Tun bayan kafa Jumhuriyar Turkiyya a 1923 karkashin jagorancin Mustafa Kemal Ataturk, Turkiyya ta zama kasar da ke dabbaka dimokradiyya da jam’iyyu da dama.
Ga dai bayanin yadda zabuka suka kasance tsawon shekara 100 a kasar.
Duk da samun katsalandan na sojoji a wasu lokutan, wanda ya kawo tsaiko ga tsarin siyasar Turkiyya a 1960 da 1971 da 1980 da 1997 da kuma 2007, kasar ta yi kokarin gudanar da zabuka tun bayan da ta koma amfani da jam’iyyu da dama a 1950.
Tun daga 1923 da aka kafa Jumhuriyar Turkiyya zuwa 1950, jam’iyya daya ce ta jagoranci kasar wadda mutumin da ya jagoranci kafa Jumhuriyar ya kafa ta, Mustafa Kemal wanda kuma ya rasu a 1938.
Zabukan da aka yi a wadannan lokuta kawai dai na je-ka-na-yi-ka-ne saboda Jam’iyyar CHP da ba ta da abokan hamayya ce ke lashe kujerun ‘yan majalisar dokoki.
Amma hakan ya sauya a zaben 1950, a lokacin da karin jam’yyu suka samu damar tsayar da ‘yan takara, kuma Jam’iyyar DP ta masu ra’ayin rikau ta samu gagarumin rinjaye tare da kafa gwamnati.
Tun wannan lokaci, sai jam’yyu masu ra’ayin rikau suka mamaye siyasar Turkiyya, a yayin da CHP da ba ta samun kuri’un da take so, ta zama babbar jam’iyyar adawa.
A watan nan na Mayu kasar za ta sake yin babban zabe mai muhimmanci matuka.
Ga dai yadda zabukan Turkiyya suka kasance shekara 100 da suka gabata:
Tasirin Daular Usmaniyya
Tarihin zabukan Turkiyya na koma wa ga Daular Usmaniyya, daular da Jumhuriyar Turkiyya ta maye gurbi, wadda ta shugabanci bangare mai girma na Gabas ta Tsakiya da yankuna masu yawa na Balkan a karni na 19.
A karshen karni na 19 ne daular ta fara rugujewa a lokacin da shugabanni da masu fada a ji na Daular Usmaniyya suka fara tunanin akwai bukatar kwaskwarima ga yanayin siyasar daular mai kabilu da mabiya addinai daban-daban wanda hakan ne zai hana ta rushewa.
A 1876, sakamakon shirin kwaskwarima na Daular Usmaniyya, daular ta koma mai aiki da kundin tsarin mulki da majalisar dokoki da aka zabi mambobinta.
An gudanar da zabe na farko a 1876 da 1877 a lokacin da Majalisar Dokoki ta yi wata doka wadda ta kasance ana aiki da ita har zuwa 1943 lokacin Jumhuriyar Turkiyya.
Amma wannan majalisa ba ta iya gudanar da ayyuka yadda ya kamata ba saboda dalilai da dama, kuma Sarkin Daular Abdulhamit II ya dakatar da ita har zuwa 1908.
A lokacin da zangon kundin tsarin mulki na biyu ya kama, lokaci ne da Kwamitin Hadin Kai don Cigaba, reshen siyasa na Kungiyar Matasan Turkawa ya kama mulki.
Bayan zabukan 1908, an sake bude Majalisar Dokokin Daular Usmaniyya a Istanbul, kawancen CUP ne ya lashe kusan dukkan zabe a fadin Daular.
A lokacin da CUP ke kiran kansa a matsayin kawancen kawo sauye-sauye, amma sun dinga amfani da hanyoyin dakile abokan hamayyarsu na siyasa.
CUP sun dinga magudin zabe ta hanyar amfani da jami’an tsaro da sauran hukumomi inda suke ayyana nasararsu a zabukan ‘yan majalisu.
