‘Yan takara 18 ne suke fafatawa a zaben amma hudu ne suka fi jan hankalin ‘yan kasar, sai kuma mace daya tilo da ta zama kallabi tsakanin rawuna.
Wadannan ‘yan siyasa fitattu ne a ciki da wajen kasar kuma sun rike mukamai na siyasa da wasu fannonin rayuwa.
‘Yan takarar su ne: Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu, Chichi Ojei, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
Fitaccen dan siyasa kuma tsohon mataimakin shugaban kasa
Atiku Abubakar, wanda ya sami shaidar dimploma a kan harkar sharia’a daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria da kuma digiri na biyu kan huldar kasa da kasa daga Jami’ar Anglia Ruskin da ke Ingila, ya dade yana neman shugabancin Nijeriya: ya soma neman shugabancin kasar tun da ya yi takara a zaben fid da gwani na tsohuwar jamiyyar SDP a shekara 1993.
A shekarar 1998 tsohon jami’in kwastam din ya ci zaben gwamnan jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar a karkashin jam’iyyar PDP amma kafin a rantsar da shi, ya amshi goron gayyata na zama abokin takarar tsohon shugaban sojan Nijeriya, Olusegun Obasanjo, a karkashin inuwar jam’iyyar ta PDP.
Sun ci zabe kuma sun jagoranci kasar a wa’adi biyu na tsawon shekara takwas. A lokacin mulkinsu (1999-2007), Nijeriya ta yi nasarar samun afuwar bashin biliyan $18 daga kasashe masu ba da lamuni na Paris Club bayan kasar ta biya dala biliyan $12.
Gwamnatin ta kuma bai wa ‘yan kasuwa damar shiga fagen sadarwar kasar, lamarin da ya sa ‘yan kasuwa na kasashen waje suka sanya hannayen jari daga kasashen waje suka shigo kasar tare da samar da ayyukan yi.
Atiku Abubakar ya yi alkawarin samar da irin wannan cigaban idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa. Yana kuma alkawarin hada kan kasar tare da sake fasalinta da kuma inganta harkar tsaronta.
Dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP din ya yi ammanar cewa zai ci zaben a wannan karon. Jam’iyyarsa, wadda ta mulki kasar daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2015 ce ke da mulki a jihohi 14 cikin jihohi 36 na kasar tare da kasancewa da karfi a wasu jihohin.
Amma dan takarar, mai shekara 76, bai tsaya a jihohin PDP kawai ba. Yana kokarin jan ra’ayin jihohin da ke karkashin jam’iyyar APC mai mulki. Yana zagaya sassan kasar don neman mutane su ba shi damar jan ragamar mulkin kasar.
“Idan kuka zabe ni a matsayin shugaban kasa, na fada kuma na yi alkawari … zan ware dala biliyan 10 domin tallafa wa matasanmu da ke da kananan sanao’i,” in ji Atiku a lokacin da yake ganawa da magoya bayansa a birnin Legas.
“Mutane suna tambaya ta cewa a ina zan samu dala biliyan goma. Idan na sayar matatan man Fatakwal da na Warri da na Kaduna, zan samu kudin.”
‘Dan Birni’ ya dage da yakin neman zabe
Bola Ahmed Tinubu, dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, wanda ya samu shaidar karatun digiri a fannin Akanta daga jami’ar jihar Chikago ta Amurka a shekarar 1979, ya shiga siyasa ne a farkon shekarun 1990 bayan ya yi aikin Akawu a kamfanoni irin su Delloite da Mobil Nigeria. Ya yi gwamna sau biyu a jihar Legas, babban birnin kasuwancin kasar daga shekarar 1999 zuwa 2007.
A wancan lokacin ya kara yawan kudin shigar jihar matuka. Shi ya assasa wasu manyan ayyuka a Legas kamar unguwar Eko Atlantic City (wadda aka kirkira bayan an yi wa unguwar Victoria Island katanga daga ruwan teku da ke kwararowa unguwar VI) da kuma kasuwar kasa-da-kasa mara haraji ta Lekki, wato Lekki Free trade Zone inda matatan mai din Dangote, wadda ita ce matata daya mafi girma a duniya take.
Tinubu yana yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin samar da irin wadatar da ya samar a Legas.
Mai shekara 70 din da magoya bayansa ke yi wa lakabi da ‘dan birni’ yana da kwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC, wadda ke da gwamnoni 21 daga cikin gwamnoni 36 na kasar, za ta cigaba da mulkin kasar. Sai dai kuma bai yi kasa gwiwa ba. Yana zagayawa sassan kasar inda yake ganawa da masu ruwa da tsaki domin neman goyon bayansu.
“Idan kuka zabi jam’iyyar APC, ciwon da ke damunku zai warke,” a cewar Tinubu ga magoyan baynsa a jihar Binue da ke tsakiyar Najeriya.
Ya shaida wa magoya bayansa a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Nijeriya cewa: “Idan kuka zabe ni, kun zabi cigaba, kun zabi bunkasa harkar noma, kun zabi inganta wutar lantarki mai dorewa.”
Kallabi tsakanin rawuna
Princess Chichi Ojei ita ce mace daya tilo cikin ‘yan takarar shugaban kasan Nijeriya a zaben 2023.
‘Yar takarar, wadda ta fito daga jihar Delta a kudancin Nijeriya, ta yi karatu a ciki da wajen kasar. Ta halarci makarantu irin su American International School of Lagos, Institut Le Rosey da kuma jami’ar Northeastern University.
