Daga Coletta Wanjohi
Babban Taron Kayan Tarihi na Duniya na UNESCO ya bayyana wajen a matsayin "Waurin da ake kulla sadarwa da duniyar ruhaniyya."
Sophie Nanteza, mazauniyar Kampala babban birnin Uganda ce, ta bayyana wajen a matsayin wurin da dukkan iyaye ya kamata su koya wa yaron su girmama su tare da adana wajen.
Wajen na da girman kusan hekta 30 na tsaunuka a Kampala, hubbaren Kasubi kayan tarihin Masarautar Buganda ne da aka bayyana a matsayin daya daga cikin manyan masarautun Afirka.
Sarkin wancan lokacin Kabaka Muteesa ne ya kirkiri wajen, a 1882, inda ya koma makabartar sarakuna a 1884.
Jama'ar Baganda sun dauki hubbaran Kasubi a matsayin wurare na addini masu muhimmanci, Baganda wata al'umma ce ta Uganda da ke zaune a tsakiyar kasar.
A 2001, UNESCO ta bayyana Kasubi a matsayin Wurin Tarihi na Duniya, tana yabon wajen a matsayin "Bigiren kirkire-kirkire na dn adam", wanda ke bayyana irin al'adu da zamantakewar jama'ar Baganda.
Hubbaren da ke samun maziyarta 30,000 a kowacce shekara, an samar da su turakun katako da filayen ciyayi da tsarin gini mai kyau da aka yi a karni na 13.
Rose Mugerwa, mace mai shekara 50, na daga cikin wadanda suke kallon hubbaren Kasubi ba wai kawai wurare na tarihi ba, wurare ne da suke da kyawu da tsarin gini.
Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Muna girmama wannan waje sosai, wanda waje ne mai zaman lafiya." Iyalan Dan Musoke na ziya wajen din yin aikin hajji.
"Har zuwa lokacin da mahaifina ya rasu, iyayena na zuwa wannan waje daga Masaka (waje mai nisan kilomita 130 daga Kampala) a kowacce shekara don ziyara. Mun amince da waje ne mai albarka," in ji shi.
Mummunar gobara
A ranar 16 ga Maris din 2010, wata gobara ta kama a Masarautar Buganda inda wani bangare na hubbaran masarautar Buganda masu tsarki ya kone, wanda ake kira Abalongo.
An san me ya janyo wannan gobara. Nan da nan UNESCO ta saka Kasubi a jerin sunayen kayan ta na tarihi saboda gobarar "ta yi barazana ga Wajen Tarihi na Duniya", wanda yake bukatar a gyara shi tare da ba shi kariya.
Farfado da wajen na nufin dawo da matsayin hubbaran kamar yadda suke kafin gobarar, gyaran da ya hada da turaku 52 da ke wakiltar kabilun Masarautar Buganda.
Wadannan turakun suna daukar jinka, wanda ake yi a gargajiyance a salon Buganda ta amfani da salon yin rufi na "ganda".
Masarautar Buganda da gwamnatin Uganda suna aiki tare don saka ido kan dabarun maido da kayan tarihin.
Japan, da Uganda, da Norway da kuma UNESCO sun ba da gudunmawa ta hayar cibiyoyinsu na adana tarihi, kamar yadda Charles Peter Mayiga, Firaministan Buganda ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar wa Kwamitin Duniya na Kayan Tarihi.
Sama da shekaru 13 bayan nan, Kwamitin Duniya na Kayan Tarihi ya amince cewa an samu babban cigaba wajen maido da tarihin, wanda ya haifar da cire hubbaren Kasubi daga jerin wuraren tarihi da ke cikin "hadari".
Dawo da daraja
Mayiga ya bayyana cewa, "Aikin dawo da tarihin ya dauki lokaci saboda masarautar Buganda ta dauki matakin tabbatar da an kiyaye muhimman al'adu da rauhaniyya".
"Bugu da kari, aikin yana bukatar kudi mai yawa da tarin ma'aikata." Masarautar Buganda ta ce tana da burin ganin an kare wurin sama da yadda aka yi a baya.
Mayiga ya kara da cewa, "Za mu kula da hubbaren don ganin an kare matsayinsa a al'ada da rauhaniyya".
Za a bude hubbaren don ziyarar jama'a a watan Disamban 2023. Musoke ya ce, "Mun sha jira tsawon lokaci don ganin mun koma shiga wannan waje mai tsarki".
"Mahaifina ya rasu ana tsaka da aikin sake ginin hubbaren, amma a yanzu dai mahaifiyata tana raye kuma za ta koma aikinta na ziyarar hubbaren duk shekara."