Ana ci gaba da samun hauhawar farashi a lokutan shagulgula a Tanzaniya. / Hoto: Getty Images

Daga Gaure Mdee

Azumin bana ya zo wa Musulmai da dama a wani irin yanayi na hauhawar farashin kayayyaki a faɗin nahiyar Afirka, ta yadda hakan ke shafar yanayin buɗa-bakin mutane da dama.

Mutane irin su Mfaume Omari, wani ɗan acaɓa a unguwar Sinza da ke Dar es Salaam babban birnin Tanazaniya, ba sa iya buɗa-baki da komai sai rogo, maimakon kayan abinci mazu ƙara kuzari.

"Hauhawar farashi ya zame mana matsala," ya shaida wa TRT Afrika cikin takaici. "Daga kan man gyaɗa zuwa alkama da busasshen ƴaƴan itace babu abin da yake da sauƙi. A yanzu haka kilogiram ɗin nama ya kai shilling 8,000, kwatankwacin dala uku, Yaya lamarin zai kasance a lokacin Ƙaramar Sallah?"

Alƙaluma sun sake bayyana wannan matsanancin hali da ake ciki. A shekarar 2021, kashi 35 cikin 100 na mutanen da aka tuntuɓa daga Kudancin Afirka da wasu sassan Gabas ta Tsakiya sun bayyana cewa hauhawar farashi ta zamo wata babbar matsala da ƙalubale a tsawon wata gudan da aka yi ana azumi.

Shirin Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya sake fayyace lamarin, inda ya yi nuni da yadda matsalar rashin abinci ta shafi mutum miliyan 349 a faɗin ƙasashe 79 a shekarar 2022. Fiye da mutum miliyan 140 ne suka buƙaci agaji, alƙaluman da har yanz kusan haka suke.

Tsanani

To, hakan ke nuni ga iyalan da suke fatan samun sauki a yayin da ake nisa da azumi ake durfafar Sallar Idi?

Shabani Asmani, wani mazaunin birnin Dar es Salaam, shi ma ya koka a kan hauhawar farashin da ke ƙara munana yayin da bikin sallah ke ƙaratowa.

"Yanayin tattalin arziki ya zama mai tsanani ga mutane da dama. Farashin kayan abinci sun hauhawa, kuma ga alama abin zai sake ta'azzara kafin Sallah Ƙarama," kamar yadda Asmani ya shaida wa TRT Afrika.

Shi ma wani ɗan kasuwa Ali Maliza ya ce a duk lokacin da mafi yawan al'umma ba sa iya sayen abubuwa mafiya muhimmanci, to hakan yana yin mummunan tasiri a kan tattalin arziki.

Ramadan na sanya tausayi da jinƙai a tsakanin mutane. Hoto: Others

"Idan kuwa harkokin kasuwanci suka yi ƙasa, babu wanda zai tsira. Amma a wannan karon muna fatan a samu sauƙi zuwa lokacin Sallah."

A yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka tuni hauhawar farashi ta jefa mafi yawan al'umma cikin ƙunci.

Tun lokacin annobar cutar korona, gwamnatoci suka dinga samar da tallafin rage raɗaɗi da rage haraji don sauƙaƙa wa al'umma. Sai dai wadannan matakan sun samar da sauƙi na ɗan lokaci ne kawai.

Yayin da watan Ramadan ke ta tafiya, karamcin al'ummomi da kungiyoyin agaji yana taimakawa sosai wajen kawo sauƙi a irin waɗdannan lokutan wahala.

Salum Said, wanda ke zaune tare da iyalansa a birnin Morogoro na kasar Tanzaniya, ya bayyana yadda lamarin ya yi ƙamari. "Bayan yin sahur, ba ma cin abinci sai bayan buda-baki, kuma wannan abincin shi za mu ƙuƙuta mu rage har washegari, saboda yanayin tattalin arziki, ba za mu iya cin abinci sau biyu ko uku ba," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Ƙarfin imani

A cikin ƙalubalen matsi na kuɗi, tasirin Ramadan yana ci gaba da haɓaka tausayi da jinƙan juna a tsakanin al'umma.

Hauhawar farashin ba ta sa miliyoyin iyalai a Afirka sun ji ko gezau ba kan imani da miƙa wuyansu a watan Ramadan.

Kamar yadda Suleiman Omari mazaunin Dar es Salaam ke cewa, ƙarfi shi ne samun juriya a wajen bautar Ubangiji. A ƙarshe mutane kan yi nasara su zama jajirtattu a cikin kowane irin ƙalubale.

"Abin da yake faruwa a fannin tattalin arziki ba huruminmu ba ne. Amma a matsayinmu na Musulmai, dole ne mu yi azumi kuma Allah zai yi mana jagora a cikin wannan yanayi," ya ce.

"An yi la'akari da cewa farashin zai kara tashi yayin da muke shirin Idi, duk da haka sanya sabbin tufafi a ranar bikin sunna ce a gare mu, kuma ko ta yaya za mu yi."

Salum na fatan idan an shiga goma ta biyu na watan azumin, za a samu sauƙin abubuwa da dama.

"Yawanci farashi kan yi tashin gwauron zabi ne a farkon azumin amma daga baya abubuwa kan lafa. Ana tafe a hankali sai abubuwa su fara sauƙi, kuma muna fatan a wannan karon ma hakan ce za ta kasance," in ji shi.

TRT Afrika