Masu fafutuka na kokarin wayar wa da mutane kai a kan sauyin yanayi a Afirka. Hoto: TRT Afrika

Daga Coletta Wanjohi

Sidi Otieno, manomi ne a yankin Migori a Kudu maso Yammacin Kenya, sai dai bai fahimci mummunan tasirin da ke gab da fada wa duniya ba saboda matsalar sauyin yanayi.

Kuma bai fahimci matsalar da ke tattare da abin da ake kira "El Nino effect" da "Carbon footprint" da kuma "Thermal Expansion".

Abin da Otieno da wasu miliyoyi mutane kamarsa suke gani shi ne tasirin sauyin yanayi wanda ba sa iya kauce masa a rayuwarsu.

"Idan aka yi ruwan sama a 'yan kwanakin nan, ana yin ruwan da yawa ne, wanda yake lalata amfanin gona. Haka zalika idan ruwan ya tsaya, rana tana yin zafi sosai. Komai yana zuwa da tsanani," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"A duk lokacin da na yi tunanin sauyin yanayi, wadanda suke fara zuwa raina su ne manoma wadanda ke shiga mawuyacin hali."

Ba a iya hasashen yadda damina za ta kasance wanda hakan yake nufin manoma ba za su iya yin shirin tunkarar damina ba, wanda hakan yake shafar yawan amfanin da za a samu da kuma riba.

"Har sai 'yan shekarun nan da suka wuce, mun san cewa ana fara ruwan sama ne a watan hudu na shekara. Muna gyara gonarmu don fara yin shuka, amma yanzu sai ka ga daminar ta zo a makare bayan wasu makonni," kamar yadda Otieno ya yi bayani.

"Idan abin ya yi muni sosai za a iya kin samun ruwa kwata-kwata a lokacin da ake bukatarsa, wanda yake shafar shuka kamar ta masara wacce take kwashe tsawon lokaci daga shuka zuwa girbi."

Aiki da abin da aka fada

Batun sauyin yanayi ya kasance abin da aka fi tattaunawa a kai a duniya, inda hatta Taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya sanya shi cikin manyan batutuwan da zai mayar da hankali a 2023.

Kalubalen shi ne yadda yawancin tattaunawar an takaita ta ne tsakanin shugabanni da manyan hukumomi da kuma kungiyoyi. Hoto: TRT Afrika

Haka zalika shugabannin Afirka sun yi taro kan sauyin yanayi a birnin Nairobi a kasar Kenya daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba, wanda shi ne na farko da Afirka ta shirya.

Sakon a fili yake: Afirka tana neman hanyoyin da za ta magance matsalolin sauyin yanayi wadanda suke barazana ga rayuwar mutanen nahiyar.

Kalubalen shi ne yadda yawancin tattaunawar an takaita ta ne tsakanin shugabanni da manyan hukumomi da kuma kungiyoyi.

Franklin Okinya Obonyo, shi ma wani manomi dan Kenya wanda tasirin sauyin yanayi ya shafi rayuwarsa, inda ya ce ba ya tunanin ra'ayinsa zai yi amfani.

"A wajena, sauyin yanayi yana da alaka da yadda muka daina amfani da irin da muka gada iyaye da kakanni," in ji shi. "Wannan ya sa muke samar da iri kawai daga shukar da muka girbe."

Tsarin aikin gona na iyaye da kakanni ya bai wa manomi damar sake shuka iri fiye da sau daya. Misali, bayan girbe masara, sai manomi ya ware wani abu daga abin da ya girbe saboda sake shukawa. A daya bangaren, irin da aka samar ta hanyar kimiyya ana amfani da shi ne sau daya tal.

Wata doka kan iri da shuka a Kenya ta haramta rabawa ko musaya ko kuma sayar da iri da ba a tantance ko yi masa rijista ba.

Wannan ya kashe al'adar manoma ta raba iri a tsakaninsu daga girbi saboda dorewar amfani mai kyau a yankin.

"Ba za mu iya samun isasshen abinci ba, idan muka yi amfani da irin da aka tantance shi. Wannan irin yana da rauni idan ya ci karo da sauyi a yanayi."

"Bugu da kari suna ba mu abin gidan gona ne, wanda ba ma so," kamar yadda Obonyo ya shaida wa TRT Afrika.

Ya wuce batun aikin gona

Ana kiran Irene Mwikali da sunan "Mama Yao" — kalmar tana nufin "mace mai kamar maza" a harshen Kiswahili — mambobin tawagar da take jagoranta ne suka sa mata sunan.

