An zafafa sosai a yayin gangamin zabe a Liberia. Hoto: Reuters

Daga Emmanuel Onyango

An yaba wa shugaban kasar Liberia George Weah sakamakon amincewa da shan kaye a zabe, bayan kwashe shekaru shida yana mulki sakamakon nasarar mika mulki ga farar hula a karon farko bayan yakin basasar da aka tafka.

Buga wayar da ya yi tare da taya shugaban da aka zaba Joseph Boakai ya kwantar da hankali a kasar da ake zaman dar-dar.

"Liberia ta yi nasara," in ji Weah yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a rediyo bayan sanar da sakamakon zabe.

Cigaban siyasa a Liberia abu ne da ake wa kallon sabo a tsakiya da yammacin Afirka, inda a 'yan shekarun nan sojoji suke yawan juyin mulki da kara wa'adin zaman su a kan mulkin.

"Ba abu ne da aka saba gani a wannan yankin ba a ce shugaba ya amince da ya fadi zabe. Duba da yadda aka fafata a zaben, sannan shugaba mai ci ya fito ya amince da an kayar da shi, ina tunanin wannan abun yabawa ne," in ji Adama Dempster, Sakatare Janar na Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam a Liberia.

Radadin yakin basasa

"Shi (Weah) ya kafa tarihi da kin aiki da tsarin siyasar Yammacin Afirka." ya fada wa TRT Afirka.

George Weah ya kira abokin takararsa ta waya tare da taya shi murna.

Weah dan shekara 57, tsohon dan kwallon kafa na kasa da kasa, a zagayen farko ya kara da 'yan takara 19, wanda daga nan takarar ta dawo tsakanin mutane biyu kawai. Ya sha kaye da tazarar kuri'u 20,567. A shekarar 2017 aka zabi tsohon dan kwallon na FIFA.

A tsakanin shekarun 1989 da 2003 kasar ta sha fama da yakin basasa ya yi ajalin mutane kimanin 250,000, amma a yanzu tana farfadowa a hankali tare da sharbar romon dimokuradiyya.

Dempster ya kara da cewa "Liberia ta zama kasar abar misali na kwarai da dimokuradiyya ke aiki.

"Mun yi zabuka cikin nasara tun bayan yakin basasa, kuma zabuka ne da suke na gaskiya ba tare da magudi ko wuru-wuru ba."

A zagayen farko na zaben Boakai ya kayar da Weah. Hoto: Reuters

An samu damuwa da tsammanin afkuwar rikicin bayan zabe sakamakon arangama da aka samu tsakanin magoya bayan 'yan takara daban-daban a yayin zagaye na farko da aka gudanar a watan Oktoba. An kuma samu tashin hankali tsakanin kabilu da kauyuka.

ECOWAS ta bazama

Wannan yanayi ya zaburar da Kungiyar Yammacin Afirka ta ECOWAS, wadda ta yi gargadi kan sanar da sakamakon da ba shi ba, sannan ta gargadi masu ingiza rikici kan za ta tuhume so kan duk abu mara dadi da ya faru.

Ta yi gargadi da cewa "ECOWAS, Tarayyar Turai da Kasashen duniya za su tuhume su da alhakin duk wani abu da aka yi wanda ya janyo rikici."

Kungiyar mai kasashe 15 na Yammacin Afirka na ta kokarin daidaita kanta inda ta ke ta fama da juyin mulki a shekaru uku da suka gabata, yayin da kasashe hudu suka koma karkashin mulkin soja. Kasashen sun hada da Nijar, Mali, Burkina Faso.

A karon farko kenan da aka gudanar da zabe bayan ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, wadanda aikinsu ya kawo karshe a kasar a 2003 bayan gama yakin basasar.

Duk da cewa Liberia ta kammala zaben ba tare da rikici ba, masu fafutuka da kare hakkon dan adam na cewa har yanzu akwai rabuwar kawuna d asuke bukatar a magance su cikin kankanin lokaci.

Hadin kan Liberia

Dempster added. Dempster ya kuma ce "Ina tunanin kalubalen shi ne a hada kan dukkan 'yan kasar Liberia waje guda, a kirkiri yanayi na kula da kasa, zama tare da fara tattaunawar sulhu."

A kalla mutane biyu ne suka mutu, wasu 18 suka jikkata yayin da mota ta kutsa kan masu murnar nasarar Boaka.. Hoto: Reuters

A jawabin sa na amincewa da shan kaye, Weah ya tunatar da wanda zai gaje shi cewa "'Yar karamar rata ta kuri'un da aka samu na nuni da tsananin rarrabuwar kan da ake da shi a kasarmu."

Ya kara da cewa "Mu daure mu magance wannan rarrabuwar kawuna da yakin neman zabe ya janyo, sannan mu hada kai a matsayin kasa daya al'umma daya."

Zababben shugaba mai jiran gado Boakai ya bayani tare da yin kiran da a hada kai don sake gina kasar inda ya kuma tabbatar da karbar mulki cikin nutsuwa.

A ranar Talatar nan Boakai ya bayyana cewa "An gama zabuka, kuma dole mu hada kai waje guda a matsayin al'umma don sake gina kasarmu."

Ya kara da cewa "Ina rokon dukkan 'yan Liberia, ba tare da duba ga kabila, yare, kasa, asali, addini ko 'rayin siyasa ba, a su zo mu tafi tare don kubutar da kasarmu."

TRT Afrika