Manyan 'yan takarar shugaban kasa a zaben Gana John Dramani Mahama da Mahamudu Bawumia sanannu ne a fagen siyasar Gana. /Photo: TRT Afrika

Daga Susan Mwongeli

'Yan takara goma sha biyu, masu jefa kuri'a da suka fahimci siyasa, da kuma kasar da ke sa ran samun abubuwa da dama.

A yayin da Gana ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 7 ga Disamba, ana gaf da kammala yakin neman zabe inda ake ganin yadda manyan 'yan takara za su fafata.

Wanda zai gaji shugaba Nana Akufo-Addo da ke kammala wa'adinsa na biyu a ofis, zai fito ne daga cikin wadannan 'yan takara biyu na jam'iyyar NPP mai mulki da na jam'iyyar adawa ta NDC.

An fi mayar da hankali ga dan takarar NPP Dr Mahamudu Mawumia, mataimakin shugaban kasar ta Yammacin Afirka a yanzu haka, da John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC wanda ya taba zama shugaban kasa daga 24 ga watan Yuli, 2012 zuwa 7 ga Janairun 2017.

Dr Bawumia, wanda ya yi karatu a Oxford kuma dan siyasa masanin tattalin arziki ya yi shuhura da tsarinsa na kawo sauyi a cigaban zamani, kuma yana yakin neman zabe da manufofi biyu na farfado da tattalin arziki da cigaban fasaha.

Wa'adin mulkinsa a matsayin mataimakin shugaban kasa ya samu nasara a bangaren sadarwar zamani, duk da ya fuskanci suka kan yadda gwamnati mai ci ke kalubalantar matsalolin tattalin arziki.

A watan Fabrairu, Dr Bawumia ya bayyana karara kan shirinsa na gina tattalin arzikin kasar "mai rauni".

"A lokacin da muka shiga office a 2017, mun fuskanci tattalin arziki mai rugujewa, tare da matsaloli da dama da kalubale mai yawa.

Amma duk da tattalin arziki mai rauni da muka gada, dole ne mu kama aiki mu gyara matsalar," in ji shi, a wani jawabi da ya yi wa kasar.

Bayan watanni goma sha daya, taken yakin neman zane na NP shi ne "Haura shekaru takwas - wanda ke nufin aniyar jam'iyyar na yin mulki sama da shekaru takwas din da Nana Akufo-Addo ya yi.

Abokin hamayya mai tasiri

Amma akwai isassun alamun d ake nuna wannan abu ba mai sauki ba ne ga jam'iyyar mai mulki.

A yayin da Mahama na jam'iyyar adawa ta NDC yake fadin cewa "Kyawun dimokuradiyya shi ne tana ba mu damar mulki na shekaru hudu don kawo sauyi".

Yana daya daga cikin 'yan siyasar Gana kwararru, dan takarar na NCD da aka haifa a 1958 da yankin Damongo na arewacin kasar, ya yi digiri a fannin tarihi tare a aiki a matsayin malamin sakandire.

Siyasar Mahama ta hada da zama mamban majalisar dokoki, mataimakin minista, ministan sadarwa, da kuma mataimakin shugaban kasa.

Ya zama shugaban kasar Gana a watan Yulin 2012 bayan mutuwar shugaba John Atta Mills, inda ya lashe zaben shugaban kasa bayan watanni biyar.

A 2016, ya fadi zabi a hannun Akufo-Addo, a loakcin yana dan takarar jam'iyyun adawa.

Takara mai tazara kadan

'Yan takarar shugaban kasar Gana da ke kan gaba na dogaro kan yankunan da suka fi yawan magoya baya inda suke ta kokarin kira ga 'yan kan katanga a gaf da zaben na 7 ga DIsamba.

Farfesa G Etse Sikanku na Jami'ar Kafafen Yada Labarai da Sadarwa ta Gana (UniMAC) na kallon manyan 'yan takarar shugaban kasar a matsayin suna kai da kai a zaben da zai yanke makomarsu a siyasance da kuma dora kasar bisa turba.

