Daga Benjamin Sivanzire
Gilbert Mapepe, wani matashi ne dan kasar Cango, yake shiga irin ta 'yan kwalisa masu ado da aka fi sani da 'archetype sapeur' ko kuma wanda ya yi karatu a yankin da ke magana harshen Faransanci ta 'La Sape' inda mutum kan cancara ado tun daga kai har zuwa kafa.
A wata kasuwa da ta cika da samfuran kayayyakin da ake shigo wa da su daga ko'ina a fadin duniya, 'dan kwalisan matashin wanda ya fito daga garin Kisangani a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Cango ya shahara wajen kawata wa kansa da duk wani abu da aka yi shi daga kasarTurkiyya.
"Ina saka samfuran kayayyakin Turkiyya a jikina kamar yadda nake ciN abinci a kowace rana, Gilbert ya shaida wa TRT Afrika yayin da yake sanye da samfurin rigar Fernando na Turkiyya.
Ko da yake dalibin wanda ke shekararsa ta biyu a karatun fannin kimiyyar Kwamfuta ba shi kadai ba ne ya ke da sha'awar ado da tufafin Turkiyyar.
A kan manyan titunan Kisangani, birni na uku mafi girma a Kongo, Kayayyakin kasar Turkiyya ne aka fi bukata saboda inganci da kuma araharsu, Shagunan sayar da kayayyakin suna dada cika da batsewa a dukkan fadin birnin.
A gefen babbar hanyar da ke cike da cunkoson jama'a a cibiyar kasuwanci ta Makiso, wani dan kasuwa ne Bienvenu ya ke siyar da wasu kayayyaki 'yan kanti "na komai da komai daga Turkiyya" domin ya iya samar da bukatun abokan cinikinsa.
Wani lokaci Bienvenu yakan yi jiran makonni kafin kayayyakin da ya yi odar su daga Turkiyya su iso hannunsa.
Tashar farko da kayayyakin suke sauka ita ce Kinshasa, sama da kilomita 1,200 daga ainihin wajen da ake siyar da su.
Wasu lokutan, samfuran kayayyakin da ake odar shigowarsu ta kamfanonin tafiye-tafiye ba sa isowa da wuri saboda jinkiri da ake samu a wajen fannin tsare-tsare.
Duk da haka, kasuwancin Bienvenu na dada habaka duk da hatsarin da ke tattare da da yinsa.
Boro Ezanga Kombo, daya daga cikin takwarorin Bienvenu a kasuwanci, ya tabbatar da cewa yadda tufafin Turkiyya suke kara karbuwa ya wuce duk wasu wahalhalu da ake fuskanta.
'Couture Culture' wani kanti ne na sayar da kayan sawa da ke kusa da na shagunan Bienvenu.
Cédric Molimo ne ya zo siyan kwat da wando, su ne irin suturun da ya ke sha'awar sanyawa yayin da ya ke shirin gabatar da karatunsa na karshe a fannin ilimin sadarwa.
Ba ya so ya bar komai a baya wajen burge alkalan da su saurari gabatarwasa , yana da tabbacin cewa yanayin shigarsa za ta taka rawa mussamman a lokacin.
Zabin tufafin da Molimo ya yi don babban ranar an shigo da su ne daga Turkiyya.
"Dole ne mutum ya yi kyau - babu wata hanya da ta wuce haka," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika bayan kashe dalar Amurka 120 a siyan rigar kwat din da wando.
Kamar dai Gilbert, David Wangu, wani kwararren mai daukar hoto kuma mai sha'awar kayayyakin ado, masoyin tufafin Turkiyya ne, Kuma a shirye yake ya biya kudin duk wani tufafi da yake so.
Yayin da ya ke samun kwarin gwiwa ta hanyar tallace-tallace da gidan silima da kuma shawarwari daga abokan aikinsa, David bai boye kansa daga mallakar durowar sabbin kayayyakin Turkiyya ba.
"Na sayi wannan akan dala 150, dayan kuma akan dala 250," David ya nuna hotunan da ya dauka a cikin kwanfutansa ta laptop.
"Don yin ado da mai kyau, ba sai mutum ya jira ya kai wani matsayi babban a aikinsa ba," in ji shi.
Schadrack Mukohe da abokansa sun shagaltu da wayoyinsu wajen kallon wasan kwaikwayon Turkiyya mai suna Soz don sanin abubuwa da ke faruwa, da nufin samun wasu samfuran shiga daga babban jarumin fin din, Tolga Saritas.
Suna masu godiya ga aikinsu na zane-zane, za su iya yin oda ta yanar gizo don samun sabbin tufafin da ake yayi a Turkiya, Sun yi imanin cewa cancara ado mai kyau zai taimaka musu wajen samun ci gaba a burinsu na sauran sha'awar yin waka.
Kungiyar matasan suna da burin amfani da samfuran kayayyakin da sauran abubuwa wajen hada bidiyon da suke shirin yi a wata mai kamawa.
Dangantakar kasuwanci mai karfi
Farfesa Daddy Saleh, kwararre kan ci gaban tattalin arzikin kasashen kudancin kasar, ya danganta tasirin da Turkiyya ke da shi kan salon sauturar kasar Congo da “inganta hadin gwiwar kasashen biyu cikin sauri.
"Wannan wani sabon salo ne na sake farfadowa bayan barkewar cutar ta duniya. A shekarar 2022, an yi kiyasin cewa ciniki tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka miliyan 40, in ji shi.
“Sabbin yarjejeniyoyin da suka shafi tsaro da sufuri da ababen more rayuwa da sauran fannonin tattalin arziki sun inganta.
Ana ci gaba da kiraye-kiraye a DRC kan batun cin gajiyar kwarewar kasuwancin Turkiyya don horar da 'yan kasar su shiga a dama da su.