Kenyan police detain Caroline Nduku Mutisya, whose son Erickson Mutisya was shot and killed in a recent anti-government protest . Hoto / Reuters

Daga Emmanuel Onyango

Damuwar da ake shiga a kasashen Afirka da dama na samun madogara a shafukan sada zumunta inda dubban mutane tsofaffi da matasa ke nuna ƙorafi game da matsalolin da suka daɗe suna ci musu tuwo a ƙwarya.

Nahiyar na da mafi yawan matasa a duniya kuma an yi hasashen nan da shekaru 25 za ta haura mutum biliyan 2.5.

Sai dai kuma, matasan na Afirka ba sa gamsuwa da ayyukan kawo cigaba da gwamnatoci ke yi.

Ta hanyar amfani da dabarun sadarwa na zamani irin wadanda aka yi amfani da su a lokacin zanga-zangar Masar a 2011 da ta #EndSars a 2020 a Nijeriya, matasan Afirka da dama na sake amfani da fasahar sadarwar zamani wajen neman jagoranci mafi kyau.

"Idan jagoranci ba zai iya abin da ya dace ba, to abin da ya dace zai same su," in ji Abdullahi Yalwa, wani mai nazari da ge garin Bauchi a Nijeriya.

A makonni bakwai da suka gabata, kalaman "Dole Ruto ya Tafi", "Ku Bijirewa Kudirin Dokar Kudi" da "Dakatar da Kisan da 'Yan sanda ke yi" sun karaɗe kowane sashe na kasar Kenya, a yayin da matsa da ke zanga-zanga suke nuna ɓacin rai da rashin gamsuwarsu da gwamnatin Shugaba William Ruto.

An fara wannan bore ne a shafukan sada zumunta wanda ƙudirin dokar kudi ta janyo, doka ce da ta tanadi karin kudin haraji da tashin kayan abinci irin su burodi, man girki da kunzugun mata.

Amma sai nan da nan lamarin ya koma zanga-zangar adawa da gwamnati a fadin kasar don nuna yadda jama'a ba sa jin dadin shugabancin.

A shafukan sada zumunta aka kitsa da ingiza zanga-zangar ta Kenya. hoto / AFP

Lamarin ya shaida yadda masu zanga-zangar suka mamaye ginin majalisar dokoki, suka lalata wani bangare na Kotun Koli da hana gudanar da kasuwanci tsawon kwanaki a Nairobi Babban Birnin Kenya.

Mahukunta sun mayar da martani ta hanyar kawo sojoji don taimaka wa 'yan sanda kwantar da hayaniyar.

A kalla mutane 50 aka kashe sakamakon martanin da jami'an tsaro suka mayar, kamar yadda wata kungiyar kare hakkokin dan adam mai goyon bayan gwamnati ta bayyana.

A kasar Uganda mai makotaka da Kenya, matasa sun samu karfin gwiwa da abubuwan da suka faru a Kenya inda su ma suka fara gangami a shafukan sada zumunta suna adawa da munanan cin hanshi da rashawa a gwamnatin Yoweri Museveni.

Amma mahukunta sun yi gargadi kan kwaikwayar zanga-zanga, inda Museveni ya gargadi jama'a kan 'kar a yi wasa da wuta".

Amma duk da haka 'yan Uganda sun fita kan tituna a ranakun Laraba da Alhamis a Babban Birnin Kampala, inda 'yan sanda suka tare su a lokacinda suke kokarin shiga ginin majalisar dokoki.

An kama kusan mutum 100, saboda karya doka da oda da suka yi, kamar yadda rahotannin kafafan yada labaran kasar suka sanar.

‘Zamani iri daya’

"Abubuwan da suka janyo zanga-zanga mabambanta ne. A Kenya game da kudirin dokar kudi da haraji ne, yayinda a Uganda kuma game da satar kudin gwamnati ne.

Amma abin da yake iri guda shi ne shekarun masu zanga-zangar. A dukkan kasashen biyu, duk 'yan zamani daya ne," in ji lauyan kare hakkokin dan adam a Uganda Kliza Eron.

Ya shaida wa TRT Afirka cewa "A Uganda, shfukan sadarwa na zamani sun zama muhimman ginshiƙan zaburar da mutane kuma an samu barazanar katse sadarwar intanet a kasar."

Jami'an tsaron Uganda sun kama wani mai zanga-zanga tare da jan sa a kan titi a Kampala. Hoto / Reuters

Nijeriya, kasar da ta fi girman dimokuradiyya a Afirka, na fuskantar irin wannan zanga-zanga da za a fara a kwanaki masu zuwa.

