A kasa da watanni uku kafin COP27, Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya Kan Sauyin Yanayi da za a gudanar a Masar a watan Nuwamba, kasashen sun yi kira da a kawo karshen “rashin adalcin yanayi”.
Rahoton Hukumar Tsare-Tsare kan Sauyin Yanayi (CPI), Afirka dake fitar da kaso 4 na iskar carbon, duk da ita ce ta biyar mafi yawan jama’a a duniya, nan yanki mafi illatuwa daga rikicin dumamar yanayi.
Ministan Harkokin Wajen Masar kuma Shugaban COP27, Sameh Chokry a wajen Taron Makon Sauyin Yanayi na Afirka da aka gudanar a Libreville, Gabon, a wani bangare a shirye-shiryen COP27, ya shaida cewa “Wannan tsagwaron rashin adalci ne yadda Afirka dake fitar da kaso 4 na iskar carbon a ban kasa, amma kuma mutanenta sun fi kowa illatuwa daga illar sauyin yanayi.”
A dukkan tarukan sauyin yanayi da jami’anta suka halarta, Afirka ba ta taba daina tambayar wadanda suka fi gurbata muhalli-- wato kasashen dake da masana’antu--- kan su bayar da gudunmowa don bayar da kariya ga raywa a Afirka ta hanyar bayar da kudade. Amma nahiyar dake bukatar dala biliyan 250 a shekara don magance matsalar sauyin yanayi, a shekarar 2020 dala biliyan 29 kawai aka ba ta taimako.
Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo na jiran a aiko mata da dala biliyan 10 bayan gama COP26, amma kawai an yi mataalkawarin dala miliyan 500 a cikin shekaru biyar.
Bankin Cigaban Afirka ya bayyana cewa, sauyin yanayi ya illata kayayyakin da Afirka ke samarwa. “Nahiyar na kallon zaftarewar kayan da take samarwa da kaso 5 zuwa 15b cikin dari saboda sauyin yanayi. A tsakanin 2016 da 2019, kasashen Afirka gaba daya sun karbi dala biliyan 18.3 don magance matsalar sauyin yanayi, wanda nan da tsakanin 2020 da 2030 adadin zai kai dala biliyan 127”, kamar yadda rahoton AfDB mai takwn ‘Duba ga tattalin arzikin Afirka ya bayyana’.
Mummunan sakamakon zai afku
Tsakanin tsananin zafi, tsawa, fari da ambaliyar ruwa, sakamakon dumamar yanayi a Afirka zai munana inda za a samu karin dajarar zafi 1.5 ma’aunin selshiyos--- An yi hasashen me zai faru idan aka samu wannan sauyi.
Sakamakon haka, amfanin gona kamar su zaitin a Arewacin Afirka ko Kahwa a Gabashin Afirka za su ragu sosai.
Sannan za a samu karuwar cututtuka kamar su zazzabin cizon sauro a Yammacin Afirka da Tsakiyar Afirka, sai kuma zazzabin dengue a Kudanci da Gabashin Afirka.
Game da kamun kifi kuma, akwai hatsarin a samu raguwar sa da kaso 50 a Afirka ta Yamma.
Tare da samun karuwar digri 2 a ma’aunin selshiyos a Arewacin Afirka, kaso 20 na dabbobi ba za su amfana da yanayin tsirarsu ba, inda a Yammacin Afirka kuma za a samu raguwar samun amfanin gona da kaso 42 nan da shekarar 2050, kaso 90 na tsirran dke karkashin teku a Madagascar za su kare, sannan kuma tuddan dusar kankara na Rwenzoris da Kilimanjaro za su narke.
An gano samun darajar zafi sama da digiri 30 a ma’aunin selshiyos a Afirka ta Kudu ya kara yawan rikici da kashe mutane da ake yi da kaso 18.