"An san dukkan su a fagen siyasar Gana. Mahama na yakin neman zabe da alkawarin sake fasalin Gana da magana kan tattalin arziki, inda Dr Bawumia kuma yake nasa gangamin da irin ayyukan raya kasa da wannan gwamnatin ta gabatar." ya fada wa TRT Afrika.

"Babban jigon yakin neman zabensa shi ne sauyin tattalin arziki. Ya yi amanna da cewa fasahar sadarwa za ta iya sauya kasar da ciyar da ita gaba."

An haife shi a Tamale da ke arewacin Gana, Dr Bawumia ya yi PhD a fannin tattalin arziki. Kafin shiga siyasa, ya yi aikin banki a Gana, a babban bankin kasar inda har ya kai matsayin mataimakin gwamnan babban banki.

Daya daga cikin hatsarin da ke tattare da bukatar Bawumia na zama shugaban kasa ita ce, shi ne yadda ake da koma baya a kasar a fannin tattalin arziki.

Shi da jam'iyyar NPP ne za a dora wa laifin ciyo bashi da yawa da yadda rayuwa ta yi tsada a kasar wanda hakan ke kara bakantawa jama'a.

Wasu kwararru na tantamar ko zai iya kawo wani sabon abu ga kasar ta Yammacin Afirka.

Duk da haka, yakin neman zaben NPP ya mayar da hankali kan sauyin tattalin arziki, yin alkawarin daukar matakan rage haraji, samar da tsarin jami'a mai saukin kashe kudade, da samar da kamfanin jiragen sama.

"Dr Bawumia na kuma magana game da horar da matasa kan fasahar sadarwa da amfani da yanar gizi saboda adadin mutane da yawa na bukatar ayyukan yi.

Ya yi alkawarin kawo manufofi da tsare-tsare da dama wanda shi da masu taya shi kamfe suka yi amanna za su taimaka wajen daga martabar kasar daga inda take a yanzu," in ji editan Asaase Radio da ke birnin Accra, Willberforce Asare yayin tattaina wa da TRT Afrika.

A wajen Mahama, "kwarewa" ce babban jgon da yake isa ga masu jefa kuri'a.

"Mutane da dama na magana kan kwarewa, amma abinda ke yin aiki shi ne samun ikon isar da manufofin ga tsarin dimokuradiyya mai taimaka wa jama'a.

Ya kuma gina yakin neman zabensa kan doron sanin aiki, yana mai tunatar da jama'a cewa ya taba zama shugaban kasa a baya kuma ya san meye ma'anar shiga wannan ofis din," in ji Farfesa Sikanku.

A loakcin da yake kujerar shugaban kasa kafin Akufo-Addo ya karbi mulki, Mahama ya bayar da fifiko kan samar da kayan more rayuwa.

Mayar da hankali ga tattalin arziki

Sai dai kuma, kasar mai dimbin arzikin zinare na fuskantar kalubalen durkushewar tattalin arziki da karancin lantarki.

Wannan ne ya janyo aka saka masa wani lakabi na "Dumsor", ma'ana "kashewa da kunnawa".

A kokarinsa na sake dawo wa kan mulki, Mahama na fatan masu jefa kuri'a za su zabe shi don ya cika alkawarinsa na sake gina tattalin arziki da samar da karin ayyukan yi.

Asare na kallon wannan a matsayin kalubale. "Yana iya fuskantar wasu matsaloli wajen bayyana wa jama'ar Gana me yake nufi da "tattalin arziki na awanni 24,"

NPP da NDC sun mamaye siyasa Gana tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga Turan mulkin mallaka na Birtaniya a 1957.

Wannan zabe ba wai wani sabon abu ba ne. Dukkan jam'iyyun sun dogara kan yankunan da suka fi yawan magoya baya, inda suke kuma jan hankalin wadanda ke kan katanga.

"A kasarmu, kana bukatar kashi 50+1 na kuri'un da aka jefa don lashe zabe. Domin yin hakan, kana bukatar ka samu gangarowar masu jefa kuri'a zuwa bangarenka," in ji Asare.

Idan babu dan takarar da ya samu sama da kashi 50 a zaben, to 'yan takara biyu da suka fi samun kuri'a za su fafata a zagaye na biyu.

Gare ku masu jefa kuri'a.

TRT Afrika