Sama da mutane miliyan ne suka gudu daga Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo saboda rikici. Hoto: TRT Afrika

Daga Dayo Yussuf

Kanyere da 'ya'yanta maza su biyar sun zauna a sansanin Don Bosco da aka jibge 'yan gudun hijira da suka rasa matsugunansu a garin Goma na tsawon shekaru uku.

Rikici tsakanin dakarun gwmanati da mayakan M23 'yan tawaye ne ya tirsasa wa mutanen barin gidajensu a gundumar Rutshuru da ke lardin Arewacin Kivu.

A yayin da aka gudanar da babban zabe, wadanda aka raba da matsugunansu irin su Kanyere ba su samu damar amfani da hakkinsu na 'yan kasa ba.

Kanyere Mbenda ta fada wa TRT Afirka cewa "Na yi matukar bakin ciki a zuciyata saboda ba ni ma da lokacin tunanin wani zabe."

Matar mai matsakaicin shekaru na bibiyar labaran siyasa, amma kuma ta ce ba su samu sukunin jefa ƙuri'a ba.

"Ina kuka dare da rana. Ina tunani game da yarana da abun da za mu ci, ba ma iya samun mudun shinkafa da ake sayarwa da rahusa, me ya sa zan damu kaina da wani batun jefa kuri'a?" in ji Kanyere.

'Abinci na fi bai wa fifiko'

Kanyere na daga cikin 'yan kasar Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo a yankunan Kivu ds Goma miliyan 6.9 ne suka kauracewa gidajensu saboda rikicin da ake yi tsawon shekaru.

Alkaluman Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR na cewa rikicin baya-bayan nan da ya barke tun watan Oktoba tsakanin mayakan M23 da dakarun gwamnati ya janyo daduwar 'yan gudun hijira cikin kankanin lokaci a kasar.

Kungiyar Yaki da Gudun Hijira ta Kasa da Kasa (IOM) ta ce baya ga wadanda aka raba da matsugunansu a cikin kasar, rikicin ya kuma tilastawa sama da mutum miliyan guda guduwa daga kasar. Mafi yawan su ba su samu damar jefa kuri'a ba a zaben.

Hukumar zaben ta bayyana cewa ba za a jefa kuri'a a sansanonin 'yan gudun hijira ba. Hoto TRT Africa

Shugaba mai ci Felix Tsishekedi da ke neman wa'adi na biyu na fuskantar wasu 'yan takara na adawa su sama da 20. Haka kuma za a zabi 'yan majalisar dokoki a zaben.

Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo na daya daga cikin kasashen duniya mafiya arziki duba da yawan albarkatun kasa, amma tsawon shekara tana ta fama da yaki.

Kanyere ta yi amanna da cewa mutane irin ta ba sa amfana da arzikin kasar. Tana jin ana tauye mata hakki inda 'yan siyasa da kasashen waje suke sace arzikin kasarsu.

Kanyere ta ce "A lokacin da suke ba ni abinci da yarana, za mu fahimci juna, sannan ina son su ba ni wajen da zan zauna na kula da yarana."

Mafi yawan 'yan gudun hijirar sun gujewa hare-haren 'yan tawaye a Gabashin Kongo. Hoto: TRT Africa

Salomon Munyandekwa, wanda shi ma ya gujewa rikicin tare da iyalinsa zuwa sansanin Rutshuru ya bayyana ra'ayi iri daya da na Kanyere.

'Muna bukatar tsaro'

Salomon ya yi korafi da cewa "Muna shan wahala sosai. Yanz idan mutum yana gwagwarmayar yadda zai rayu, kuma a ce wai maimakon ya tafi neman abinci sai ya je ya hau layin jefa kuri'a?"

Ya kara da cewa "Ka ga wannan babbar matsala ce gare mu wadda za ta sanya da yawan mu ba za su iya jefa kuri'a ba."

Ba wai rikicin ne kadai yake takurawa mutane guduwa daga gudajensu ba. Ambaliyar ruwa ma ta raba dubban daruruwan mutane da gidajensu a wannan shekarar.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun ce suna son jefa kuri'a idan har gwamnati za ta samar da isassun matakan tabbatar da tsaron lafiya da rayukansu.

"Za mu so a ce mun jefa kuri'a a zabukan a yayin da makiya ('yan tawaye) ba sa nan," in ji Salomon.

Sama da mutane miliyan shida aka raba da matsugunansu a Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo sakamakon yaki. Hoto TRT Afrika

Hukumar Zabe ta Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta bayyaba cewa ba a yi tanadin ajje akwatunan zabe a sansanonin 'yan gudun hijira ba.

Hukumar zaben ta kara da cewa ba za a gudanar da zabe a gundumomin Rutsuru da Masisi ba saboda hare-haren 'yan tawaye.

A zaben 2018, miliyoyin 'yan kasar Kongo ba su iya jefa kuri'a ba saboda dalilin rashin tsaro.

TRT Afrika