Bayan 1913, CUP suka kafa tsarin jam’iyya daya inda suka jagoranci kasar har zuwa Yakin Duniya na I.
Zabukan lokacin yaki
A karshen Yakin Duniya na I, kawancen kasashen Yamma sun afkawa kusan dukkan iyakokin Daular Usmaniyya.
A 1919 Mustafa Kemal ya jagoranci Yakin Kwatar ‘Yancin Kan Turkawa daga hannun Ingila da Faransa da suka mamaye su.
Duk da cewar ‘yan mamayar sun yi alfahari da samun gwamnatocin dimokradiyya, sun rufe Majalisar Dokokin Daular Usmaniyya tare da korar dukkan shugabanninta zuwa kasashen waje a 1920.
A wannan shekarar ne Ataturk da magoya bayansa suka yi kira da a kafa sabuwar Majalisar Dokoki a Ankara, garin da ba a mamaya ba, sannan suka yi kira da a gudanar da zabe a garuruwan da ba a mamaye ba don zabar ‘yan majalisar da za su taho Ankara.
An sakawa majalisar suna Babbar Majalisar Kasa ta Turkiyya, sunan da ake amfani da shi har yanzu ga Majalisar Dokokin Turkiyya.
Bayan zabukan 1920, an zabi shugabanni a zauren Majalisar Dokoki ta Ankara, ‘yan majalisar na Istanbul ma da suka fito daga majalisar Daular Usmaniyya sun zama mambobi a Ankara, garin Anatoliya ya zama hedikwatar Turkiyya.
Wannan zabe na da muhimmanci saboda Majalisar Dokokin Ankara ta samu nasarar jagorantar yakin kwatar ‘yancin kai inda aka fatatattaki Turawan mamaya.
Wani zaben mai muhimmanci da aka sake yi shi ne na watan Yunin 1923 kafin sanar da kafa Jumhuriyar Turkiyya a watan Oktoban shekarar, wanda daga nan ne aka bar tsarin Daula zuwa Jumhuriyya.
Wannan majalisa da aka kafa lokacin yaki na da wani salon a dimokradiyya saboda yadda take da bangarori biyu, rukunin Farko da Rukuni na Biyu wanda suke da ra’ayoyi mabambanta game da yadda za a tafiyar da Turkiyya.
Babbar Majalisar Kasa ta Turkiyya ta yi nasarar Yakin Kwatar ‘Yancin Kai. Amma wadannan kungiyoyi guda biyu na da sabanin ra’ayi kan yarjejeniyar zaman lafiya da Turawa ‘yan mamaya.
A lokacin da rukunin farko da Mustapha Kemal Ataturk ke jagoranta suke kira da a amince da Yarjejeniyar Lousanne, rukuni na biyu kuma da ‘yan siyasa masu ra’ayin rikau suka mamaye suke kira da kar a yi hakan.
Sakamakon haka Mustafa Kemal da magoya bayansa suka rusa Majalisar Dokoki, suka yi kira da a gudanar da sabon zabe don a samu sabuwar Majalisar Dokoki da za ta goyi bayan zaman lafiya.
1923-1950: Zabuka karkashin jam’iyya daya tilo
A 1923 zabuka sun yi manyan tasiri saboda yadda aka fara da jam’yya daya tilo, wadda ba ta fuskanci wata jam’yyar adawa ba a zabuka biyar da aka gudanar a 1927 da 1931 da 1935 da 1939 da kuma 1943.
Kungiyoyin adawa irin su PRP da FRP sun dan bayyanu kadan inda aka rufe su ta yadda ba za su iya shiga zabe ba.
Majalisar Dokoki ta sake zabar Mustafa Kemal Ataturk a matsayin Shugaban Kasa sau hudu.
