samu bindiga.

"Ba haka muka saba ba. Kwacen waya kawai muke yi, amma ba mu taba amfani da makami ba. Nan na shiga tsoro domin rike bindiga matsala ce. A jagaliyanci, muna ganin amfani da bindiga don aikata miyagun ayyuka zai iya jefa mutum ga halaka."

A 2017, 'yan sanda sun harbe abokansa guda biyu a lokacin da suke yunkurin yin fashi da tsakar rana. Nan jikinsa ya ba shi cewa shi ma hakan zai faru da shi idan bai tuba ba.

"Sai na koma kauyen Kibarage, amma kuma rashin aikin yi ya sa na kasa daina tunanin aikata miyagun laifuka," in ji shi.

A lokacin ne Aaron Kifogo - wanda kocin kwallon kafa ne - ya ba George damar sauya rayuwarsa.

Yanzu George Ekombe ya mayar da hankali wajen buga bidiyo gem da wasan kwallon kafa. Hoto: TRT Afrika

"Koci Aaron ne ya same ni ya ce min na fara zuwa kungiyarsa ina buga kwallo. Aaron matashi ne mai shekara 30, amma a wajena ya zama tamkar mahaifi. Shi ne ma ya taimaka min wajen bude shagon nan da nake samun na abinci."

Aaron, wanda jagoran matasa ne a kauyen, yana yawan jawo matasa kusa da shi domin wayar musu da kai su sauya rayuwarsu.

Abin mamaki

A lokacin da George ya rufe shagonsa, sai ya kira abokinsa Setrick Isichi, mai shekara 26, wanda abokin wasansa ne mai shagon gefensa.

Hanya daya kadai da Setrick ke samun kudi ita ce tsinto robobin ruwa daga wani shagon zuwa wani shagon, kuma yana samun Dala daya a kullum.

Shi ma labarin rayuwarsa irin ta George ce.

"Na fara aikata laifuka ne ina da shekara 15. Na kasance ina sha'awar kudaden da mutane suke samu idan sun yi sata," kamar yadda Setrick ya bayyana wa TRT Afirka.

Laifinsa na farko shi ne kwacen waya da ya yi a hannun wani da yake wucewa a cikin mota. Nasarar da ya samu ce ta sa ya cigaba da sace-sace har tsawon shekara bakwai.

Ya cigaba da magana cikin tattausar murya, fuskarsa a daure, sannan yana kishingide.

"Wata rana a shekarar 2012, abokaina guda uku suka yi kwacen waya suka gudu. Sai ni ma na yi yunkurin binsu," in ji shi, sannan ya kara da cewa, "Da na yi yunkurin guduwa, sai mutum biyu suka kama ni suna ihun barawo. Cikin 'yan dakika mutane suka taru."

Fuskarsa da hannunsa sun nuna alamar dukan da ya sha a hannun mutanen.

Setrick isichi ya ce yana murza kwallon kafa da kuma yin ga-ruwa domin samun abin kashewa. Hoto: TRT Afrika

'Yan sanda ne suka ceci Setrick, suka kai shi asibiti, da ya warke suka tura shi gidan yari.

Setrick ya sha wahala a zamansa a gidan yari na shekara biyu, inda babu wanda ya ziyarce shi. Amma zaman ne ya zama silar shiriyarsa. Tun a gidan yarin ya koma makaranta.

Cikin murmushi ya rika tuno abubuwan da suka faru a gidan yarin, inda har wani jami'in tsaro ya ba shi kiwon beran masar guda uku, amma kafin ya bar gidan sun hayayyafa sun zama 50.

Bayan an sake shi daga gidan yari, Setrick sai ya koma kauyen Kibarage da nufin tuba daga aikata miyagun laifuka. Sai ya fara kananan sana'o'i domin samun na abinci, sannan ya fara buga kwallon kafa.

Sai dai a wani yanayin jarabta, ‘ya’yansa sun mutu a rana daya kafin su kai shekara daya.

"Na yi da-na-sanin sace-sacen da na yi da jefa mutane cikin damuwa. Lokacin da yarana suka mutu, abin da ya zo raina shi ne bala'i ne ya fado min saboda barnar da na aikata wa mutane," in ji shi cikin zubar da hawaye.

Kyawun kwallon kafa

Matasa da dama a kasar Kenya sun daina karatu kuma ba su da ayyukan yi. Hoto: TRT Afrika

Duk da cewa an fi sanin mutanen Kenya da tseren fanfalaki a duniyar wasanni, wasan kwallon kafa na cikin fitattun wasanni a tsakanin yara da matasan kasar.

Yara wadanda ba za su iya sayen kwallo ba, suna amfani da roba su mayar da ita kwallo. A wajen matasa, suna kallon harkar a matsayin wasan nishadi da neman arziki.