Kasar na fama da matsin tattalin arziki mafi muni a tsawon shekaru da dama. Matasa ta shafukan X da TikTok na shirya zanga-zanga don tirsasawa gwamnati da ta rage farashin lantarki da man fetur, ta bayar da ilimi kyauta, ta sanya dokar ta ɓaci kan hauhawar farashi, ta kuma bayyana albashin 'yan majalisar dokoki da ma sauran bukatu.

Ana ganin yadda ake ta samun goyon bayan zanga-zangar a fadin kasar, inda ake ta yada kalamai irin su #EndBadGovernanceInNigeria (KawoKarshenShugabanciMaraKyauaNijeriya).

Mahukuntan kasar na ta gargadin masu zanga-zangar inda shugaban 'yan sanda ke cewa "Ba za mu zauna mu nade hannayenmu ba" mu kalli wasu mutane "Su tayar da rikici".

"Matasan da ke zanga-zanga sun zautu saboda yadda aka yi biris da rayuwarsu," in ji Yalwa a yayin zanta wa da TRT Afirka.

Fafutuka a yanar gizo da ta gangara zuwa kan tituna a yanzu ta bayyana irin tasirinta wajen jan hankalin kasashen duniya.

Yadda matasa suka shirya zanga-zangar a kasashen uku sun zama dabarun kwakwayon juna, ba tare da na fahimci cewar wani dan siyas ako wani mutum ne ya shirya su ba.

"Kar ka daimautu da wadannan kalaman da ke cewa wai da ma muna da jagora, ko kuma ya kamata mu samu. Babban abin jin dadi shi ne yadda ba mu da jagora, ba mu da jam'iyyar siyasa, ba mu da wata kabila ko yare.

"Ana cikin mawuyacin hali, in ji Hanifa Adan, daya daga cikin masu shirya zanga-zanga a Kenya a wani rubutu ta shafinta na X.

Masu shiryawar sun kuma kauce wa kafafan yada labarai inda suka mayar da hankali kacokan ga shafukan sada zumunta.

"Batun fasahar kere-kere da shekarun jama'a zare ne da suka hade kasashen Afirka da dama waje guda. Wadannan abubuwa guda biyu ba za a iya biris da su ba a shugabancin Afirka," in ji Kliza.

Shugaban Kasa ya yi amai ya lashe

Yadda ake ganin an samu nasara musamman a Kenya, abu ne da ke karfafa gwiwar matasa masu zanga-zangar.

An tirasasa wa Ruto wajen yin amai ya lashe ta hanyar janye kudirin dokar kudi, ya rusa majalisar zartarwa tare da karba murabus din shugaban 'yan sandan kasar.

Tuni shugaban kasar kenya ya shigar da 'yan adawa cimin kunshin Ministocinsa, sannan ya sanar da shirin rage kashe kudade ciki har da rage kasafin kudin ofisoshin matar shugaban kasa da matar mataimakinsa.

Amma wasu da dama na cewa kokarin wata dabara ce ce da aka saba gani a irin siyasar Kenya.

"Gwagwarmayar ta haifar da da mai ido, wanda ba don ita ba Ruto ba zai yi abinda ya yi ba. Babu tantama game da muhimmancin zanga-zangar duba da irin da tasirin da ta yi a Kenya da Uganda," in ji Kliza.

"Ba za a ci gaba da zanga-zanga har abada ba, amma yiyuwar ta afku zai ci gaba da kasancewa saboda jama'ar ba sa sauya wa kuma fasahar sadarwa na kara habaka."

Masu zanga-zanga a Uganda na kira ga shugabar majalisar dokoki Anita Among wadda ta ce ba ta aikata laifin komai ba. Hoto / Reuters

A gefe guda, gwamnatocin Kenya da Uganda sun dora laifin afkuwar zanga-zangar kan wasu mutane a ke kasashen waje.

"Cewa suke zanga-zangar na da turaku guda biyu. Na farko shi ne daukar nauyi daga kasashen waje da a koyaushe suke lalata harkokin cikin gida na kasashen Afirka shekaru 600 da suka gabata," in shugaba Museveni ta shafin X.

Ta hanyoyi daban-daban, zanga-zangar ta sake wayar da kawunan matasa, rukunin mutanen da ake yi wa kallon ba su da sha'awar batutuwan da suka shafi shugabanci.

Sai dai kuma, Abdullah yelwa na da ra'ayin cewar suna fuskantar kalubalen mayar da gwagwarmayar tasu ta kawo sauyiu na siyasa mai inganci.

Ya lura da cewar "Abu na rashin jin dadi game da ita shi ne yadda masu zanga-zangar ba su da tsariin da zai maye gurbi kuma ya fi wanda aka kora.

Amma kuma mai nazarin ya bayyana cewa ya yi amanna wadannan zanga-zanga za su farkar da shugabanni su san muhummancin matasa a shugabanci da cigaba, ta yadda za su dinga bayar da kulawa ga bukatunsu.

TRT Afrika