An kubutar da dubban rayuka a Uganda karkashin wani shiri da Amurka ta dauki nauyi cikin shekara 20/AA

A shekaru 20 da suka gabata, an kubutar da dubban rayuka da suka hada da na yara kanana a Uganda karkashin wani shiri da Amurka ta dauki nauyi.

A watan Afrilun 2004, mutum na farko a kasar Uganda da ke dauke da cutar kanjamau ya fara karbar maganin kubutar da rayuwa a duniya, a karkashin shirin Amurka da ke samar da tallafi mafi girma don yaki da kwayar cutar AIDS.

Bayan shekaru 20, a yanzu mutumin na da shekaru 53 -- kuma yana rayuwarsa lafiya kalau - godiya ga wannan magani da ke hana mutuwar garkuwar jiki (ART), wanda shiri ne da shugaban Amurka na lokacin, George W. Bush ya samar a 2003, kan Shirin Gaggawa Don Yaki da Kanjamau (PEPFAR).

Daga 2004 zuwa 2022 PEPFAR ya ceci rayukan mutane 600,000 da suke dauke da cutar HIV da kuma hana wasu mutanen 500,000 kamuwa da cutar.

Wannan adadi ya hada da jarirar da iyayensu 230,000 suke dauke da cutar a Uganda, in ji Emilo Dirlikov, masanin cututtuka masu yaduwa da ke aiki tare da Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (CDC) a Uganda.

Yau PEPFAR yana bayar da magungunan cutar kanjamau ga sama da mutum miliyan 20 da suka hada da manyan da yara a Afirka da wajen nahiyar.

A duniya baki daya, PEPFAR ya yi gagarumin aikin maganin cutar kanjamau tare da kubutar da rasa rayuka miliyan 25 a kasashen duniya da dama.

An kiyasta cewa akwai jarirai miliyan 5.5 da aka haifa ba tare da cuta mai karya garkuwar jiki ba, kuma wasu kimanin miliyan daya sun samu kulawar riga-kafin kamuwa da cutar.

Shirin PEPFAR ya samar da cibiyoyin kula da lafiya, wanda kasashen da ake hada kai da su suke amfani da su wajen magance Covid-19, Ebola da sauran cututtuka masu yaduwa.

A Uganda, a watan Maris din 2017 aka fara yaki da HIV/AIDS a lokacin da Shugaban Kasar Yoweri Museveni ya kaddamar da Littafin Kudirin Shugaban Kasa don hanzarta aiwatar da shirin yaki da cutar.

Shirin PEPFAR ya ceci rayukan mutum 600,000 da suke dauke da cutar HIV a Uganda/AA

Ya gabatar da tsare-tsare biyar da suka takaita bayanan hanyoyin da ya kamata a bi don farfado da yaki da cutar HIV/AIDS, da kuma jagorantar kasar wajen samun nasarar kakkabe cutar gaba daya nan da shekarar 2030.

Mary Borgman , jagorar shirin PEPFAR a Uganda, ta bayyana cewa “Tsawon lokaci an samu ingantuwar aikin gano cutar. Za kuma a iya amfani da wannan hanyar wajen magance barkewar wasu cututtukan da kuma gudanar da bincike.”

Bayan shekaru 20, PEPFAR ya dakatar da aiki tare da abokan kasa da kasa inda ya koma samo kudade daga hukumomin da ke Amurka sannan a mika su kai tsaye ga kungoyoyin kasa da suka hada na Uganda, kamar cibiyoyin tura mutane asibitoci.

Dan kasar Uganda wanda ya samu damar kubutar da rayuwarsa ta hanyar PEPFAR, ya kasance mai aikin sa kai a karamin asibitin Entebbe inda aka gano yana dauke da cutar HIV.

Rayuwa ta zama cikakkiya gare shi.

TRT Afrika