Rumfar Zabe a Nijeriya/ AA

Wannan zabe yana da muhimmanci sosai musamman a irin wannan lokaci da tattalin arzikin kasar ke fuskantar koma-baya, da kuma matsaloli irin na tsaro.

Ko a farko-farkon watan Janairun 2023, sai da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na kasar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya yi gargadin cewa zaben na fuskantar hadarin soke shi ko daga shi saboda ta’azzarar da matsalar tsaro ke yi.

Sai dai gwamnatin Nijeriya ba ta mayar da martani kan kalaman Farfesa Yakubu ba.

Zaben zai zama karo na bakwai a Nijeriyar tun bayan komawarta turbar dimokradiyya a shekarar 1999, bayan shafe gwamman shekaru tana karkashin mulkin soja.

Tsarin zaben da Nijeriya ke bi irin na shugaban kasa ne da ‘yan majalisun dokoki na tarayya da gwamnonin jihohi da kuma ‘yan majalisun jihohi.

Wato dai tsarin zabenta irin na Amurka ne ba irin na Birtaniya mai firaminista ba.

Masu sharhi kan al’amura a Nijeriyar tuni suka fara tsokaci kan yadda suke ganin zabukan bana za su kasance.

“A fahimtata zaben bana zai fi duk na baya karbuwa saboda dokar zaben da shugaban kasa ya sa wa hannu a bara,” in ji shugaban kungiyar kasa ta kasa ta Care International a Nijeriyar, Dr Hussaini Abdu.

Masanin ya ci gaba da cewa “dokar zaben ta fitar da kudurori da dama don karfafa zabe da amfani da na’urorin fasaha na zamani da za su taimaka kwarai wajen dakile magudin zabe, da ya zama ruwan dare a kasar.”

To bari mu yi duba dalla-dalla kan yadda tsarin zaben yake a Nijeriyar.

Yaushe ake zabe a Nijeriya?

Dimokradiyya ta dawo a Nijeriya ne a shekarar 1999, inda aka yi zabe a watan Fabrairu.

Shi ne zaben dimokradiyya na farko tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 1993.

Tun daga 1999 din kuma ake yin zaben duk bayan shekara hudu, inda ake fara na shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya a Fabrairu sai na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a watan Maris.

Sai dai kundin tsarin mulkin kasar ya yarda mutum ya sake tsayawa takara, wato bayan shekara hudun farko, to ana iya yin tazarce don neman karin wata shekara hudun.

Amma wannan tsari yana aiki ne a kujerun shugaban kasa da na gwamnoni kawai, yayin da ba a iyakancewa majalisun dattawa da wakilai da na dokokin jihohi ba.

Su wa ake zaba a Nijeriya?

Nijeriya tana da yankuna shida ne da suka hada da arewa maso gabas mai jiha shida da arewa maso yamma mai jiha bakwai da arewa ta tsakiya mai jiha shida.

Sai kudu maso gabas mai jiha biyar da kudu maso yamma mai jiha shida sai kuma kudu maso kudu mai jiha shida, inda jumullar jihohin ya zama 36.

Al’ummar Nijeriya na zaben shugaban kasa wanda yake tafe da mataimakinsa, sai ‘yan majalisar dattawa 109, uku daga kowace jiha sai daya daga birnin tarayyar kasar, sai kuma ‘yan majalisar wakilan tarayya 360 duk daga fadin kasar.

Duk da cewa kasar na da jihohi 36 ne, a 2023 za a yi zaben gwamnoni a jiha 28 ne kawai sai kujerun majalisun dokoki 993, saboda yadda shari’o’in zabuka a baya suka sa na sauran jihohi takwas din suka bambanta.

Su waye masu zaben?

Duk dan kasa da yake da shekara 18 zuwa sama yana da damar kada kuri’a, a kasar mai yawan jama’a fiye da miliyan 200 da kabilu sama da 370.

Kazalika duk mai son yi zabe dole sai ya mallaki rijista mai dauke da bayanansa da kuma hotonsa, wadda hukumar zabe ke yi.

Wani abu da ke da daure kai shi ne na yadda adadin mutanen da aka yi wa rijista a zaben bana bas u kai ko rabin yawan al’ummar kasar ba.

INEC ta ce ta yi wa mutum 93,469,008 rijista, inda jihar Legas, cibiyar kasuwancin kasar ke kan gaba da mafi yawan masu rijista har 7,060,195, yayin da jihar Kano da ta fi kowacce yawan al’umma kuma cibiyar kasuwancin arewacin Nijeriya take da mutum 5,921,370.

“’Yan shekara 18 zuwa 34 su ne suka fi yawa a cikin masu katin zabe a 2023 da yawan su ya kai 37,060,399, wato kashi 39.65 cikin 100.

“A jumullar yawan mutanen gaba daya kuma 49,054,162 wato kashi 52.5 cikin 100 maza ne yayin da 44,414,846 kashi 47.5 cikin 100 mata ne,” in ji Farfesa Yakubu a jawabin da ya yi.

Manyan ‘yan takara a zaben

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 11 ga watan Janairun 2013 ya ce jam’iyyu 18 ne ke da ‘yan takara a zaben na 2023, sai dai hudu ne suka fi jan hankulan ‘yan kasar a fafatawar.

Akwai dan takarar jam’iyya mai ci, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne kuma jagaban jam’iyyar ta APC, wato Bola Ahmed Tinubu mai shekara 70.

