Shugaban Turkiyya  ya ziyarci kasashe fiye da 30 na Afirka cikin ‘yan shekarun nan /  Photo: AA

Yadda yanzu Turkiyya ke tashe a nahiyar Afirka, abu ne da ba kasafai ake gani ba a can shekarun baya.

To amma kasar ta bayyana karara cewa ta himmatu wajen kyautata hulda da Afirka a matsayin ‘’daya daga cikin ginshikan’’ tsarinta na hulda da kasashen waje ta fuskoki daban-daban.

Ta ce tana yin hakan ne saboda nahiyar na kara taka rawa da kuma kasancewa mai muhimmanci a ‘’fagen lamuran duniya.’’

Shugaba Recep Tayyip Erdogan wanda alamomin girmamawa na kasarsa suka hada da tauraruwa da kuma jinjirin wata, ya nuna cewa da gaske yake domin ganin ta haska a Afirka.

Ya karade Afirka, inda ya ziyarci kasashe fiye da 30 cikin ‘yan shekarun nan, yana jadda manufofin kasarsa da kuma sanya hannu kan yarjeniyoyi da nufin karfafa huldar tattalin aziki, da siyasa da al’adu da ilmi da kuma hadin kai ta fuskar tsaro da soji.

Adadin ziyarar da Erdogan ya kai Afirka, abu ne da ba a saba ganin wani shugaba na yi ba, kuma alama ce ta aniyarsa wajen inganta hulda tsakanin Turkiyya da Afirka.

Alkaluma daga Ma’aikatar Harkokin waje ta Turkiyya na nuni da cewa harkokin cinikayya sun karu daga kimanin naira biliyan biyar a 2003 zuwa naira biliyayan fiye da 34 a 2021 abin da ke alamta aruwar cinikayyar cikin hanzari.

Su ma kamfanonin Turkiyya sun gudanar da ayyukan raya kasa da ilmi da kuma jin kai da suka kai na naira biliyan 78 a sassa daban-daban na Afirka.

Turkiyya tana kuma da yarjejeniyoyin cinikayya ba tare da shamaki ba tsakaninta da wasu kasashen Afirka da suka hada da Masar da Moroko da Mauritius da kuma Tunisiya, domin saukaka harkokin kasuwanci da na tattalin arziki.

A shekara ta 2021, lokacin da shugaban Turkiyya ya ziyarce shi a Abuja, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana hulda tsakanin kasarsa da Turkiyya a matsayin ‘’mai kwari da kyawu kuma ta kud-da-kud.’’

‘Turkiyya na samun karuwa, Afirka na samun karuwa’

Shugaba Erdogan ya ce alamomin girmamawa na kasarsa da suka hada da tauraruwa da jinjirin wata na nuna da gaske kasar take don ganin ta haska a Afirka/Photo AA 

A cewar ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya, kasar na da aniyar aiki tare da kasashen Afirka ta fuskar tarihi, da al’adu da zamantakewa.

Sannan da albarkatun kasar da ke nufin ‘’amfanar juna’’ da kuma tsarin ‘’magance matsalolin Afirka ta hanyoyin da suka dace da Afirka.’’

A cewar Ambasada Sulaiman Dahiru, wani tsohon babban jami’in difilomasiyyar Nijeriya, ‘’Turkiyya ta nuna basira’’ saboda yadda take mayar da hankali ga Afirka da nahiyar Asiya a tsarinta na hulda da kasasehn waje.

Ambasada Dahiru na da ra’ayin cewa ‘’ana samun nasara’’ a hulda tsakanin Turkiyya da Afirka saboda Turkiyya na amfana daga kasuwannin Afirka, su kuma kamfanonin Turkiyya da ke aiki a Afirka na taimaka wa wajen ayyukan raya kasa a nahiyar da kuma samar da ayyukan yi.

Ya ce: ‘’Turkiyya kasa ce da ci gaba, tana da karfin tattalin arziki, tana da karfin masana’antu. Don haka yayin da kamfanoninta su ke birjik a Afirka, lamarin zai kasance karuwa ga Afirka kuma karuwa ga Turkiyya.’’

Yanzu dai ana yawan samun kayan da kamfanonin Turkiyya ke yi kamar kujeru da gadaje, da tufafi da motoci da kuma kayan alatu na lataroni da ma kayan abinci.

Mutane da dama kan sayi kaya kai tsaye daga Turkiyya a kawo yanzu gida a Afirka, saboda intanet da kuma ingancin tsarin kasuwanci.

