#JJH53 : Kenya's most famous play comes home after 45-year wait / Photo: AFP

Daga Gaure Mdee

A zamanin baya, fataucin zinare daga Zimbabwe zuwa Tanzania a garin Kilwa a Lindi na gabar teku, ya bude kafar da wani rukunin mutane suka fara jirkita wani harshe wanda su kadai suke fahimta.

Wani cakudadden yare ya samu tsakanin mutanen, wanda mutane mazauna bakin teku ke amfani da shi, da kuma ‘yan kasuwar Shona.

Ana kiran sa da Swahili, harshen da kiyasin mutum miliyan 250 cikin kasashe 13 suka magana da shi a yau.

Juma Kibacha, masanin tarihin shari’a, kuma malami a makarantar Institute of Management da ke Dar es Salaam, ya ce “Wannan wani kauli ne game da yadda harshen Swahili ya samu, har ya zama harshen gamagari a yankin gabashin Afirka.

A zahirin gaskiya, bincikena ya nuna haka, kuma shi ne abin da na yi imanin ya faru.”

A zahiri, sunan Swahili ya zo ne daga kalmar Larabci ta “sawāḥilī” – wadda jam’in siffatau ne na kalmar Larabci mai ma’anar “’yan bakin gaba”.

“Harsunan sun yadu daga Tsakiyar Afirka, har zuwa yankunan kudanci da kudu maso gabashin Afirka, kafin a kekketa Afirka zuwa kasashe daban-daban a shekarar 1885, lokacin Taron Berlin, wanda kuma ya dakatar da cigaba da watsuwar Bantu.”

Farfesa Aldin Mutembei, mai bincike kuma daraktan Kiswahili a makarantar Conficius Institute da ke Jami’ar Dar es Salaam

Sai dai wannan daya ne kawai daga cikin ra’ayoyin da ke ikirarin asalin samuwar Swahili, da kuma yaduwarsa a fadin yankin.

Harshen ya shahara zuwa wani babban abu mai zuciya da ruhi cikin birane da yawa, kuma harshe ne mai zaman kansa mai mabiya daga yankuna masu dimbin yawa.

Ga misali, a Nairobi, harshen Sheng wani nau’in Swahili ne gwamutsattse da Ingilishi, wanda ake jin sa a bakin matasa ‘yan birni da ke Kenya.

Ana magana da harshen Swahili a makarantu a Tanzaniya da Kenya/Photo AA

Harshen Lingala na Jamhuriyar Dimukradiyar Congo, a zahiri Swahili ne hade da murdiya da kuma sauyin haruffa.

Kuma har harshen Turkanci yana da kalmomi irin na Swahili, kamar uba (baba), da alkalami (kelam) da daftari (deftar), da sauransu.

Amma alal hakika, me wannan abin yake nufi a karshe ga harshe mai irin wannan yaduwa, a tarihi da kuma damammaki?

Shin wannan zai iya zama mai riba a harkar kasuwanci? Bari mu bar batun Tarayyar Afirka a gefe. Mu dauka a ce an samar da dandalin Kasuwanci Mara Haraji, kuma mai amfani da harshe daya; wannan ba zai kayatar ba?

Yadda Swahili ya samu watsuwa cikin yankunan abu ne da za a iya dangantawa kan abubuwa hudu kamar yaduwar jama’ar Bantu da addini, da kuma yanayin mutanen na marabci da kuma iya karbar sauran harsuna ba tare da ya rasa ruhinsa ba.

Yaduwar al’ummar Bantu

A zahiri, sunan Swahili ya zo ne daga kalmar Larabci ta “sawāḥilī” – wadda jam’in siffatau ne na kalmar Larabci mai ma’anar “’yan bakin gaba”/Photo AA

An kiyasta cewa kashi 65 na al’ummar Afirka ‘yan asalin tushen harsunan Bantu ne ko kuma mausu alaka da Bantun.

Kuma wannan rukunin tushen harsuna ya mamaye kaso mafi girma na yankunan Afirka sama do kowane rukuni.

Yana da muhimmanci a fahimci cewa Swahili dan tushen Bantu ne, wanda hakan yake sa harshen shiga wurare.

Farfesa Aldin Mutembei, wani mai bincike ne kuma daraktan Kiswahili a makarantar Conficius Institute da ke Jami’ar Dar es Salaam.

Ya ce “Harsunan sun yadu daga Tsakiyar Afirka, har zuwa yankunan kudanci da kudu maso gabashin Afirka, kafin a kekketa Afirka zuwa kasashe daban-daban a shekarar 1885, lokacin Taron Berlin, wanda kuma ya dakatar da cigaba da watsuwar Bantu.”

Addini da kasuwanci

Harshen Swahili ya karade yawancin kasashen gabashin Afirka

Kafin mulkin mallaka, akwai kasuwanci da yawa da ake yi da Swahili, har ta kai wasu kalmomin gabashin Afirka mai nisa sun karbu a harshen an kuma shigar da su.

Rubutaccen harshe ya fi saurin yaduwa sama da harshen baka. Kuma Swahili ya samu alaka da addini saboda Larabawa su suka fara rubuta Swahili a rubuce.

‘Masu fafutukar yada Kiristanci da kuma masu neman ma’adanai sun yi kokarin dakile yaduwar harshen Larabci, amma sai suka samu harshen ya riga ya shige maganganun mutanen Bantu.