‘Ya ce ga attajiri Emmanuel Ojei. Shafinta na kafar sadarwa ta LinkedIn ya nuna cewa babbar kwararriyar jami’a ce ta harkar kudi a kamfanin Nuel Ojei Holdings.
A shekarun bayan, an samu mata irin su Sarah Jubril da Oluremi Sonaiya da suka tsaya takarar shugaban kasar. Amma ba su cimma burinsu ba.
Shin za ta zarce daga takara zuwa shugabancin Nijeriya? ‘Yar takarar jam’iyya APM na da kwarin gwiwar cewa za ta zama mace ta farko da za ta shugabanci kasar Nijeriya. Ta yi imanin cewa za ta lashe zaben shugaban kasa domin yawan mata da matasa a cikin ‘yan Nijeriya.
Mai shekara 44 din ta ce an jima ana hana mata da matasa taka rawa wajen gudanar da mulkin Nijeriya. Tana ganin lokaci ya yi da ya kamata a bai wa mata da matasa da suka fi yawa a Najeriya damar jan ragamar mulkin kasar.
A hirar da ta yi da kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) Princes ta ce: “Zan samar da yanayi da zai habaka tattalin arziki, kwanciyar hankali a fagen siyasa, hadin kan kasa da kuma zaman lafiya ta fagen addini da zamantakewa.
“Son mayar da Nijeriya tafarkin daukaka ne ke gabana.”
Kwankwasiyya: Jar hula, ‘ya’yan ‘amana’
Rabiu Musa Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano ne. Tsohon ma’aikacin gwamnatin ya taba ministan Tsaro daga shekarar 2003 zuwa 2007 tsakanin wa’adi biyun da ya yi yana mulkin jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar (PDP). An san gwamnatinsa da samar da abubuwan more rayuwa da kuma inganta harkar ilimi. Ya gina hanyoyi da gadaje a Kano. Ya kuma gina jami’o’i biyu mallakar jihar Kano, Jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano da ke Wudil da kuma jami’ar Northwestern University.
A lokacin da yake kan karagar mulki a Kano ya ba da damar karatun digiri na biyu kyauta ga ‘yan jihar 2,600 zuwa kasashe 14. Ya cigaba da ba da damar karatun digiri din kyauta bayan ya kammala wa’adinsa. Wadannan nasarorin da kuma kwarewar da ya samu a lokacin da ya yi ministan tsaro na cikin abubuwan da yake yakin neman zaben shugaban kasa da su.
Tafiyarsa ta Kwankwasiyya da aka fi sani da saka jajayen fuluna ta mamaye jiharsa ta Kano da wasu sassan Arewacin Nijeriya. Wasu sanannun ‘yan siyasa daga jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP sun shiga jam’iyyasa, musamman a arewacin kasar.
Dan takarar, mai shekara 66, ya ce yanzu yana kutsa kai kudancin kasar ne. Yana da yakinin cewa zai ci zaben 2023.
A lokin da yake magana a wani gangamin yakin neman zabe a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Nijeriya, Kwankwaso ya ce : “Tsarinmu zai magance matsalolin kowa a kasar nan, musamman matasa maza da mata wadanda suke son zuwa makaranta, wadanda suke son su samu ayyukan yi da sauransu. Babu wanda za a hana karatu domin matsayinsa.”
Tafiyar ‘Obedients’ ta dage
Peter Obi na daya daga cikin ‘yan takarar da ke sahun gaba a cikin masu neman shugabancin Nijeriya. Dan takarar, mai shekara 61, tsohon ma’aikacin banki ne wanda ya yi gwamnan jihar Anambra na tsawon shekara takwas tsakanin shekarar 2007 zuwa 2014 a karkashin inuwar jam’iyyar APGA.
Mista Obi ya adana wa jihar Anambra kudi kuma ya saka mata hannayen jari a kamfani mai zama kansa. Ya kuma mayar da hankalin kan harkar ilimi da lafiya a lokacin mulkinsa. Dan kasuwan da yake neman shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Labour Party, yana neman jan hankalin ‘yan Najeriya da tarihinsa na adana kudi da kuma maganar da yake na mayar da Najeriya kasa mai kerekere daga kasa mai sayan abubuwa
Dan takarar, wanda ake yi wa magoya bayansa akabi da sunan Obidients, yana da farin jini sosai a kafafen sadazumunta inda yake samun nasara a kuri’un jin ra’ayin jama’a. Idan masu suka suka ce masa jam’iyyarsa ba ta da mutane a kasa, sai Peter Obi y ace ‘yan Najeriya da ke shan wahala ne mutanensa dake kasa. Sai dai bai dogara kacokan a kan mutanen nasa ba. Yana yawo sassan kasar domin yakin neman zabe.
“Alkawarin da Datti da ni muka dauka wa mutanen Kano shi ne na daya mu kare mutanen Nijeriya,” in ji Obi cikin magoya bayansa a birnin Kano da ke arewa maso yammacin kasar.
“Za mu tabbatar da cewa abokan gaba, masu laifi ba su fi gwamnati karfi ba.”
‘Yan Nijeriya ne dai za su kada kuri’un da za su tabbatar da ko kuma musanta fatan wadannan ‘yan siyasan a zaben gamagarin da za su yi cikin watan Fabrairun 2023.