Daga Eudes Ssekyondwa, TRT Afrika, Kampala
Wani dan asalin Congo, Livingstone Matata ya zo yammacin Uganda a watan Yulin bana don fara sabuwar rayuwa a sansanin masu neman mafaka na Nakivale, wajen da yake da tantuna farare da ke a nisan kilomita 200 daga babban birnin Kampala.
A watannin ukun da ya dauka a wannan waje, yanayi mara kyau ne babbar jarrabawar da ya fuskanta wajen gwagwarmayar rayuwa.
Matata ya shaida wa TRT Afirka cewa "Mun zo wannan waje kusan a lokacin damuna, amma kuma babu ruwa saman a wannan lokaci. Mazauna yankin suna cewa sare bishiyoyi na daga dalilan da suka janyo rashin samun ruwan saman. Kayan amfanin gonata na yamushewa."
Bwiza Mutonore, da ke rainon yaro kuma ba ta da miji, na gwagwarmaya don neman itacen girki. A kowacce rana, ganyaye da rassan da aka sare na sake tohowa.
"Babu bishiyoyi a wannan waje. Sai na yi doguwar tafiyar mil da yawa don samun itace, wasu lokutan ma ka fuskanci hatsarin kora daga masu gonaki.. idan ba ka samu itace ba, to akwai yiwuwar ka kwana da yunwa."
Wani ta'ajibi kuma, wannan dogaro kacokan kan itace don yin girki na daya daga cikin dalilai da suka sanya Nakivale ke fiskantar barazanar sauyin yanayi.
'Yan gudun hijira mafi yawa
Afirka ce ke dauke da sama da kaso 30 'yan gudun hijirar duniya, inda Uganda kaɗai ke da da adadin da ya haura jama'ar wasu kasashen nahiyar.
Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumban 2023 sun bayyana cewa kasar ta Gabashin Afirka na dauke da 'yan gudun hijira miliyan 1,520,966 da masu neman mafakar siyasa 47,271.
'Yan kasar Sudan ta Kudu ne a kan gaba, kuma 'yan Jumhuriyar Dimukuradiyyar Kongo da ke biye musu baya.
"Sannan sai wasu 'yan Somalia, Burundi, Eritra, rwanda, Ethiopia da Sudan ma na gudun hijira zuwa Uganda a kowacce shekara.
Amma kuma a yayin da Uganda ta ke samun yabo saboda rungumar 'yan gudun hijira, abubuwan da ke afkuwa a yankin Nakivale mai girman sukwaya kilomita 184 na bayyana yadda kalubale ke karuwa wajen kula da su da biyan bukatunsu na yau da kullum.
Sauyin yanayi da sare bishiyu ya janyo, ya kara ta'azzara matsalolin 'yan gudun hijirar.
Shirin Samar da Abinci na MDD (WFP) ya rage adadin kunshin abincin da yake bayarwa da kaso 70 zuwa 60 a watan Afrilu 2020, inda ya kara raguwa a watan Fabrairun 2021.
Wani ma'aunin samun kayayyaki mara dadi shi ne WFP za su iya kashewa kowanne mutum guda cent 0.35 ne kawai a kowacce rana a 2022, amma kuma ana bukatar cent 0.68 don biyan bukatunsu a karkashin shirin.
Wannan na nufin akwai babban gibin cimaka, inda kayan da ake da su za su biya kaso 52 ne kawai na bukatar abinci mai gina jiki da ake da ita a kowacce rana.
"Dadin dadawa ga taimakon da muke ba su, dukkan 'yan gudun hijirar da ke Nakivale na dogaro ne kan gonaki don rayuwa," in ji Santo Asiimwe, shugaban shirin WFP da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nakiwale yayin tattaunawa da TRT Afirka.
"Yanayin da ake ciki ba shi da kyau inda a yanzu muka fita daga watan Oktoba, kuma ga shi babu alamun ruwan sama."
Manufofin cigaba
Uganda na baiwa 'yan gudun hijira damar aiki da 'yancin zuwa duk inda suke so karkashin wani tsari masi suna "tsarin dogaro da kai", wanda aka dinga yabon sa kan cewa na daya daga cikin tsare-tsaren kula da 'yan gudun hijira mafi kyau a duniya.
Ta wannan hanya ne 'yan gudun hijira irin su Matata da Bwiza suke gwagwarmaya don cike gurbin matsalolin taimamon jin kai da ake ba su wanda ba ya isa.
"Samun wata 'yar gona na da muhimmanci gare mu; ko kuma mu mutu da yunwa," in ji Matata.
"Matsalar ita ce yadda wadanda suka zo kafin mu suka sare bishiyu da dama, don samun itace ko samun gonar yin shuka. Illar hakan ne ka addabar mu a yanzu."
Mafi yawan 'yan gudun hijira sun fahimci irin illar da ke tattare da sare bishiyu da korran ganyaye.
"Yarana na fada min cewa wannan itacen da muke amfani da shi ne ke janyo matsalar sauyin yanayi - cewa kuma yana bayar da gudunmowa ga rashin smaun ruwan sama.
"Amma idan babu itace da me za mu yi girki?" tambayar da Bwiza ta yi kenan. "Mu 'yan gudun hijira ne, ba mu da hanyoyin samun kudade da yawa."
Dasa bishiyoyi
Enoch Twagirayesu, dan gudun hijira daga Burundi na tattara sauran abokan zaman sa a Nakivale don gwada sake assasa koren yanki.
Ya zuwa yanzu kungiyar ta shuka bishiyoyi 350,000 don magance matsalolin sauyin yanayi a yankin.
Twagirayesu ya shaida wa TRT Afirka cewa "Burina shi ne na sake mayar da sansanin 'yan gudun hijira na Nakivale ya koma kore shar. Muna wayar da kan 'yan gudun hijira da jama'ar yankin da su shuka bishiyu a tsakiyar gonakinsu na ayaba."
Akwai kalubale sosai ga aikin ganin an tafi tare da kowa, kamar yadda Twagirayesu ya gano.
Ba kowa ne ke fahimtar muhimmancin shuka bishiyoyi ba, yayin da wasu kuma ma ba su damu ba saboda sun yanke shawarar ba za su dauki lokaci mai tsawo suna zaune a sansanin ba.
Ya ce "Yana da wahala a iya zaburar da mutane, musamman matasa, don su dabi'antu da dasa bishiyoyi."
Babban Kwamishinan Kula da 'Yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya dauki nauyin wani shiri ta hanyar wata Kungiyar Cigaban Al'umma mai suna Nsamizi domin ta yi aikin yaki da sauyin yanayi a yankin ta hanyar shuga bishiyu da yawa.
A tsakanin watan Mayu 2022 da 2026, shirin na da manufar dawo da bishiyu da tsirrai da ke wajen don jin dadin rayuwar 'yan gudun hijirar. A yanzu ana biyan 'yan gudun hijirar don gudanar da wannan aikin.
"Muna shuka bishiyu duba da adadin da muke so a shekara. A 2023, muna da manufar shuka bishiyu a hekta 80 a Nakivale kadai, da kuma a wata hekta 10 da ke yankin Uruchinga," in ji Rachael Akamumpa, jami;in kula da makamashi a Cibiyar Cigaban Al'umma ta Nsmaizi.
Hukumar ta MDD da abokan huldar ta na fatan nan da shekaru biyar, ba za su kawar da matsalar sauyin yanayi ne kawia ba, za kuma su bayar da gudunmowa wajen rage iskar carbon a Uganda.