A Filin Wasan Kibarage Bamboo, ana yawan zuwa buga kwallo daga karfe hudu na yamma a kullum. Mutanen garin sukan zo domin atisaye daban-daban. Wasu a kungiyance, wasu kuma a daidakunsu. Har ma yara ba a bar su a baya ba.

Wasu kuma suna zuwa ne domin su zauna suna kallo, suna hira.

Da Aaron Kifogo ya busa husir, 'yan wasan Kungiyar Kibarage Sportiff- Kungiyar da George da Setrick suke- sai su shiga atisaye.

'Yan wasan suna kiransa da suna Fiesco, wanda shi da kansa ne ya rada wa kansa. Wasu suna rungume shi, wasu kuma su taba kafadarsa a lokacin da suke zagaye da shi suna sauraron jawabi.

"Sha'awa da fushi ne suka saka ni a harkar kwallon kafa," in ji matashin mai shekara 29 da yake daukar dawainiyar 'yan uwansa biyu.

“Kasancewar a kauye na taso, sai na lura aikata miyagun laifuka na bata rayuwar mutanenmu baya. An harbe abokaina da dama, wasu kuma mutanen gari ne suka kashe su. Ni ma an taba kama ni da zargin almundahana lokacin ina karami. Bayan an sake ni, sai na yanke shawarar sauya rayuwata saboda 'yar uwata da dan uwana da nauyinsu ke wuyana."

A shekarar 2018 Aaron ya fara gangamin wayar da kan matasa kan illar aikata miyagun laifuka da ya sanya wa suna 'Youth Campaign Against Crime' domin matasa irinsa su gane illar shiga aikata miyagun laifuka. Kalubalensa a lokacin shi ne bai da amsa a duk lokacin da matasan suka tambaye shi wace sana'ar zai ba su idan suka daina aikata miyagun laifuka.

"Zan samu matashi wanda yake cigaba da aikata miyagun laifuka, na ja hankalinsa a kan ya shigo cikinmu. Ina ba su shawarar cewa kwallon kafa zai taimaka mana wajen daina shaye-shaye da kaucewa zuwa gidan yari da ma mutuwa. Akwai dan sauki a kasancewa tare da mu saboda babu wanda zai kyare ka a nan domin kusan kashi 90 dinmu a nan mun taba kasancewa masu aikata laifi."

Kungiyar ta fara ne da 'yan wasa 15, amma yanzu sun kai 40.

George yana atisaye da kungiyar, amma idan sun shiga gasa, yakan koma ya rika yi musu sankira.

"Harkar wasanni ta tseratar da ni daga harsashi da gidan yari. Kwallon kafa ya cire min tunanin jagaliyanci da fyade," in ji George.

"Idan na zo nan atisaye, ina tashi ne lokacin da na gaji. Sai na koma gida na kwanta na yi barci. Ba ni da lokaci da karfin da zan fita na yi sata. Wannan shi ne sauyin da kwallon ya samar mini.'

Shi kuma Isichi cewa ya yi, kwallon kafa ya sa ya zama mutum.

"Na yi abokai da dama. Sanadiyar kwallon, na yi tafiye-tafiye da dama a kasar nan. Yanzu akwai wuraren da idan na shiga, mutanen da ban sani sai su rika kiran sunana suna cewa na nuna bajinta a wasa. Mutane su yi farin ciki saboda ni ma ai wani abu ne. Ban taba samun hakan ba lokacin da nake aikata laifuka."

Aaron yana dogaro ne da abokansa wajen gudanar da kungiyar. 'Yan kungiyar suna kiransa 'mai kiran neman agajin wasu' domin yana yawan kiran wasu kungiyoyin domin aron kayayyakin wasansu idan suna da wasa.

Kimanin shekara hudu da suka gabata, kafin assasa kungiyar 'Kibarage Spotiff, kauyen Kibarage na rasa akalla matasa biyar duk shekara, kuma ana kashe su ne saboda aikata miyagun laifuka. Aaron ya ce yanzu adadin ya ragu zuwa mutum biyu a shekara saboda matasa da dama suna shiga kungiyarsa domin sun fahimci amfanin wasanni.

Ya ce wasu iyayen ma da kansu ne suke kawo yaransu kungiyar tasa.

Haka kuma an bude kungiyoyin kwallon kafa da dama a yankin domin jawo hankalin matasa su gyara rayuwarsu. Wasu suna yin wasan kwando wasu kuma na sauran wasanni.

Haka kuma kungiyar Aaron ta zama ta taimakon kai da kai. Kowane dan wasa yana kawo rabin Dala duk wata, wanda ake tarawa a sayi kayan wasa da kuma taimakon juna.

Ya ce burinsa nan gaba a kai lokacin da za a daina kashe matasan Kibarage saboda sun aikata miyagun laifuka.

A wajen George da Isichi, kwallon kafa ya bude musu wani sabon babi domin yin rayuwa mai kyau.

TRT Afrika