A 2021 lokacin da shugaban Turkiyya ya ziyari Nijeriya, Shugaba Buhari ya ce hulda tsakanin kasarsa da Turkiyya ta kud-da-kud ce/Photo AA

Wata alama karara ta huldar kasuwanci da tattalin arzikin ita ce yadda ake samun karuwar zirga-zirgar kamfanin sufurin jirgin sama na Turkish Airlines wanda mallakin gwamnatin Turkiyya ne, da jiragensa ke sauka a kasashen Afirka da dama.

Matasa na ribibin zuwa karatu a Turkiye.

A cewar Mrs Idayat Hassan, daraktar Cibiyar Kyautata Dimokuradiyya da Raya Kasa wato Centre for Democracy and Development a Nijeriya, Turkiyya ‘’ta samu nasarar jawo ra’ayin mutane da dama a Afirka’’ ta hanyar amfani da ‘’dabarar lalama’’

Mrs Hassan ta shaida wa TRT Afrika cewa dabarar Turkiyya ta zuba jari a fannin ilmi ga ‘yan Afirka, da bayar da dama samun kiwon lafiya da kuma horar da ma’aikata a fannoni daban-danan tare da karfafa hulda ‘’tsakanin al’umomi da kuma tsakanin gwamnatoci’’ ta kasance ‘’mai kayatarwa ga mutane da dama.’’

Ingancin ilimi a Turkiyya ya sa kasar ta kasance daya daga cikin wuraren da aka fi zuwa neman ilmi a duniya/Photo AA

Akwai makarantu da dama da Turkiyya ke ba da kudin gudanar da su a Afirka yayin da gwamnatin Turkiyya ta bai wa dalibai fiye da 15,000 tallafin karo ilmi a kasar, galibinsu matasa daga Afirka, cikin kimanin shekaru fiye da 20 da suka gabata.

Haka nan wasu dubban kuma sun tafi karatu a kasar sakamakon tallafin gwamnatocin kasashensu ko kuma su suka dauki nauyin kansu kuma adadin na karuwa a kullum.

Wannan ya sa Turkiyya ta kasance daya daga cikin wuraren da aka fi zuwa neman ilimi a duniya.

Moustafa Aminou Tukur, wani dan Nijeriya dake karatu a Jami’ar Fasaha ta Yildiz da ke Istanbul ya shaida wa TRT Afrika cewa abin da ya fara ba shi sha’ar zuwa Turkiyya shi ne ‘’ingancin ilimi’’ wanda ya ce ‘’ya fi na Nijeriya sau 100’’ musaman idan aka yi la’akari da kayan karatu.

Tukur na daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin tallafin karatu na gwmanatin Turkiyya da ake kira Turkiye Burslari Scholarship.

Ya yi nasarar kammala digirinsa na farko da na biyu, yanzu kuma yana digirin-digirgir a fannin nazarin alkaluma da kimiyyar kwamfuta.

Yana fatan idan ya kammala digirin-digirgir din ya koma gida domin ‘’na ilmantar da 'yan baya’’.

Ya bayyana Turkiyya a matsayin ‘’gidana na biyu’’ saboda yadda bai gamu da wata matsala ta bambancin al’ada ba tun zuwansa kasar a 2013.

Da tsohuwar zuma ake magani’

Wata alama karara ta huldar kasuwanci da tattalin arzikin ita ce ta karuwar zirga-zirgar kamfanin sufurin jirgin sama na Turkish Airlines a kasashen Afirka/Photo AA

Ilimi dai daya ne tak daga cikin hanyoyi da dama da Turkiyya ke amfani da su wajen kyautata hulda da Afirka.

Kasar tana kara tasirinta ta fuskar fasaha da al’adu inda fina-finan kasar ke kara samun karbuwa – fina-finan kuma da ake fassarawa a harsunan Afirka ciki har da Hausa da kuma Ingilishi.

A cewar mai fashin baki, Idayat Hassan yunkurowar kasashe irin su Turkiyya da China a Afirka ta kasance ‘’ta kawo ci gaba’’ da ‘’sakin mara’’.

Ta kara da cewa hakan ya bai wa Afirka ‘’wani kyakkyawan fata na daban da kuma kusanci.’’

Mrs Idayat na da ra’ayin cewa ‘’Turkiyya na tasowa a matsayin wani zabi’’ ga kasashen Afirka ko da sun samu matsala da kasashen yamma.