Bayan mutuwar Ataturk, an ci gaba da mulkin jam’iyya daya karkashin Ismet Inonu, shugaban kasa na biyu wanda shi ma aka zabe shi har sau hudu a matsayin shugaban kasar.
Sakamakon Yakin Duniya na II, tsarin shugabanci na jam’iyya daya a Turkiyya ya bayar da damar kafa jam’iyyu a karon farko tun bayan kafa Jumhuriyar.
Jam’iyyar DP ta adawa wadda mambobinta tsofaffin ‘yan Jam’yyar CHP ne sun samu damar shiga zabe. Wannan ne karon farko da aka koma amfani da jam’iyyu da dama a siyasar Turkiyya.
A lokacin da aka bai wa wasu jam’iyyu damar shiga zabe a 1946, CHP ta yi amfani da abubuwa da dama wajen matsa lamba don kalubalantar DP, jam’iyyar masu ra’ayin rikau, wadda ke cikin jam’iyyun da shugaban kasar Turkiyya na yanzu Recep Tayyip Erdogan ya tasirantu da su wajen kafa jam’iyyarsa ta AKP a 2001.
Sakamakon haka da yawan mutane suka bayyana zaben 1946 a matsayin “wanda aka yi magudi”, sannan CHP ta yi wasu dokoki da masu nazari suke wa kallon ba su dace da tsarin dimokradiyya ba, a ganin masu sharhi da dama.
Zaben 1950
Duk da matsin lamba da babakeren CHP, Jam’iyyar DP ta taso tare da bunkasa wanda wannan zabe ya bayyana hakan karara inda jam’iyyar ta masu ra’ayin rikau ta samu rinjaye a Majalisar Dokoki karkashin Adnan Menderes.
Masanin tarihi Baturke-Ba’amurke Kemal Karpat ya kira wannan al’amari da ‘Babban Sauyi a Siyasa da Zamantakewar Turkiyya”.
A lokacin yakin neman zabe, wata fastar Jam’yyar DP da ke nuna hannu yana rubuta “Ya isa, mutane na da ‘yancin yanke hukunci” ya yi tasiri sosai a zukatan masu jefa kuri’a da suka kasance karkashin mulkin CHP na tsawon shekaru.
“Hatta magoya bayan CHP ma sun tasirantu da wannan fastar” kamar yadda Mehmet Oznur Alkan, Farfesa Kan Kimiyyar Siyasa a Jam’ar Istanbul ya rubuta.
Bayan zaben 1950, Jam’iyyar DP ta lashe zabuka biyu da suka biyo baya na 1954 da 1957 inda Majalisar Dokokinta mai rinjaye ta zabi Celal Bayar a matsayin shugaban kasar har sau uku.
Amma a 1960 juyin mulki na farko a Turkiyya ya kawo karshen mulkin DP.
1960-1980: Juyin mulki da yawa tare da zabuka
Juyin mulkin 1960 ya rushe Jam’iyyar DP kuma sojoji suka daure shugabanninta. Har ta kai ga an zartar da hukuncin kisa ga Firaminista Adnan Menderes da Ministan Kudi Hasan Polatkan da Ministan Harkokin Waje Fatih Rustu Zorlu.
A takaice dai wannan juyin mulki ya saka siyasar Turkiyya a hali mai muni.
Daga baya an kirkiri sabuwar dokar zabe inda aka rungumi tsarin D’Hondt. Wannan ya tanadi raba kujerun Majalisar Dokoki daidai da yawan kuri’un da aka samu a kowanne yanki. Wannan ne tsarin da ake ci gaba da aiki da shi har yau a Turkiyya.
Duk da mummunan juyin mulkin da aka yi, jam’iyyun masu ra’ayin rikau sun lashe mafi yawan kuri’u a zaben 1961.
Jam’iyyar AP karkashin Suleyman Damirel ta masu saukin ra’ayi amma masu riko da addini da ya jagoranci gwamnatocin ra’ayin rikau daban-daban daga 1960 zuwa 1990, ta zama wani ci gaba na Jam’iyyar DP.