Jam’iyyar Labour na da dan takara Peter Obi mai shekara 61 kuma tsohon gwamnan jihar Anambra ne a kudu maso gabashin kasar.

Tsohon gwamnan jihar Kano a arewa maso gabashin Nijeriya mai shekara 66 Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ne dan takarar jam’iyyar NNPP.

Ita kuwa babbar jam’iyyar adawa ta kasar PDP ta tsayar da Alhaji Atiku Abubakar mai shekara 76 wanda tsohon mataimakin shugaban Nijeriyar ne.

Rumfunan zabe

Akwai rumfunan zabe 176,846 a fadin Nijeriyar.

Ana bude rumfunan zabe da misalign karfe 8 na safe agogon kasar, wato 7 agogon GMT, inda ake farawa da tantance mutane kafin daga bisani su kada kuri’unsu.

Sai kuma a rufe rumfunan ta hanyar dakatar da zabe da misalin karfe 4 na yamma.

INEC ta ce a tsari dole a samu jami’anta hudu a kowace rumfar zabe, hakan ne ma ya sa ta dauki Karin ma’aikata na wucin gadi har miliyan 1.4, kamar yadda wata jami’a mai magna da yawun hukumar Zainab Aminu ta gaya wa TRT.

Kowace jam’iyya na da damar ajiye wakilanta da ake kira ejen a kowace rumfa, baya ga dumbin jami’an tsaro na ‘yan sanda da ake jibgewa.

Yawan ‘yan sandan Nijeriya dai ya kusa 400,000, “kuma duk wani jami’in dan sanda da ke kasar zai kasance a bakin aiki a ranar zabe,” kamar yadda wani babban jami’I ya gaya wa TRT Africa.

Kazalika baya ga masu zabe, ana samun masu sa ido na kasashen waje da na cikin gida da ‘yan jarida da ke halartar rumfunan zabe.

Dr Hussaini Abdu wanda ya sha kasancewa cikin masu sa ido kan zabuka a kasar kuma a bana ma zai yi hakan karkashin kungiyar Yiaga Africa, ya ce sa ido a zabuka irin wannan ya zama dole.

“Muna hakan ne don tabbatar da cewa abin da aka gudanar ya samu karbuwa bisa dokoki da kudurorin da kasashen duniya suka sa wa hannu kamar Majalisar Dinkin Duniya da ECOWAS da AU.

“Sannan sa idon na da amfani don tabbatar da cewa gwamnati mai ci ko hukumar zabe ba su yi magudi ba. Kuma al’umma ma sun fi yarda da masu sa ido irinmu fiye da hukumomi,” in ji masanin, wanda har hukumomi na Amurka da Tarayyar Turai kan yi aiki da shi.

Tsarin yin nasara

Kamar tsarin zabe ya bambanta a kasashe da dama, haka ma tsarin cin zaben yake da bambanci.

A wata ganawa da ya yi da kungiyar Tarayyar Turai ranar 12 ga Janairun 2023, wani babban jami’in INEC Festus Okoye ya ce mataki ce mataki na farko ga duk dan takarar shugaban kasar da yake son cin zabe shi ne dole ya fi sauran yawan kuri’u.

Mataki na biyu kuwa dole dan takara na bukatar samun kashi 25 cikin 100 na kuri’un kashi biyu bisa uku na jihohin kasar 36.

Wato dai bayan yawan kuri’u, to sai kuma idan mutum ya yi nasara a jihohi 24 cikin 36 da ake da su.

Idan kuma ba a samu wanda ya yi nasara ba bisa wannan tsari, to za a je zagaye na biyu tsakanin dan takara mafi yawan kuri’u da wanda ya fi samun kuri’u a kashi biyu bisa uku na jihohin kasar.

Sai dai duk da cewa ba a taba zuwa zagaye na biyu ba tun da ake yin zabe a Nijeriya, a wannan karon masu sharhi na has ashen hakan na iya faruwa.

Dr Abdu ya ce “Abin da ya sa wasu ke ganin hakan ka iya faru shi ne don a da tseren yawanci na jam’iyyu biyu ne kawai a gaba-gaba, amma wannan karon jam’iyyu hudu ne masu karfi a kan gaba.

“Shi yasa ake ganin idan har masu zabe suka kacaccala to sai an koma zagaye na biyu,” y ace.

To ko zuwa zagaye na biyu ka iya zame wa hukumar zabe ta INEC kalubale? Tambayar kenan da na yi wa wata jami’a mai magana da yawun hukumar Zainab Aminu.

Ta ce “Tuni mun yi shirinmu tsaf ko da hakan ta kasance. Don har mun tanadi takardun kuri’a da za a yi amfani da sui dan har hakan ya faru.”

Bayan kamala zabe kuma INEC ce take da alhakin sanar da sakamakon a hukumance tare da mika wa wanda ya yi nasara sakamakonsa.

Yaushe ake rantsar da wanda ya yi nasara?

Tun daga 1999 ana rantsar da sabon shugaban kasa da sabbin gwamnoni ne a ranar 29 ga watan Mayun shekarar da aka gudanar da zaben.

Amma a wannan karon za a rantsar da su ne a ranar 12 ga watan Yuni, bayan da shugaba mai ci Muhammadu Buhari ya sauya hakan a shekarar 2018.

TRT Afrika