Daga Eudes Ssekyondwa
Kamfanin China mai suna CNOOC International, wanda yake cikin manyan kamfanoni masu karfi a bangaren makamashin kasar Uganda ne ke aiki tukuru domin hako man fetur din daga rijiyar Kingfisher kafin lokacin da aka kayyade.
Kamfanin Man Fetur na Uganda, wato Petroleum Authority of Uganda (PAU) ne yake sa ido kan aikin. Sai dai yana fuskantar kalubale da dama, musamman kan batun muhalli, kasancewar aikin ya fara jawo gurbacewa da wasu matsalolin muhalli a kasar.
“Yanzu haka, mun fi mayar da hankali ne a kan hako man daga rijiyar farko,” in ji Michael Okello, jami’in PAU a tattaunarwarsa da TRT Afrika.
Masana harkar hako ma’adinai sun kiyasta cewa rijiyar ta Kingfisher za ta iya samar da gangan mai miliyan 180. Kasar Uganda na da burin amfani da albarkatun man fetur din domin yaki da talauci da inganta ababen more rayuwa.
Ana cigaba da hako man ne tare da shimfida hanyoyin bututun mai, inda za a rika tafiyar da shi daga rijiyar zuwa matatar man da ke yankin ma’aikatu na Kabaale Industrial Park.
An kiyasta cewa akwai akalla gangan man fetur biliyan 6.5 kwance a Yammacin Uganda, inda daga ciki akwai akalla ganga biliyan 1.4 da ya isa hakowa domin kasuwancinsa.
Aikin na hako man a yanzu na hadaka ne, inda kamfanin TotalEngergies EP na kasar Faransa ke da kaso mafi yawa na kashi 56.67, sai CNOOC International mai kashi 28.33, sai kamfanin man fetur na Ugandan mai kashi 15.
Bayan rijiyar Kingfisher, ana kuma aikin hako mai a Tilenga. Sama da rijiya 400 ne kamfanin TotalEngergies ke aikin hakowa a Tilenga, wanda shi ne daya bisa ukun babban gandun dajin Uganda, wato Murchison Falls.
Haka kuma kamfanin na kasar Faransa ne yake da kaso mafi yawa na kashi 62 na aikin shimfida bututun mai a kasar na Gabashin Afrika, wanda ya kai tsawon kilomita 1,443 domin tafiyar da man fetur din daga Kabale-Hoima zuwa birnin Chongoleani da ke kusa da tashar jirgin ruwa ta Tanga da ke Tanzania.
Idan aka kammala, bututun man zai dauki gangan mai 246,000 a kullum.
Barazana ga muhalli
Sai dai masana muhalli suna ta nanata yiwuwar gurbacewar muhalli daga ayyukan na kamfanin na kasar Faransa.
“Aikin shimfida bututun man ya shafi gandun dazukanmu. Muna fargabar ayyukan kamfanin zai shafi rayuwar dabbobinmu idan ba su bi a tsanaki wajen adana halittun da muhalli ba,” inji Diana Nabiruma na Cibiyar Africa Institute for Governance a zantawarta da TRT Afrika.
“Idan muka tarwatsa dazuka, halittun da suke rayuwa a cikin dazukan za su watse. Wannan yana da matukar muhimmanci a kula da shi,” inji ta.
Haka kuma akwai bukatar biyan diyya ga mutanen da aikin hako man ya raba da muhallansu.
A nasa bangaren, Kamfanin TotalEngergies ya ce aikin da yake yi a Tilenga da EACOP ya sa dole ya saya fulotai da suka kai fadin hekta 6.400.
Daga ciki akwai sauya muhalli ga iyalai 775, wanda ya shafi kimanin mutum 19,098.
A Satumban 2022, Majalisar Turai, wadda Faransa ke ciki ta bayyana, “damuwa matuka kan take tauye hakkin mutane a kasashen Uganda da Tanzania,” biyo bayan aikin na shimfida buttutun man.
Mambobin majalisar sun bayyana cewa kusan mutum 118,000 ne aikin ya shafa, wanda daga cikinsu akwai wadanda aka rusa musu gidajensu domin samar da hanyar motoci.
A watan Julin 2023, kungiyar Human Right Watch ta fitar da wani rahoto a game da ayyukan kamfanin TotalEnergies bayan tattaunawa da mutanen kasar, ciki har da iyalai 75 da aikin ya raba da muhallansu daga yankuna biyar na Uganda.
Rahoton ya bayyana cewa, “Manoma sun ce an tilasta musu amincewa da yarjejeniyar biyan diyya da aka rubuta da Ingilishi, wanda kuma mafi yawansu ba sa iya karantawa, wasu kuma sun bayyana cewa tsabar kudi aka ba su a madadin canja musu fulotai da tsarin duniya ya tanada.”
“Sun zo suna ta dandana mana zuma a baki,” kamar yadda wani dan yankin ya bayyana. “Mu kuma sai muka amince da su. Yanzu mun rasa fulotanmu, kuma ba mu samu kudaden diyyar ba, sannan ’yan fulotan da suke rage mana, ambaliya ta mamaye su, sannan kura ta gurbata iskar da muke shaka.”
Kamfanin TotalEngergis ya kare kan shi a wata wasika da ya rubuta zuwa ga kungiyar Human Rights Watch, inda ya ce kamfanin ya biya diyya kamar yadda dokokin kasar Uganda ya tanada.
A Yunin bara, ’yan kasar Uganda su 26 sun maka kamfanin TotalEnergies a kotu a birnin Paris bisa zargin tauye hakkin mutane a kasar.
A daidai lokacin da ake cigaba da wannan tata-burzar, da kuma ganin zuma da madin aikin, mutanen kasar Uganda na fata aikin zai inganta tattalin arzikin kasar, a daidai lokacin da wadanda aikin ya shafa suke jiran a biya su diyya.