Bisa la'akari da aiki mai wahala da take yi, suna ne da ke jinjina mata da kuma wayar da kai kan sauyin yanayi a tsakanin mata a unguwar Mathare a birnin Nairobi.

Kwanan nan tasirin sauyin yanayi ya jawo mummunar ambaliyar ruwa a Libiya. Hoto: Reuters

"Duk lokacin da na ji batun sauyin yanayi, ina alakanta hakan da hakkin dan Adam. Babu adalci kan yanayi idan ba a yi adalci ta fuskar kare hakkin dan Adam ba, musamman ga mu mata," in ji Mwikali.

Ta shaida wa TRT Afrika cewa mata ne sauyin yanayi ya fi shafa ba kai-tsaye ba.

"Mutum yana koma wa gida babu isasshen abinci, ko ma babu abinci saboda kudin abinci ya yi sama sanadin manoma suna samar da abinci kadan ne saboda sauyin yanayi. Idan mace ta tambaya ko ta yi korafi sai a doke ta ko kuma ta fara fadi tashin nemarwa yaranta madafa," in ji Mwikali.

"Idan na ji ana maganar sauyin yanayi, na kan yi tunanin me ya sa ba mu da isasshen abincin da za mu ci a yanzu. A yankunanmu mutane ba sa iya cin abinci akai-akai saboda ya yi tsada.

Muryar matasa

Lokacin da Kenya ta karbi bakuncin Babban Taron Afirka kan Sauyi Yanayi, Dereva Mutua da sauran masu zayyane-zayyane sun bayyana al'umma allunansu. Sun samar da buroshi da fenti ga mutane don su rubuta sakonninsu kan sauyin yanayi.

"Duk lokacin da na tuna da sauyin yanayi, na kan tuna da yadda ake mayar da wurare birane da kuma yadda shugabanninmu ba sa ganin tasirin haka a kan muhalli," in ji shi. "Duka ci gaba da kafa masana'antu a kewaye da mu zai iya kasancewa abu ne mai kyau ga tattalin arziki, amma kuma suna gurbata muhallinmu. Ana sare bishiyoyi don a yi gine-gine."

Wani takwaransa mai zayyane-zayyane Fredrick Odhiambo ya ce a ganinsa abin mayar da hankali kan tattaunawa kan sauyin yanayi a kan ci gaba da kasashe daban-daban suke nema, ba tare da koya wa jama'a yadda ba za mu gurbata muhalli ba.

Mafita daga jama'a

Babban taron shugabannin Afirka kan sauyin yanayi a Nairobi ya samar da mafita da dama wajen yaki da sauyin yanayi. Gabalin abin da aka cimma za su fito ne daga Babban Taron Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.

"Duk lokacin da shugabanni suka yi babban taro, ya kamata su yi la'akari jama'a marasa karfi kamar mu don muma mu bayar da gudunmuwa a zahiri kan yadda sauyin yanayi yake shafar mu," in ji Otieno.

Hukumomi na ta kokarin ganin an shawo kan sauyin yanayi a duniya. Hoto: Climate-change/Africa

"Yawancin abubuwan da aka cimma ana yin haka ne ba tare da jin ra'ayinmu ba. Ba ma jin su suna ambatowa a fili yadda za su taimaka wajen ganin abin da Afirka take nema na taimako daga kasashen da suka ci gaba wajen zai taimaki al'ummomin da ke kokarin shuka bishiyoyi da kare muhalli."

Mwikali ta yi amannar cewa ya kamata a ba mata muhimmanci a tafiyar. "Ta yaya shugabannin za su cimma matsaya da za ta taimaka wa mata a unguwanni marasa tsari da matsalar sauyin yanayi ta shafe su, idan ba su tuntube mu muka fada musu yadda abin yake ba?" in ji ta.

Mai zayyane-zayyane Mutua bai amince da kiraye-kirayen shigo da karin mutane yayin tattaunawar fitar da tsare-tsaren yaki da sauyin yanayi.

"Yawancin matasa ba su fahimci abin da ake nufi da sauyin yanayi ba — suna ganin batu ne kawai da ya shafi mutane masu ilimi mai zurfi kadai," in ji shi. "Dole ne gwamnatinmu ta kara wayar da kan jama'a saboda yayin da aka yi gaba, yaki ne na kowa da kowa."

TRT Afrika