17 ga watan Satumba na nufin wani ƙarshen makon ga Joy Ukadike a yayin da ita da ƴar uwarta suka fita daga gidansu da ke unguwar Ojo ta Jihar Legas a kudu maso yammacin Nijeriya zuwa coci.
A daren wannan ranar an yi ruwa kamar da bakin ƙwarya, amma ba ta san akwai wani bala’i da ke jiranta a ƙofar gidanta ba.
Joy ta gigice da ganin yanayin da illahirin hanya da gidaje da shagunan da idanunta ke iya hangowa a kewayen ke ciki.
Mutanen unguwar suna ta fita da shiga cikin gidajensu a cikin ruwan da ke ya yi ambaliya ya kai musu ha rƙugu, wanda da alama ruwan da aka yi cikin dare ne ya jawo ambliayr ruwa.
Wasu gidajen – ciki har da na Joy – sun tsira daga bala’in ambaliyar saboda layin gidansu a kan tudu yake ba gangare ba kamar inda sauran gidajen suke.
A wannan makon sai da maudu’in #lagosfloods ya yi tashe a shafukan sada zumunta, inda waɗanda ambaliyar ta shafa suka dinga wallafa bidiyoyi masu ban tsoro, daga ciki har da wanda aka ga fasinjoji daga cikin wata motar bas da ruwa ya kusa shafe ta a kan titin da take tafiya suke ta leko da kawunansu ta cikin taga suna ihun neman taimako.
Hankalin Joy ya kwanta ganin cewa lamarin bai shafi gidanta ba, amma ta yi ta mamakin dalilin da ya sa duk shekara sai an yi ambaliya.
“Me ya sa mu mutane da gwamnati ba za mu koyi darasi daga abubuwan da suka sha faruwa ba, da kuma ɗaukar matakai don kauce musu?” ta faɗa cikin mamaki.
Wadannan su ne tambayoyin da ake bijiro da su a yankunan Afirka da dama, inda ambaliyar ruwa a birane ta zama wani iftila’in da ke jawo ɓarna da sanya mutane cikin tashin hankali.
Mummunan bala’i
A watan Oktoba, wata zaftarewar ƙasa da mummunar ambaliya da aka yi a gundumar Mbankolo a yammacin Yaoundé da ke Kamaru sun jawo mace-mace da mummunar ɓarna.
Ɓallewar wasu madatsun ruwa biyu da mahaukaciyar guguwar da ta taso daga Tekun Bahar Rum sun jawo mummunar ambaliya a yankin arewa maso gabashin Libiya ranar 11 ga watan Satumba.
Lamarin ya jawo kwararar ruwa kubik biliyan ɗaya a yankunan da dama suke cikin matsala. Kashi ɗaya bisa huɗu na birnin Derna ya lalace gaba ɗaya. Kusan mutum 20,000 ne suka mutu a wannan bala’in.
A bara aka yi mamakon ruwan sama a N'Djamena, babban birni Chadi irin wanda ba a gani ba a shekara 30 din da suka wuce, inda sai komawa amfani da kwale-kwale aka yi, sannan dubban mutane sun rasa muhallansu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.
Kazalika mummunar ambaliya da zaftarewar ƙasa da aka yi a watan Afrilun 2022 a Afirka ta Kudu sakamakon mamakon ruwan sama na tsawon kwana uku sun tursasa ƙasar ayyana dokar ta ɓaci. Ɗaruruwan mutane dun mutu sannan dubban gidaje sun lalace.
A farkon shekarar nan, Bankin Raya Ƙasashen Afirka ya ranta wa Jamhuriyar Benin kusan dala 176 don inganta birane da gina abubuwan da za su jurewa ambaliya wacce sauyin yanayi ke janyowa.
Wani bincike na lafiyar al’umma na 2022 mai taken “Epidemiology of floods in sub-Saharan Africa: A systematic review of health outcomes", wato yawan afkuwar ambaliya a yankin kudu da Hamadar Saharar Afirka, ya ce ambaliya ta shafi mutum biliyan 2.3 a fadin duniya a shekara 20 ɗin da suka gabata, kuma duk sun jawo matsalolin lafiya daban-daban.
