Daga Sylvia Chebet
Ƙiba ba wai mutum ya zama ƙatoto ko ya kasa saka kaya ƙanana ba ne. A yanzu ta zama babbar matsalar lafiya ta duniya da ke ta'azzara amma kuma ba a ba ta kulawa ta musamman.
Wani sabon nazari da mujallar lafiya ta The Lancet ta gudanar ya ce ya zuwa 2022, akwai mutane sama da biliyan guda da ke fama da ƙiba a duniya.
Bayanan jama'a da aka samu daga ƙasashe 200 ko yankuna a shekara ukun da suka gabata sun nuna cewa kashi 43 na manya da ke duniya na da ƙibar da ta wuce ƙima.
To me ya sanya mutane ke yin ƙiba?
Dr. Francesco Branca, wanda aka yi rubutun da shi kuma darakta a Sashen abinci mai gina jiki na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ya ce, amsar wani buɗaɗɗen sirri ne.
"Duniya ta sauya sosai a tsarin cimaka. Abincin da ke da maiƙo da sukari ko aka sarrafa su sosai ne ake ci a ko'ina," Dr Branca ya shaida wa TRT Afirka. "Suna da araha, ana samun su dare da rana sannan ana tallata su sosai, musamman ga yara."
Kayan ƙwalam da maƙulashe, rashin isashen barci, yawan gajiya da zama a waje guda ne ke ta'azzara yawan masu ƙiba a duniya.
Na kama su tun suna matasa
Ƙwararru sun lura da cewa ƙiba na samun mutane ne tun suna da ƙarancin shekaru.
Rahoton Lancet ya bayyana cewa tun 1990, yawan ƙiba a duniya ya ninka sau huɗu a tsakanin yara ƙanana da matasa.
"Samarwa da amfani da abincin yara na ta'azzara matsalar ƙiba. Mun ga cewa yaran da ake shayar da su kawai ba sa yin ƙiba mai hatsari," in ji Dr. Branca.
Hujjoji na kimiyya sun bayyana alaƙar da ke tsakanin nonon uwa da samun gangar jiki mai lafiya.
"Su (Jarirai da ake shayarwa) na iya zama mafi zama a kyakkyawan yanayin sawa jikinsu da abubuwan da suke bukata . Abin takaici kuma, amfani da kayan abinci da ke da sukari a lokacin yarinta na janyo ƙiba sosai," in ji jami'an WHO.
Matsalar ƙiba a Afirka
Binciken Lancet ya yi bayani kan sauyi babba daga rama zuwa ƙibar da ta wuce misali a ƙasashe da dama musamman ma na Afirka. A yanzu ƙasashen na da yawaita masu ƙiba sama da ƙasashen da suka ci-gaba.
"Ƙiba matsala ce ga ƙasashe matalauta da masu tasowa da ke fuskantar sauyin tsarin rayuwa. Samuwar masu ƙiba da yawa babban ƙalubale ne ga Afirka da dama tana fama da matsalolin kula da lafiya," in ji Dr Branca.
"Mutane da ke rayuwa da ƙiba na iya fuskantar matsalar samun aikin yi. Mun yi hasashen cewa za a samu raguwar kashi uku na kuɗaɗen-shigar ƙasashen sakamakon larurar ƙiba."
A nahiyar Afirka, Masar ce ke da mafi yawan masu ƙiba a tsakanin maza da mata. Binciken ya nuna cewa kashi 59 na matan Masar na da ƙiba, ita ce ƙasa ta tara a duniya wajen yawan masu ƙiba. Kusan kashi 32 na mazan ƙasar na da lalurar ƙiba, waɗanda su ne na 33 a duniya.
"Mun ga hanzartuwar masu ƙiba a arewaci da kudanin Afirka. A Yammacin Afirka ma an bayyana ta a matsayin babbar matsala, musamman a ƙasashe irin su Nijeriya," in ji Dr Branca.
Amma wasu ƙasashen musamman na Kahon Afirka ba sa fama da wannan matsala.
Cututtukan da ƙiba ke janyowa
Ƙibar da ta wuce misali na janyo mutuwar mutane miliyan biyar kowacce shekara a duniya. Munanan cututtuka irin su ciwon sukari, ciwon zuciya, tare da wasu nau'uka na ciwon daji na da alaƙa da ƙiba.
Binciken Lancet ya yi ƙarin haske game da muhimmancin kare kai da magance kiba tun ana yarinta da zuwa lokacin manyantaka.
Likitoci na bayyana cewa an fahimci dalilan da suke janyowa da kuma kare kai daga ciwon sukari, amma ɗabbaka su ne yake da wahala a matakin gwamnati da ɗaiɗaikun mutane.
"Abu ne da za mu iya farawa yau, mu tabbatar da abincinmu na da kyau kuma da gina jiki. A dinga cin hatsi zalla, kayan marmari da kayan miya. A rage amfani da sukari da kayan zaƙi musamman lemuka. Mu dinga shan ruwa. Shi ne abu da muke buƙata," Dr Branca ya faɗa wa TRT Afirka.
"Ka zama mai kazar-kazar, ka dinga tattaki maimakon hawa mota, ko idan za ku waje marar nisa ne ba dole ne sai ka dinga zuwa wajen motsa jiki ba, amma za ka iya dinga yin motsi, a je aiki a ƙasa sannan ka dinga wasa da yaranka."
A wajen babban taron lafiya na 2022, ƙasashe mahalarta sun amince da Shirin WHO na yaƙi da ƙiba, wanda zai taimaka wajen yaƙi da cutar nan da 2030.
"Ana buƙatar ayyukan gwamnatoci da al'ummu don kakkaɓe matsalar ƙiba da yawa tare da komawa kan turba... Abu mafi muhimmanci, aikin na buƙatar haɗin kai ga ɓangaren da ke zaman kansa, wanda na da muhimmanci ga tasirin kayan da suke sayarwa," in ji Darakta Janar na WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus.
A matakin gwamnati, ya ce ya zama dole ƙasashe su tabbatar cewa tsarin kula da lafiya ya sanya rigakafin ƙiba a ayyukan da yake yi.
Gano alamomin ƙiba
Bin diddigin yanayin jiki na BMI, wani tsari ne da ake amfani da girma da tsayi na mutum, kuma hanya ce ta kimiyya mafi kyau don kula da sanya idanu kan ƙibar da mutum ke yi.
A lokaci da BMI din mutum ya haura 25, alamu ne da ke nuna yana da ƙibar da ta wuce ƙima. A yayin da BM yake kusa da 30, to an kai matakin tsoro kan ƙiba a mutuwa.
Wata hanya mai kyau ta kula da ƙibar mutum ita ce duba yanayin da ƙugu ke ciki. An bayyana 80cm a matsayin kaurin ƙugun da ya kamata ga mata, 90cm ga maza. Idan aka samu sama da haka to lallai ana da ƙibar da ba a so.
Dr Branca. Dr Branca ya kuma ce "Wannan na nufin man da muke tarawa zai zama a wajen cikinmu. Mai a ciki na sanya hatsarin kamuwa da ciwon sukari na rukuni na biyu wato type 2."
Ya bayar da shawarar neman magani ga waɗanda suke fama da ƙiba.
"Kar su ji kunya," jami'in na WHO ya faɗa wa TRT Afirka. "Kar kuma wasu su ɗora musu laifi. Likita zai iya bayar da shawarwari da kulawar da suka dace, sannan ya bayar da shawarar abincin da za a dinga ci, tare da nau'in motsa jinin da ya dace don rage ƙiba."