Jam’yyar AP ta lashe zabukan 1965 da na 1969, inda take samun rinjaye a Majalisar Dokoki kuma take kafa gwamnatin masu ra’ayin rikau karkashin Demirel.
Amma wani juyin mulkin a 1971 ya sake tafiyar ruwa da gwamnatin Demirel, wanda wani sabon kutufo ne ga dimokradiyyar Turkiyya.
Dokar da sojoji suka kirkira a 1971 ta bayar da damar kafa gwamnatin hadaka.
Hadin kan Demirel da shugabannin soji ya janyo masa kalubale babba inda tun daga sannan babu wata jam’iyya a karkashinsa da ta iya lashe zabe ita kadai.
CHP karkashin Bulent Ecevit ta zo ta farko a zaben 1973, ta kafa gwamnatin hadaka da ba ta jima ba tare da Jam’iyyar NSP — jam’iyyar masu ra’ayin rikau.
Har zuwa zaben 1977, kamar yadda ya kasance a 1973, gwamnatocin hadaka marasa rinjaye ne suke jagorantar Turkiyya.
Wannan ya ci gaba har zuwa juyin mulkin 1980 wanda ya rushe dukkan tsarin siyasar Turkiyya tare da soke dukkan jam’iyyu.
Daga 1980 zuwa 2000: Dawowar hadakar jam’iyyu
Bayan juyin mulkin 1980, an gudanar da zaben farko a 1983 inda Jam’iyyar ANAP karkashin Turgut Ozal, mai ra’ayin rikau kuma da ya fito daga tushen MSP kamar Erdogan ta samu nasarar rinjaye a Majalisar Dokoki.
Jam’yyar Ozal ta sake lashe zabe a 1987. Tsarin samun kaso 10 na kuri’un da aka jefa kafin jam’iyya ta samu damar samun kujera a majalisa ya taimakawa nasarar Ozal.
Wannan tsari ne da ‘yan siyasa masu alaka da juyin mulki suka samar don ganin an samu zaman lafiya da daidaito a siyasance.
Amma bayan an zabi Ozal a matsayin shugaban kasa, sai ANAP ta fara durkushewa ta kuma fadi zaben da aka yi a 1991.
A tsakanin 1991 da 2002, lokacin da AKP ta hau karagar mulki, babu wata jam’iyya da ta yi nasara ita kadai a majalisa wajen kafa gwamnati a zabukan 1995 da 1991.
Gwamnatocin hadaka ne suka mamaye fagen siyasar Turkiyya.
2002-2023: Nasarorin Jam’yyar AKP
A karkashin shugabancin Erdogan, AKP ta mamaye siyasar Turkiyya inda ta dinga yin nasara a jejjere a 2002 da 2007 da 2011.
A watan Yunin 2015 ne Jam'iyyar AKP ta rasa rinjaye a Majalisar Dokoki, amma ta sake samun rinjayen bayan sake zabe a watan Nuwamban wannan shekarar.
An sake zaben ne bayan da jam’iyyun da suka shiga majalisa suka gaza kafa gwamnatin hadin kai.
Bayan sauya tsarin shugabanci daga majalisa zuwa na shugaban kasa mai cikakken iko ta hanyar kuri’ar jin raba gardama da aka jefa a 2017, Erdogan ya sake lashe zaben shugaban kasa a 2018 a matsayin kawancen al'umma wanda ya hada jam’yyun AKP da MHP, sun kuma samu rinjaye a Majalisar Dokoki.
Tare da zaben shugaban kasa na shekarar 2023 da za a gudanar a tsakiyar watan Mayu, an sanya idanu don a ga yadda siyasar Turkiyya za ta kasance inda kawancen da AKP ke jagoranta zai fafata da kawancen jam’iyyu shida da CHP ke jagoranta.