Kasar Zambiya na cikin mawuyacin hali na barkewar cutar kwalara. Photo: Others

Daga Charles Mgbolu

Cutar kwalara ta iya yaƙin sunƙuru wajen yin kisan gilla a ƙasashen Afirka da dama.

Ana kamuwa da kwalara ne ta hanyar cin gurɓataccen abinci ko ruwa da ke ɗauke da ƙwayoyin cuta.

"Ƙwayar cutar da ke jawo kwalara na iya jure tsananin zafin ciki ta yadda takan shiga hanji ta hargitsa zaman lafiyarsa ta wajen haddasa ruɗewar ciki mai jawo amai da gudawa," kamar yadda wani ƙwararren likita a brnin Legas na Nijeriya, Dakta Adedoyin Ogunyemi ya shaida wa TRT Afrika.

Zambia, ƙasa mai yawan al'umma miliyan 20, a yanzu haka tana fama da ɓrkewar annobar kwalara.

Tun watan Oktoban bara, hukumomi suka rawaito cewa fiye da mutum 9,000 ne suka kamu da cutar, sannan mutum 370 suka mutu.

A shekarar 2023, fiye da mutum 48,280 ne ake zargin sun kamu da cutar a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, inda 421 suka mutu, kamar yadda alƙaluman Hukumar Lafiya ta Duniya WHO suka nuna.

An yi amannar ita ce annoba mafi muni da ta barke a ƙasar tun shekarar 2017.

Kashi 62 cikin 100 na waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar a undumar Kivu suke, saboda yawan cunkoson jama'a da rashin samun tsaftataccen ruwan sha da kuma rashin tsaftar makewayi.

Wuraren da abin ya fi ƙamari su ne sansanonin ƴan gudun hijira a yankin babban birnin lardin, Goma.

Alƙaluma masu ɗaga hankali

WHO ta ce alƙaluman farko-farko sun nuna yadda aka samu ƙaruwa mai ɗaga hankali ta masu kamuwa da cutar kwalara a 2023, inda mutum 667,000 suka kamu sai kuma mutum 4,000 suka mutu a fadin duniya.

A shekarar 2021, Cibiyar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Nijeriya ta rawaito cewa mutum 111,062 ne suka kamu da kwalara, sannan mutum 3,604 suka mutu a fadin ƙasar.

Ƙasashe irin su Malawi da Afirka ta Kudu da Zimbabwe da Kenya da Burundi da Habasha ma suna ta fama da annobar.

Ma'aikatan kiwon lafiya na sa kai na Zambia suna taimakawa da allurar rigakafin kwalara. Photo: WHO. Photo WHO

A watan Agustan 2023 Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya ce yawan yaɗuwar cutar kwalara a ƙasashen Afirka da dama "ba annoba ba ce kawai, wani batu ne na gaggawa da ke shafar yara."

Jami'an lafiya kamar irin su Dakta Adedoyin Ogunyemi sun yi gargaɗi cewa ba za a kawo ƙarshen mummunar annobar ba idan har ba a magance abubuwan da ke jawo ta ba.

"Idan dai har za a ci gaba da amfani da gurɓataccen ruwan sha da rashin tsaftar muhalli da tasirin sauyin yanayi, da yawan ambaliyar ruwa, to lallai kuwa wannan mummunar ƙwayar cuta za ta ci gaba da yaɗuwa," a cewar Ogunyemi.

A ranar Talata 16 ga watan Janairu, Zambiya ta ƙaddamar da wani gagarumin kamfe na yin rigakafi a cikin babban birninta Lusaka, wanda yake yawan fama da mummunar annobar kwalara.

An fara kamfe din ne da ba da alluran rigakafi miliyan 1.4 a ranar Litinin daga WHO, wacce ta warewa ƙasar alluran rigakafin miliyan 1.7.

A lokacin da take ƙaddamar da gangamin a yankin George Township na birnin Lusaka, Ministar Lafiya Sylvia Masebo ta ce sau ɗaya za a yi wa mutane allurar maimakon sau biyu kamar yadda aka tsara, saboda ba za su isa a yi wa kowa da kowa ba.

"Sannan kuma ma'aikatan lafiyarmu ne za su yi wa mutane alluran, waɗanda su ne a gaba-gaba wajen yaƙi da cutar kwalara," in ji Masebo.

Shugaban Zambiya Hakainde Hichilema ya bukaci 'yan kasar da su ci gaba da yin taka tsantsan daidai da ƙa'idojin kiwon lafiya saboda ɓarkewar cutar "har yanzu yaɗuwa."

Dangerous short-cut

Jami'an kiwon lafiya sun yi gargadin cewa allurar rigakafi kadai ba ta isa ba. Suna kira da a ƙara himma wajen magance koma bayan muhalli da ke ƙarfafa yaɗuwar ƙwayoyin cutar tun da farko.

Dokta Ogunyemi ya yarda cewa dole ne a magance tushen cutar mai saurin kisa.

''Muna bukatar tsarin da ya shafi bangarori da yawa. Ma’aikatun albarkatun ruwa da raya karkara, da tsare-tsare na birane duk abokan aikinsu ne wajen tabbatar da samar da ababen more rayuwa ga jama’a.”

WHO ta yi gargadin sake bullar cutar kwalara a duniya ya kasance matakin gaggawa na mataki na 3, matakin cikin gida mafi girma na gaggawar lafiya da ke bukatar cikakken martani a duniya.

TRT Afrika