Wata hula mai adon zinare na daga kayayyakin da za a arawa Ghana. Photo / British Museum

Daga Charles Mgbolu

A 1987, masarautar Asante ta fada karkashin harin dakarun Birtaniya. Ingila ta aika da mayaka karkashin Sir Garnet Wolseley don yakar Asantehene Kofi Karikari, Sarkin Jama'ar Asante.

Asante, kamar sauran sanannun labuilun Afirka a wancan lokacin, na fuskantar mamaya da munanan hare-haren Turawan mulkin mallaka a Ingila da ke mamaye iyakokin Afirka.

A ranar 26 ga Oktoban 1874 ne mayakan Birtaniya suka afka wa fadar Kofi Karikari wanda hakan ya janyo tsige shi daga kan mulki. An maye gurbinsa da dna uwansa, Mensah Bonsu, kamar yadda bayanan Gidan Adana Kayan Tarihi ma Birtaniya suka nuna.

Sojojin Birtaniya da suka kai harin sun kuma sace kayayyakin fadar, sun saci zinare da kayan tarihi tare da kai su Ingila, inda aka ajje su a gidajen adana kayan tarihi.

Gidan Adana Kayan Tarihi na Ingila da Gidan Adana Kayan Tarihi na Victoria da Albert manyan cibiyoyi ne da ke dauke da kayayyakin tarihi da a'ladu na fadar Asante da sauran kasashen Afirka da dama.

Dukkan wadannan gidajen adana kayan tarihi sun sanar a wata sanarwar hadin gwiwa a ranar Laraba cewa an dauki kayayyaki 32 daga fadar sarkin Asante kum za a bayar da su aro ga Ghana na tsawon shekaru uku.

Adana Kayan Tarihin sun ce "Kayayyaki masu adon zinare da azurfa da ke da alaka da fadar Asante ne za a baje-kolin su a Gidan Adana Kayan Tarhi na Kumasi a karshen shekara, a wani bangare na bayar da aro na tsawon lokaci da Gidajen Adana Kayan Tarihi na Victoria and Albert da na Birtaniya za su yi."

Kayan tarihi masu kyau

A Gidan Adana Kayan Tarihi na Victoria and Albert, akwai wasu kayayyaki masu adon zinare da aka bai wa taken "Zinaren Asante" da za a nuna su ga maziyarta.

Wani abu guda da yake jan hankalin mutane shi ne wani dunkulen zinare mai siffar hauren giwa da yake ƙyalli da sheƙi, wanda aka samar shekaru sama da 150 da suka gabata.

Kahon yaki mai siffar hauren giwa da ake da adon zinare. Hoto / V&A Museum

Sai dai kuma, a Ghana da wasu kasashen Afirka an yi suka sosai game da wannan labari na bayar da aro da aka samu, inda wasu ke kallon hakan a matsayin wani cin fuska, a ce kayan tarohon da aka sace ta karfi daga Ghana amma a ce Birtaniya na bayar da aron su ga kasar.

"Ina tunanin wannan dabarar 'yan mulkin mallaka da daniiya ne. Su nuna suna da cikakken karfin iko, za su iya kai hari, su lalata tare da sace kayan mutane masu muhimmanci su gudu da su, kuma su ki dawo musu da su," in ji Abdul Karim Ibrahim, wani mai karatun digirin-digirgir a Cibiyar Nazarin Afirka da ke Jami'ar Ghana a Accra.

"Ba za a taba amincewa da wannan ba saboda ya saba da ka'idojin da muke tafiya a kai. Kuma ina tunanin wannan yaudara da cin fuska ne ga kakanninmu, musamman wadanda suka fafata yaki don ganin ba a sace wadannan kayayyaki ba," in ji Ibrahim.

Mafi yawan kayan arzikin da aka sace yayin yakin Ingilawa da Asante na bayyana tsagwaron misalin sassakar zinare, al'adu, tarihi, da muhimmancin bauta ga jama'ar Asante.

Duk da cewa Jonathan Ofori, mazaunin Kumasi na kallon matakin a wani abu mai kyau, yana kuma ganin cewa hakan na sake dabbaka rashin adalci na tarihi da karfafa sace kayan tarihi.

Ofori ya fada wa TRT Afirka cewa "Ya zama dole mahukuntan Ghana, da ma Fadar Mashie su kai wannan batu ga mahukuntan Birtaniya, saboda wadannan kaya na sake hada jama'ar Asante da tarihinsu."

Tsauraran dokokin Birtaniya

Amma masu shiga tsakani da suke ta yin aiki ba hutawa na tsawon shekara guda, na bayyana cewa tsauraran dokokin Birtaniya ne suke hana su karbo wadannan kayayyaki daga giudajen adana kayan tarihin Ingila.

"Birtaniya ta kirkiri dokoki tattare da wadannan kayayyaki, kuma dokokin na da tsauri. Dokokin kayan tarihi na da tsauri sosai.

"Gidan adana kayan tarihi na kasa a Ingila ba shi da ikon dawo da kayayyakin gaba daya din-din-din," in ji Ivor Agyeman-Duah, Babban Mai Shiga Tsakani daga Masarautar Asante, yayin tattaunawa da Joy News a Ghana.

Siffar wannan faifan na kama da hudar furen fofoo kafin ta bude ta zama ruwan dorawa. Hoto / V&A Museum

Wannan kiranye da aka yi na ta samun goyon baya a 'yan shekarun nan don ganin an dawo da kayan tarihi da al'adun Afirka da aka sace lokacin mulkin mallaka zuwa nahiyar.

A watan Afrilun 2023, Finland ta dawo da wasu duwatsu masu tarki da 'yan mishan suka sace wa jama'ar Ovambo da ke Namibia a yau.

Sanna akwai matsin lamba na a dawo da dubunnan kayan tarihi da al'adu da dakarun Birtaniya suka sace a lokacin mulkin mallaka, da wadanda aka yi gwanjonsu a Landan kuma wasu kasashe da hukumomin Turai suka saya tare da mallake su.

Wadannan kayayyaki sun hada da dubunnan kayan al'adu na Tagullolin Benin da Birtaniya ta sace daga Masarautar Benin da ke a Nijeriya a yau.

Ivor Agyeman-Duah ya yarda da masu suka da ke cewa dole a dawo da wadannan kayan tarihi, amma fa cimma wannan buri na da matukar wahala.

Ivor Agyeman-Duah ya ce "Kusan shekaru 50 kenan muna ta magana kan a dawo da wadannan kayayyaki, kuma ba mu samu wani cigaba ba. Dole ne mu sake salo da dabaru. Dole ne mu sake duba ga wasu zabukan."

Dubunnan kayan da aka sace suna kasashen waje. amma muhawarar nan da ƙarfinta, masu fafutuka na fatan manyan kasashen Turai da suka sace wadannan kayayyaki za su saduda wata rana su dawo da kayyakin masu daraja ga Afirka sakamakon kiraye-kirayen da ake ci gaba da yi.

TRT Afrika