Matsalar a Nijeriya
A bara Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Nijeriya (NEMA) ta sanar da cewa mutum 600 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihohi da dama, inda gidaje 200,000 suka lalace, sannan ya yi mummunan tasiri a kan kusan mutum muliyan biyu.
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya rawaito cewa fiye da mutum miliyan 2.5 ne suke buƙatar agaji a Nijeriya, kuma kashi 60 cikin 100 daga cikinsu yara ne.
UNICEF ta ce yaran suna kuma barazanar kamuwa da cututtuka masu alaƙa da ruwa kamar nutsewa da tamowa, a sakamakon ambaliyar mafi muni da ta shafi kasar a cikin shekara 10.
Dr Selegha Abrakasa, wani ƙwararre kan kimiyyar muhalli a Jami’ar Port Harcourt da ke kudu maso kudancin Nijeriya, ya ce asarar rayukan da aake yi abin damuwa ne matuƙa saboda har yanzu mutane ba su fahimci kimiyyar da take jawo yawan ambaliyar da kuma yadda za a shiryawa irin waɗannan annoba.
Ƙalubalen shi ne a tabbatar da cewa akwai ingantaccen tsarin kariya da zai dinga ankarar da mutane yiwuwar samun ambaliya, sannan a yanayin da ba a shirya sosai ba kuma ya kasance an tsara yadda za a kwashe mutane daga yankunan da abin ya faru,” ya bayyana wa TRT Afrika.
A shekarar 2012, ambaliyar ruwa sun jawo tumbatsar tekuna har bakin gaɓa tare da shafe filaye da dama a jihohi 36 na ƙasar, sannan mutum kusan 400 sun mutu, wasu miliyan 1.3 kuma sun rasa muhallansu.
Bala’in ya kuma jawo barnar da aka yi ƙiyasin cewa ta kai dala biliyan 17, a cewar NEMA.
Shekara bakwai bayan nan, ambaliyar ta shafi mutum 277,555 da kuma hallaka 158.
Shekara guda bayan nan, yawan wadanda abin ya shafa ya zama 2,353,647, baya ga macemace 69.
Gine-gine ba bisa ƙa’ida ba
A ranar 18 ga watan Oktoban bara, hukumomi sun rushe fiye da gine-gine 20 da aka gina su a kan magudanan ruwa a unguwar Lekki da ke Jihar Legas, don kare afkuwar ambaliya.
Kwamishinan muhalli na jihar Tokunbo Wahab, ya shaida wa manema labarai cewa an fara aikin gina wuraren da aka rushe ɗin a shekarar 2020 bayan bayar da gargaɗi, yana mai nuni da cewa za su toshe magudanan ruwa. Amma sai mazauna wajen suka yi biris da gargadin da kuma sanarwar.
Peter Kolawale, wani injiniyan gine-gine a Lagos ya jaddada cewa bai kamata a zuba ido ba tare da bai wa wuraren da amlabiya za ta iya shafa muhimmanci ba.
“Wannan babban laifin ne kuma bai kamata gwamnati ta ƙyale ba,” ya shaida wa TRT Afrika.
Kolawale ya zargi injiniyoyi da kawar da kai kan irin waɗannan abubuwa ba tare da ƙoƙarin ganin sun yi ƙoƙarin hana yin gini a riin yankunan da ke kan magudanan ruwa ba.
“Ba sa lura cewa bai kamata kuɗi ya rufe musu ido ba, batu ne na ceto rayuka,” ya faɗa.
Duk da cewa ambaliyar da ta faru a baya-bayan nan ba ta shafi gidan Joy ba kai tsaye, amma har yanzu tana fama da tashin hankali da fargabar abin da ka je ya zo. “Ina shirin barin unguwar nan,” ta ce.
Kolawale ya ba da shawarar cewar ya kamata duk mai neman gida ya yi taka tsantsan. “Idan unguwar da kake zaune ta cikin hadarin afkuwar ambaliya, to a dinga lura da alamu,” ya ce.
“Ka fara bincikenka tun daga shigar damina don ka san me za ka fuskanta.”