Ƙasashen biyu waɗanda ke yankin Tsakiyar Afirka a baya sun kasance a ƙarƙashin Masarautar Kongo. / TRT Afrika.

Mutane da dama a faɗin duniya na yawan mamaki kan yadda za a samu ƙasashen Kongo daban-daban kuma kowace a Afirka - wato Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da kuma Jamhuriyar Kongo.

Ƙasashen biyu makwabtan juna ne a tsakiyar Afirka.

Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo na da girman murabba'in kilomita 342,000 da kuma mutum miliyan 5.7.

Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo wato DRC tana da Kinshasa a matsayin babban birninta, ita kuma Jamhuriyar Kongo na da Kongo Brazzaville a matsayin babban birninta.

Domin guje wa ruɗewa, akasari ana bambance ƙasashen da manyan biranensu - wato Kongo Kinshasa da Kongo Brazzaville.

Felix Tshisekedi ya zama Shugaban DRC a 2019. / Hoto: Others

Shugaban Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a yanzu shi ne Felix Tshisekedi inda shugaban Jamhuriyar Kongo na yanzu shi ne Denis Sassou Nguesso.

Tasirin mulkin mallaka

Tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, ƙasashen biyu na Kongo suna haɗe ƙarƙashin Masarautar Kongo - har da ƙasar Angola a yanzu.

Duka ƙasashen ba wai suna ɗaya kaɗai suke da shi ba, jama'arsu na da harsuna iri ɗaya - wato harsunan Lingala da Kikongo.

Haka kuma Faransanci shi ne harshen da ake amfani da shi a hukumance a ƙasar sakamakon Faransa ce ta yi musu mulkin mallaka.

Faransa ce ta ba Kongo Brazzaville ƴancin kai. Duk da cewa Kongo Kinshasa a ɗayan ɓangaren ƙasar Belgium ce ta ba ta yancin kai, ƴan Belgium ɗin su ma suna amfani da Faransanci a matsayin harshensu.

Cobalt na daga cikin albarkatun ƙasa da DRC ke da shi. / Hoto: AFP

Ƙasashen Turai sun rinƙa zaluntar ƙasashen Kongon biyu inda suka kwashe musu ma'adinai. Ƙasashen biyu suna zagaye da Kogin Kongo inda suke da tarin albarkatun ƙasa waɗanda suka haɗa da zinare da cobalt da copper.

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC)

Yana da muhimmanci a fahimci cewa an zana iyakokin ƙasashe na zamani a Afirka a lokacin da aka kakkasa nahiyar, lokacin da ƙasashen Turai suka ware wa kansu yankuna a taron Berlin na 1884-1885.

Sarki Leopold na biyu na Belgium ya lallashin taron kan ya ba shi damar kula da yankin Kongo, saboda abin da ya kira ‘kokarin jin kai’ a can.

Ya saka wa ƙasar suna Congo Free State - wadda ita ce Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a yanzu.

Sai dai kuma an tafka zalunci da dama a lokacin mulkinsa da suka hada da azabtarwa da yunwa.

An tilasta wa mutanen Kongo yin aiki domin haƙo albarkatu waɗanda suka haɗa da roba da kuma farautar giwaye domin cire haurensu domin Leopold ya wadata kansa.

Alkaluma sun bambanta, amma sama da mutum miliyan 10 - wato rabin al'ummar Kongo a wancan lokacin - sun mutu sakamakon ta'asar da aka aikata.

A shekarar 1908 ne gwamnatin Belgium ta karbi ragamar mulkin kasar, inda aka fi sanin sunan ƙasar da Belgian Kongo.

Kongo ta samu ƴancin kai a ranar 30 ga Yuni, 1960, kuma ta samu sunan 'Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo''.

Sai dai a cikin 1971, shugabanta Mobutu Sese Seko ya canza sunan ƙasar zuwa Jamhuriyar Zaire - kalmar da aka samo daga harshen Kikongo - ma'ana 'Kogin da ke haɗiye wasu koguna'.

Bayan ya mutu a 1997, an canza sunan zuwa Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC).

Ana yawan kiran Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo a matsayin Kongo-Kinshasa don bambanta ta da Jamhuriyar Kongo, wadda sau da yawa ake kira Kongo-Brazzaville.

Jamhuriyyar Kongo (Kongo Brazzaville)

Yayin da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo (DRC) ta kasance karkashin kasar Belgium, Faransa ce ta yi wa Jamhuriyar Kongo (Kongo-Brazzaville) mulkin mallaka tun a shekarun 1880, sannan masu mulkin mallaka suka saka Brazzaville a matsayin babban birninta.

Faransawar waɗanda suka mayar da hankali wajen daukar ma'aikata da hako albarkatun kasa, sun tilasta wa 'yan Afirka gina ababen more rayuwa don taimaka wa tattalin arzikin gwamnatin mulkin mallaka.

Misali, an kiyasta cewa tsakanin ƴan Afirka 15,000 zuwa 20,000 un mutu a lokacin gina layin dogo na Kongo-Ocean tsakanin 1921 zuwa 1934.

Denis Sassou-Nguesso ya zama shugaban Jamhuriyar Kongo tsakanin a 1997. / Hoto: AFP

Kongo-Brazzaville ta samu ƴancin kai a ranar 15 ga Agusta, 1960 kuma ta samu sunan "Jamhuriyar Kongo", wanda ta ci gaba da kasancewa har yau.

Shugaban Jamhuriyar Kongo (Kongo-Brazzaville) na yanzu shine Denis Sassou Nguesso wanda ya hau karagar mulki a shekarar 1997.

TRT Afrika