Misali, a cewarta, lokacin da Amurka da wasu kasashen yamma suka ki sayar wa wasu kasashen Afirka makamai, sai kaasashen ‘’suka zaga, suka kauce wa takunkumin, suka saya daga Turkiyya.

"Wannan ya taimaka wa kasar ta Turkiyya kuma ya taimaka wa kasashen a kokarinsu na magance matsalar tsaro."

Mrs Idayat ta ce ko da yake a shekarun baya-bayan nan, tasirin Turkiyya na karuwa a Afirka, to amma huldar bangarorin biyu ba yanzu aka fara ta ba, domin tun zamanin Daular Usmaniyya ana yinta – wato daruruwan shekaru da suka gabata.

A cewarta, ‘’abin da Turkiyya ke yi a yanzu, tana ‘’kara yaukaka dangantakar ne domin ta kara fitowa fili.’’

"Harkokin cinikayya tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka sun karu daga kimanin naira biliyan biyar a 2003 zuwa naira biliyan fiye da 34 a 2021.”

Alkaluma daga Ma’aikatar Harkokin Waje ta Turkiyya

A wani bangare na yaukaka dangantar ne kamar yadda Mrs idayat ta bayyana, Turkiyya ta kara adadin ofisoshinta na jakadanci a kasashen Afirka daga 12 zuwa 44 cikin shekaru 20 suka gabata.

Sannan karin kasashen Afirka akalla 28 sun bude ofisoshinsu na jakadanci cikin shekaru goma da doriya – duka da nufin inganta huldar difilomasiyya.

‘Fahimtar matsalar Afirka da burinta’

Duk da karuwar huldar siyasa, ‘’Turkiyya ba ta shisshigi a lamuran cikin gida na kasashen Afirka, sabanin kasashen yamma wanda ke son su rika bayar da umarnin a yi ko ka da a yi’’ in ji Ambasada Sulaiman Dahiru.

Ya kara da cewa kasashen yamma – irin su Faransa da Birtaniya ne - suka yi wa galibin kasashen Afirka mulkin mallaka.

To amma shekara da shekaru ‘’ba su nuna gaskiya a huldarsu da Afirka’’ kuma ba su ‘’taimaka wa Afirka yadda ya kamata duk da cewa suna kwasar albarkatun kasa na nahiyar.’’

A yanzu Turkiyya kan shirya taron kasuwanci tsakaninta da kasashen Afirka/Photo AA

Ambasada Sulaiman Dahiru ya bayyana cewa ‘’burin Afirka shi ne samun ci gaba da kuma girmamawa. Turkiyya ba ta raina Afirka.’’

Kwararren tsohon jami’in difilomasiyyar ya ce: "Duk da cewa an kawo karshen cinikin bayi, har yanzu suna daukar Afirka tamkar yankin da ake yi wa mulkin mallaka."

Ya jaddada cewa karuwar tasirin kasashe kamar Turkiyya da China ‘’na kawo sauyi a fasalin iko tsakanin kasashe’’

Ita ma daraktar cibiyar Centre for Democracy and Development, Idayat Hassan na da irin wannan ra’ayi tana mai cewa tsarin Turkiyya ‘’ya dace da halin da ake ciki a Afirka’’ kuma kasar na yin la’akari da ‘’ainihin bukatun Afirka.’’

Mrs Idayat ta ce ko da yake su ma kasashen yamma sun fara farga da gane kuskurensu kan yadda su ke hulda da Afirka, to amma kasashe irin su Turkiyya ‘’ga alama suna samun galaba.’’

Sai dai ta bayar da shawarar cewa duk da cewa Turkiyya ba ta shisshigi a harkokin siyasa, kamata ya yi ta rika karfafa shugabanci na gari a Afirka a kokarinta na kawo ci gaba.

"Turkiyya na tasowa a matsayin wani zabi’ ga kasashen Afirka ko da sun samu matsala da kasashen yamma."

Mrs Idayat Hassan, Daraktar Cibiyar Kyautata Dimokradiyya da Raya Kasa, Centre for Democracy and Development

Mai sharhin ta ce: "Muddin Turkiyya ta ci gaba da taka kyakkyawar rawa, mutane suna samun ingantaccen kaya da rahusa, da kiwon lafiya da kuma karfafa kyakkyawar dabi’a, to za ta iya samun kowane irin ci gaba.’’

TRT Afrika