Mutembei ya bayyana cewa “Cikakken mutumin Swahili Musulmi ne, saboda Larabawa Musulmai ne”.

Wannan shi ne sakon a wancan lokacin, kafin zuwan Turawan Portugal, da Jamusawa wadanda kuma suka tarar da harshen har suke masa wani kallo na bambarakwai saboda ya sabawa sautin harshen Latin.

Kuma Swahili ya samu alaka da addini saboda Larabawa su suka fara rubuta Swahili a rubuce/Photo AA

Cikin rashin sani, Jamusawa su ne suka hade kan ‘yan Bantu masu magana da Swahili a Afirka, saboda sun ba da umarnin duk masu magana da Swahili da su nazarci harshen, ta amfani da haruffan Latin.

Amma wadanda suka yi tawaye, sai suka zabi koyon harshen cikin haruffan Larabcin da Latin duka biyu.

“Wani abin al’ajabi shi ne harshen Hausa na Nijeriya yana kama da Swahili, sama da duk sauran harsunan Nijeriya da ke gefen iyakokin kasashen Hausa, sakamakon alakar Hausar da Larabci.”

Littafin Bible na farko a harshen Swahili, shi ne wanda Jamusawa suka samar, daga wani da ake kira Karl Roehl.

Bibile din na Swahili ya yi wuyar samun karbuwa a Swahili, saboda ba ya dauke da ayoyin Bible a irin Swahili da aka saba gani, sakamakon marubucin ya cire duk wasu kalmomin Swahili da ke da alaka da Larabci.

Iya karbar sabbin kalmomi

Mutembei ya ce, “Kalmar Swahili da ke nufin wayewa ita ce “ustaatabu”, wadda a ainahi ke nufin ‘zamowa Balarabe’”.

Wannan ya haifar da babban kalubale har ga ‘yan mulkin mallaka wajen amfani, a kokarinsu na cakuda Afirka Swahili Bantu da salon rayuwa irin tasu.

Hakan ya saukaka musu kara kalmomi cikin jerin kalmomin harshen Swahili.” Batun kalmar “Bantuntarwa”, shi ne abin da Swahili ya gwanance wajen yi, sabanin sauran harsunan da ke Afirka.

Swahili yana karbar bakin kalmomin ko da yaushe, wanda hakan ya sa aka iya samun nau’in Swahili mai suna Sheng a Kenya.

A shekarar 1963, an kaddamar da fara bikin Kwanzaa a Amurka, wanda daga Swahili aka samo sunansa da kuma ruhinsa.

Bakaken Amurkawa ne suka kirkiri bikinsu, wanda zai zama daban da na sauran al’ummar Amurka.

Swahili ba ya kashe sauran harsuna

Harshen Hausa na Nijeriya yana kama da Swahili, fiye da sauran harsunan kasar sakamakon alakar Hausar da Larabci/Photo AA

Tsohon malami a Jami’ar Princeton mai koyar da Nazarin Afirka, ya bayyana cewa, “sabanin Ingilishi, ko Faransanci ko Jamusanci da ire-irensu, cigaban da Swahili ke samu ba ya gasa ko hana tasiri ko shuhurar sauran harsuna a duniya”.

Shugaban Tanzania na farko, Julius Nyerere shi ya hade kan kabilun Tanzania daban-daban ta hanyar sanya su magana da harshe guda a fadin kasar.

Amma fa bai wofantar da harsunan kowace al’umma ba, kawai dai tsarin makaranta a kasar an mayar da shi na Swahili.

Shugaba Nyerere (1962-1985) na Tanzania, da Jomo Kenyatta (1964-1978) na Kenya sun daukaka Swahili a matsayin muhimmin harshe ga cigaban yankin a fannin siyasa da tattalin arziki, da ‘yancin-kai.

“Kalmar Swahili da ke nufin wayewa ita ce “ustaatabu”, wadda a ainahi ke nufin ‘zamowa Balarabe’”

Farfesa Aldin Mutembei

A hukumance, harshen Swahili shi ne harshen kasuwanci a Kungiyar Hada Kan Gabashin Afirka, wanda ta kai har ana karfafa amfani da harshen wajen rubuta takardun aiki.

An karbi harshen a wurare da dama, har ma a Kungiyar Hada Kan Kudancin Afirka, SADC, kuma an saka Swahili a cikin harsunan sadarwa a lokacin tarukan kungiyar.

A shekarar 2021, Rwanda ta nemi Tanzania ta tura mata malaman Swahili don daga darajar harshen a makarantun sakandare.

Mutembei ya Ambato tsohon shugaban Ghana, Kwame Nkurumah, a taron Tarayyar Afirka na farko, yana cewa, “Muna bukatar harshe guda a fafutukar kishin Afirka, kuma cimma wannan muradi sai ta hanyar harshe, kuma harshen nan shi ne Swahili”.

Mutembei ya kara da cewa, “Ghana ta kaddamar da koyar da Swahili a makarantun kasar a shekarar 1964, kuma akwai sashen koyar da swahili a Jami’ar Ghana. Su ne na farko a Afirka, duk da kuwa kasar ba kasar da ake magana da Swahili ba ce.”

Cewa a yanzu duniya ta amince da ranar Swahili ta Duniya, kuma za a gudanar da taron “Kishin Afirka da Swahili a Afirka: a birnin Accra, ranar 7 ga watan Yuli, hakan zai iya nuna alamar nasarar da ke gaba game da cigaban Swahili a nahiyar Afirka.

TRT Afrika