Jam'iyyun siyasa da dama a Afirka ta Kudu sun yi alƙwarin samar da ayyukan yi idan suka samu nasara a zaɓe. /Hoto: Getty Images

Daga Pauline Odhiambo

Mike Spencer Mandizvo ya shafe shekara 13 yana zaune a Afirka ta Kudu, inda ya koma ƙasar a lokacin da Afirka ta Kudun ke shirin karɓar baƙuncin Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA a 2010.

Ɗan ƙasar na Zimbabwe ya zaɓi lokaci mai kyau domin soma sabuwar rayuwa a Afirka ta Kudu. A lokacin aka ƙara inganta harkokin sufuri da makamashi da sadarwa da ababen more rayuwa inda aka kashe kimanin dala biliyan uku.

Wannan ne ya jawo aka samu ayyukan yi da dama da kuma samun kasuwanci a ƙasar, inda aƙalla baƙi maso yawon buɗe ido 300,000 suka shiga ƙasar a lokacin Gasar Cin Kofin Duniyar.

"Cikin ƙasa da mako guda muka samu aikin yi a 2010," kamar yadda Mike ya shaida wa TRT Afrika. "An ɗauke ni aiki a matsayin manajan ɓangaren abinci a wani kamfanin jirgin sama. A lokacin, babu wahala wurin samun aiki."

Mutum zai yi tsammanin wannan zai zama wani koma baya ga tattalin arzikin Afirka ta Kudu, amma abubuwa sun canza sosai tun daga 2010.

Matakin rashin aikin yi a Afirka ta Kudu ya kai kashi 32.9 cikin 100 a rubu'i na biyu na 2024, kusan makonni biyu kenan kafin zaɓe wanda jam'iyya mai mulki ta Afircan National Congress ANC zai kasance mata zakaran gwajin dafi.

Jam'iyyun siyasa da dama a Afirka ta Kudu sun yi alƙwarin samar da ayyukan yi idan suka samu nasara a zaɓe. /Hoto: Getty Images

Rashin aikin yi

Kamar sauran jam'iyyu da ke yaƙin neman zaɓe, ANC ta yi alƙwarin samar da ƙarin ayyukan yi ga 'yan Afirka ta Kudu.

Sai dai adadin waɗanda ba sa aiki a ƙasar, wanda ya kusan kai kaso 35.3 cikin 100 a lokacin korona, yana nuna cewa akwai rashin daidaito.

Kamar yadda porta Statistica mai fitar da ƙididdiga ta bayyana, akwai mutum miliyan 7.34 da ba su da aikin yi a 2023, idan aka kwatanta da miliyan 7.24 da aka da su a bara.

Ba shakka rashin aikin yi ya ci gaba da ƙaruwa a ƙasar tun daga 2013, inda a 2020 ne kawai lamarin ya ragu.

Mike na daga cikin dubban ma'aikatan da aka kora daga aiki a ƙasar a shekarar 2020 sakamakon annobar korona. Har zuwa lokacin, ya samu ayyuka masu kyau waɗanda suke biyan albashi mai tsoka, daga ciki har da wanda ya yi shekaru biyar da suka wuce na mai tabbatar da ingancin kayayyaki a ɗaya daga cikin kamfanoni mafi girma na ƙasar.

Mutumin mai shekara 37 a halin yanzu yana aiki a matsayin direban tasi domin taimaka wa matarsa da 'ya'yansa biyu da kuma danginsa da ke Zimbabwe a halin yanzu.

Mike Mandizvo wanda asalin ɗan ƙasar Zimbabwe ne da ke aiki a Afirka ta Kudu domin taimaka wa iyalinsa. / Hoto: Others

Ƙin jinin baƙi 'yan ƙasar waje

Duk da cewa Afirka ta Kudu na talatta kanta a faɗin duniya a matsayin ƙasa da ke da wuraren yawon buɗe ido da zuba jari, ƙasar wadda ke da kusan kowane irin na'in bil'adama ta kasance ƙasa wadda ba ta da kara ga baƙi.

