Daga Edward Qorro
Labarin Jacob Zuma, tsohon Shugaban Kasar Afirka ta Kudu, wani labari ne da ke nuna fafutikar siyasa, bayan ya dawo domin sake takarar shugabancin ƙasar bayan shekara shida da barinta.
Har yanzu Zuma mai shekara 82 yana da ƙima da mutumci a ƙasar, sai dai yana fuskantar matsaloli a takarar ciki har da shari'o'i.
A daidai lokacin da aka fara shirye-shiryen shiga takarar ne Hukumar Zaben Kasar, Independent Electoral Commission (IEC), ta diga alamar tambaya a kan halascin takararsa, inda take nuna daure da aka yi a shekarar 2011 saboda raina kotu.
Ko a Jam'iyyar uMkhonto we Sizwe (MK) ma tsohon Shugaban kasar yana fuskantar kalubale. Gidan talabijin gwamnati na kasar, SABC ya ruwaito a makon jiya cewa yana fuskantar barazanar kora daga jam'iyyar.
Haka kuma akwai alakarsa da iyalan Gupta na Indiya masu dimbin arziki tana kawo masa tarnaki kasancewar ana zargin alakarsa da iyalan suke yi na kasuwanci, wanda shi ne ya yi sanadiyar samun matsalarsa da Jam'iyyar African National Congress (ANC) da ya baro.
Adawar da ke tsakanin Zuma da Shugaban Kasar na yanzu, Cyril Ramaphosa, wanda tsohon mataimakinsa ne ya sa ya fice daga ANC, ya koma MK, wadda a da bangaren jami'an tsaro ce ta ANC a zamanin fafutikar yaki da nuna bambancin launin fata.
Mutane ba su samu natsuwar cewa Zuma zai iya samun nasara a sabuwar jam'iyyar ta MK ba. Amma dai shigarsa takarar za ta rage wa ANC kuri'a wanda zai kara bude takarar.
A watan Afrilun, wani binciken da Ipsos ta gudanar ya nuna cewa Jam'iyyar MK za ta iya samun sama da kashi 8 na kuri'un, sannan ANC za ta iya rasa mafi rinjaye a majalisar kasar a karon farko.
Mutum mai masoya da yawa
Duk da cewa Zuma na da abokan hamayya da yawa, amma magoya bayansa suna da tunanin cewa shi ne ya fi cancanta.
Suna cewa yana da dimbin masoya, sannan ya yi an gani, wanda hakan ya sa a cewarsu ya fi sauran cancantar gyara siyasar kasar, wadda take da shekara 30 tun bayan matsalolin nuna wariyar launin fata.
"Zuma ne ya fi cancanta. Yana cikin wadanda suka yi fafutikar kwato 'yancin kasar har ya je fursuna," inji Charles Odero, Babban Darakta na hukumar lauyoyi masu taimakon marasa karfi ta Civic and Legal Aid Organisation (CiLAO), a zantarwarsa da TRT Afrika.
An haifi Jacob Zuma ne a shekarar 1942 a wata karkara mai suna Nkandla. Mahaifinsa dan sanda ne, amma ya rasu Zuma yana da shekara biyar.
Duk da cewa bai taba zuwa makaranta ba, amma ya samu kyaututtukan karramawa na digirin digirgir masu yawa.
A shekarar 1962 ce aka kai Zuma fursuna saboda yaki da masu nuna wariyar launin fata. Sai ya gudu domin samun mafakar siyasa a 1975, amma ya dawo a shekarar 1990, sannan ya zama Shugaban Kasa a 2009.
Odero ya yi amannar cewa mutane suna son Zuma duk da tsaikon da yake fuskanta wanda ya bayyana da kuskuren da aka samu. "Mutanen Afirka ta Kudu suna kaunar Zuma."
A zaben na bana, Odero ya ce Zuma zai wahalar da ANC da sauran 'yan takarar irin su Jam'iyyar EFF ta Julius Malema.
"Idan jam'iyyun suka kasa cika sharudan da ake bukata domin lashe zaben, za a iya samun hadaka. Wannan zai iya zama nasara ga Zuma."
A Kundin Tsarin Mulkin Afirka ta Kudu, 'yan Majalisar Kasar ne suke zaban Shugaban Kasa.
Shin ya dace Zuma ya shiga takara a wannan lokacin?
Wasu masu sharhi a kan harkokin siyasar kasar suna ganin bai kamata a ce Zuma ya shiga zaben nan ba.
Moses Allan Adam, Shugaban Tanzania-based Friends of East Africa International Council, ya ce har yanzu akwai tuhume-tuhumen rashawa da Zuma ke a wanke shi kafin ya tsaya takara ba.
"Ba na tunanin shi ne ya fi dacewa ya shugabanci Afirka ta Kudu a yanzu," inji Adam.