Riek Machar da Salva Keir ne suka mamaye siyasar Sudan ta Kudu. Hoto: AP

Daga Coletta Wanjohi

Shekaru kasa da 13 bayan samun 'yancin kai daga Sudan, kasa mafi karancin shekaru da kafuwa a duniya - Sudan ta Kudu - na iran lokaci mai muhimmanci a tarihinta: babban zabenta a karo na farko.

"Jama'ar Sudan ta Kudu na son zabe, kuma ya zama dole mu samu gudanar da zabe a watan Disamban 2024." in ji James Morgan, Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu yayin tattaunawa da TRT Afirka.

Tun 9 ga watan Yulin 2011, Sudan ta Kudu ke murnar wannan rana a matsayin ta samun 'yancin kai, kasar ta kuma fuskanci shugabancin mutum guda Salva Kiir.

A yayin da gwamnati ta gamsu da cewa lokacin Sudan ta kudu ya yi na gudanar da zabe, Majalisar Dinkin Duniya na da damu kan cewar ba lallai zaben ya zama na gaskiya ba, kuma ba tare da wasu matsaloli ba.

Abubuwan da aka gani a kasar a baya-bayan nan na iya tabbatar da me MDD ke fadi. Sudan ta Kudu ta fada yakin basasa a 2013, wanda lamarin ba iya zamantakewa ya shafa ba, har da ma tattalin arziki.

"A yayin da abubuwa suka tsaya, Sudan ta Kudu ba ta shirya gudanar da zabe ba. Ana bukaytar yin abubuwa da dama kafin wannan abu," in ji Jean-Pierre Lacroix, wakilin Majalisar DInkin Duniya kan wanzar da zaman lafiya, yayin da yake bayar da rahoto ga Kwamitin Tsaro.

"Akwai babban rikici game da albarkatun kasa d akuma rashin ayyukan yi a tsakanin matasa."

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa "Gogayyar samun mulki a tsakanin 'yan boko, daduwar rikici tsakanin kabilu da kuma yawaitar masu barin kasar zuw akasashe makota" na daga matsalolin.

A watan Yulin 2015 aka shirya Sudan ta Kudu za ta gudanar da zabe a karon farko, amma wani rikicin cikin gida da ya balle a Disamban 2013 ya sanya aka kasa aiwatar da wannan shiri.

Gwagwarmayar neman mulki tsakanin gwamnatin Shugaba Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Mashar ta janyo barkewar rikici d aya sanya aka dakatar da gudanar da zaben, aka kassara dimokuradiyya da sauran al'amuran kasa.

Rikicin dan adam da yaki ya kara ta'azzarawa ya janyo asarar rayuwa 400,000 tare da raba sama da mutane miliyan biyar da matsugunansu. Kusan rabn wadanda aka raba da matsugunan nasu sun gud zuwa kasashen Suan, Ethipia da Udanga da ke makotaka da Sudan ta Kudu.

Ministan Harkon Waje Morgan ya shaidawa TRT Afirka cewa "Mun fada mutane na koyon darussa daga abubuwan da suka faru a baya.

Tarihi malami ne, mafi yawan mutan a South Sudan sun fahimci yaki ba abun so ba ne. Wannan fahimta ce daya daga matakai mafiya muhimmanci."

Dage lokacin gudanar da zabuka

Bayan shekaru na yaki da rashin nasarar samar da tsagaita wuta a lokuta daban-daban, gwamnati da jam'iyyun adawa sun sanya hannu kan yarjejeniyar kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu a ranar 12 ga Satumban 2018 a Addis Ababa babban birnin Ethipia.

Wanna ne ya bayar da damar kafa Gwamnatin Rikon Kwarya da Farfado da Hadin Kan Kasa, wadda ta sha yin alkawarin gudanar da zabe don dora kasar kan turbar dimokuradiyya.

Tare da jinkirtawa wajen aiwatar da wadannan alkawarori, sai aka dinga matsa lamba don a gudanar da zabe.

A watan Agustan 2022, gwamnatin rikon kwaryar ta kara wa'adin gudanar da zabe zuwa watan Fabrairun 2025. Sai kuma ta dawo da shi watan DIsamban 2024.

Morgan ya kara bayani da cewa "Ana kan tattaunawar zaman lafiya. Sai annoba da wasu abubuwa suka kawo tsaiko, sai muka sake samar da sabuwar taswirar aiki.

Ma'anar karin watanni 24 na gwamnatin rikon kwaryar ita ce don a samu damar kara ayyukan da ake yi."

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa zabe na gaskiya na bukatar "sabon kundin tsarin mulki, jerin sunayen masu jefa kuri'a, yanayin samar da tsaro a lokacin zabe, kayan aiki da kwararrun ma'aikata, da ma jami'an tsaro, tare da tsarin warware matsalolin da ka iya tasowa."

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi amanna cewa kafin zabe za a kammala samar da duk wadannan abubuwa.

"Babu lokacin cewa lallai mu shiryawa zabe. Wasu mutane za su ce mu dakata. Wadannan zabuka na mutanen kasa ne. Abu ne ba su me suke bukata."

Zaben Sudan ta Kudu zai zama daya daga cikin zabuka 15 da za a gudanar a nahiyar a bana, inda Tarayyar Afirka za ta zama mai sanya idanu. Kungiyar tra nahiyar na kallon a matsayin "ingantacciyar turbar dimokuradiyya".

Wasu kwararru na cewa gudanar da zabe a kasar na iya samar da shugabanci mai karfi da ake bukata sosai, da kuma kawo gyare-gyare da za su inganta rayuwar jama'ar kasar su sama da miliyan 11.

Ya zuw ayanzu dai, shugaba Kiir mai ci ne kadai ya nuna sha'awar tsayawa takara a zaben na watan Disamba.

TRT Afrika