"Yaƙi da ƙin jinin baƙi na daga cikin abubuwan rayuwa na yau da kullum a Johannesburg. Mutanen da nake ɗauka a cikin tasi a wani lokacin sukan yi mani magana kan cewa me ya sa nake ɗauke musu ayyukan da 'yan'uwansu 'yan Afirka ta Kudu ya kamata su yi," kamar yadda Mike bayyana.

Aƙalla abokan aikinsa 20 an ci mutuncinsu kan wannan aikin. "Ana yawan tuna mana cewa mu baƙi ne a nan. Ana kallonmu a matsayin barazana."

A halin yanzu akwai bakin haure sama da miliyan biyu a Afirka ta Kudu, mai yawan jama'a miliyan 62.

Akasarin ma'aikata 'yan ci rano sun fito daga Zimbabwe da Lesotho da Mozambique masu maƙabtaka, kamar yadda ƙididdiga ta nuna.

Tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a shekarar 1994, bakin haure daga kasashen Afirka da Asiya ke tururuwa zuwa Afirka ta Kudu domin yin aiki, kasuwanci, neman ilimi da kuma neman mafaka.

Wadannan sun hada da mutanen Somaliya, Habasha, Nijeriya da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, da kuma kasashen Asiya kamar China, Indiya, Pakistan, da Bangladesh.

An samu rikici mafi muni na nuna ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu a watan Mayun 2008, lokacin da aka kashe akalla mutane 62, daruruwa suka jikkata, da kuma wasu 100,000 da suka rasa matsugunansu, yayin da wasu gungun mutane suka kai hari kan gidajen bakin haure a fadin kasar.

A 2023, Operation Dudula wadda ƙungiyar bijilanti ce wadda ta koma jam'iyya, ta jagoranci wani kamfe na rufe wuraren kasuwancin 'yan ƙasashen waje. Dudula a harshen Zulu na nufin a fitar, wanda harshe ne da ake yawan amfani da shi a Afirka ta Kudu.

Rikicin ƙin jinin baƙi na Afirka ta Kudu wanda ya faru a 2014 ya yi sanadin mutuwar mutum 62 da kuma raunata aƙalla 100,000. / Hoto: Reuters

Mike wanda yake ta ƙokarin sabunta katin aikinsa tun 2010, ya bayyana cewa direbobin tasi da dama na saka kemara da rikoda a motarsu domin naɗar abubuwa musamman idan an ci zarafinsu.

"Ƙin jinin baƙi lamari ne da 'yan siyasa da dama ke amfani da shi domin samun ƙuri'u a lokacin zaɓe," kamar yadda Mike ya shaida wa TRT Afirka. "A bana, mun ga 'yan siyasa da dama da ke cewa ba su son ganin duk wani ɗan ƙasar waje a Afirka ta Kudu, ko dai suna zaune ta halastacciya ko ta haramtacciyar hanya a ƙasar."

Siyasar shige da fice

Oscar van Heerden, wanda babban mai bincike ne a Cibiyar Diflomasiyya da Jagoranci ta Afirka a Jam'iar Johannesburg, inda ya bayyana cewa akwai jam'iyyun siyasa aƙalla biyu waɗanda suke magantuwa kan batun ma'aikata 'yan ci rani.

"Jam'iyyun Action SA da Patriotic Alliance sun ɗauki matsaya kan cewa idan kana zama a Afirka ta Kudu kuma kana da takarda za ka iya zama ka yi aiki a can. Amma waɗanda ba su da takardu dole a tasa ƙeyarsu," in ji van Heerden.

"Matsayin bangarorin biyu ya ta'allaka ne kan hujjar cewa ana matsa wa gwamnatin Afirka ta Kudu game da ayyukan jin dadin jama'a a asibitoci, makarantu da kuma jin dadin jama'a.