A ma’aunin nahiya, kaso 50 na halittu za su rasa rayukansu da kaso 30, a kalla garuruwa 25 za su fuskanci darajar zafi sama da digiri 40.6 a ma’aunin selshiyos na tsawon kwanaki 150 a shekara, adadin masu cututtukan zazzabin dengue, shawara da zika zai ninka, kuma a karshe ‘yan Afirka miliyan 17 zuwa 40 za su yi kaura daga wani yanki zuwa wani a cikin nahiyar.
Wata babbar dama
Duk da ana kallon Afirka a matsayin nahiyar dake fuskantar matsalolin sauyin yanayi na tsawon lokaci, tana da damarmaki da dama z-da za ta yi amfani da su wajen rage tasirin dumamar yanayi. Wasu ma na tunanin nahiyar ce za ta zama wajen samun hanyar magance wannan matsala ta gurbacewar muhalli a duniya.
Daga cikin damarmakin da ake da su, shi ne makamashi mai sabuntuwa: Amfani da makamashin hasken rana da na iska a nahiyar zai sauya labarin, ba ga nahiyarkadai ba, har ma ga sauran sassan duniya.
Nahiyar na kuma danganawa ga wanzar da amfanin gona, kamar noma dazuka wanda manufarsa ita ce a raya kasar noma ta yadda za ta dinga anfanarwa. Fasahar nan ta ‘biochar’, wadda take amfani da gawayi wajen rayar da kasar noma, misali ce inda a Kamaru ta farfado da kasar da ta mace a dazuka.
Shirin ‘Great Green Wall’ da Tarayyar Afirka ta kaddamar a 2007, shiri ne dake da manufar shuka miliyoyin bishiyu ---, kuma na da nufin a sakesamar da dazuka a Afirka, a hana kwararowar hamada da sahara, inda a lokaci guda ake inganta yanayin rayuwa da kula da lafiyar al’uma, ana kuma yaki da karancin abinci da talauci.
Nahiyar za ta kuma iya amfani da damar yawan jama’a da take da su da biranenta don gina manyan birane na fada a gani, sauya fasalin gine-gine zuwa masu amfani da makamashi mai sabuntuwa da samun iska mai inganci.
Gabon, mafi kyawun muhalli a duniya
Libreville, Babban Birnin Gabon, ya karbi bakuncin taron Makon Afirka Kan Sauyin Yanayi--- mataki na uku na tarukan da Hukumar Yakida Sauyin Yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya take dauka, an gudanar da taron a tsakanin 29 ga Agusta zuwa 2 ga Satumba, sama da mahalarta 1,000, da suka hada da ‘yan siyasa, wakilan kungiyoyin kasa da kasa da kungiyoyin farar hula, sun tattauna kan matakan da aka dauka a wajen taron COP26.
Shugaban Kasar Gabon Ali Bongo Ondimba ya fadi cewa manufar ita ce a samu murya daya daga Afirka a wajen taron COP27 tare da bayar da ingantattun shawarwari.
Shugaban na Gabon ya ce “Lokaci ya yi da mu ‘yan Afirka za mu dinga yanke hukunci da kanmu”, inda ya kuma zayyana yadda kasashen duniya suka gaza aiwatar da manufofin COP21 da aka yi a 2015, inda ake da manufar nan da shekarar 2100, dumamar yanayi a duniya zai zama kasa da digiri 2 a ma’aunin selshiyos, wanda ya haura na masana’antu da aka bayyana a matsayin 1.5.
Ba arashi ba ne yadda aka zabi Gabon a matsayin wajen gudanar da taron Makon Sauyin Yanayi: Kasashen duniya na yabon kasar saboda “zama zakaran gwajin dafi” wajen aiyukan kyautatuwar yanayi da yaki da dumamar yanayi. Kasa dake da mutane kasa da miliyan 10, na nan a tsakiyar Afirka kuma a cikin dazukan zafi. Ana mata lakabi da huhu na biyu na duniya bayan Amazon.
A watan Yuni 2021, Gabon ta zama kasar Afirka ta farko da aka baiwa kudade saboda gagarumar gudunmowar da take bayarwa wajen yaki da gurbacewar yanayi da zuke iskar carbon, inda ta iya adana dazukanta da kaso 90 na iyakokinta.