"Akwai kuma batun cewa da yawa bakin haure da suke zaune ba bisa ka'ida ba na kwace ayyukan yi daga 'yan Afirka ta Kudu."

Tsarin lasisin aiki

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ce ke bayar da lasisin aiki ga 'yan ƙasashen waje wadda ba ta wuce ta shekara biyar, ko kuma lokacin kan ta'allaƙa ne da kwantiragin aiki.

Wannan (ma'aikatar harkokin cikin gidan) na daga cikin ƙungiyoyi da dama na Afirka ta Kudu waɗanda suke da alhakin bayar da kariya ga baƙi 'yan ƙasashen waje," kamar yadda van Herdeen ya bayyana.

"Akwai wasu ƙungiyoyi da dama waɗanda ke kula 'yan ƙasashen waje kuma sun ta'allaƙa ne kan ƙasar da mutum ya fito. Misali, akwai wasu ƙungiyoyi da ke hukumomi da ke kula da walwalar 'yan Zimbabwe da Malawi da sauran 'yan ƙasashen waje a ƙasar."

Haka kuma akwai wasu ƙungiyoyin 'yan sanda na musamman da ake buƙatar su bayar da kariya ga 'yan ƙasashen waje, duk da cewa Mike ya bayyana cewa ƙungiyoyin na bayar da kariya ne ga ma'aikatan diflomasiyya zalla da kuma ma'aikata 'yan ci rani da ke samun kuɗi masu tsoka.

Akwai ma'aikata 'yan ci rani da dama da ke fatan gwamnati za ta kawo ƙarshen ƙin jinin baƙi. / Hoto: Reuters

Yawancin 'yan kasar Zimbabwe na iya yin aiki bisa doka a Afirka ta Kudu ta hanyar lasisin aiki na musamman da aka bai wa 'yan kasashen waje daga kasashe makwabta.

"Bizar aiki ta farko da na samu ita ce DZP, izini na musamman da aka ba ’yan ƙasar Zimbabwe. Daga baya an sake ba ni wani izini na musamman mai suna ZSP, sannan kuma takardar izini ta musamman mai suna ZEP,” in ji Mike.

Wa'adi na ƙarshe don neman takardar izinin aiki na musamman na huɗu shi ne Disambar 2024. "Tsarin sabunta izinin aiki ba shi da sauƙi. Ya zama mafi rikitarwa a cikin shekaru kuma yana iya zama mai matukar damuwa," in ji Mike.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuni da cewa jam'iyyar ANC da ke kan karagar mulki tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata shekaru 30 da suka gabata, na fuskantar barazanar rasa rinjayen 'yan majalisar dokoki a hannun jam'iyyar Democratic Alliance (DA), jam'iyyar adawa a hukumance karkashin jagorancin John Steenhuisen, da kuma Jam'iyyar Economic Freedom Fighters ta Julius Malema.

Ana kuma kallon tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, wanda yanzu ke jagorantar jam'iyyar uMkhonto we Sizwe (MK) bayan yin hannun riga da ANC, a matsayin barazana duk da cewa kotun tsarin mulkin Afirka ta Kudu ta hana shi tsayawa takarar shugabancin kasar saboda wani hukunci da aka yanke masa da kuma hukuncin dauri a gidan yari saboda samunsa da laifin cin hanci da rashawa.

Ma’aikata bakin haure irin su Mike, duk da cewa ba za su iya kada kuri’a a zaben ba, amma suna da kwarin gwiwa cewa wata kila gwamnatin hadin gwiwa za ta iya yin aiki don dakile matsalar kyamar baki a kasar.

"Ina da yaƙini kan cewa ANC za ta ci zaɓen, duk da cewa ba da yadda take so ba, don haka akwai yiwuwar a kafa gwamnatin haɗaka," kamar yadda ya yi hasashe.

TRT Afrika