Kotun Kasa da Kasa da ake kuma kira Kotun Duniya na birnin Hague a kasar Netherlands. Hoto: Reuters

Daga Sylvia Chebet

An soma shari'a tsakanin Afirka ta Kudu da Isra'ila, inda tawagogin manyan lauyoyi suka tunkari Kotun Kasa da Kasa da ke birnin Hague.

A takardun shigar da kara masu shafi 84, Afirka ta Kudu ta zargi Isra'ila da aikata kisan kare-dangi kan Falasdinawa a Gaza, tana gabatar da kararta da gamsassun bayanai kan kashe-kashen da Isra'ila ke yi tun bayan harin da Hamas ta kai musu a ranar 7 ga Oktoba.

Karar ta zayyana yadda Isra'ila ke kashe Falasdinawa da rusa gine-ginensu, sannan da yadda ta mamaye Gaza baki daya tare da yanke musu duk wasu kayan bukatu na rayuwa da suka zama wajibi ciki har da ruwa, abinci, man fetur da magunguna.

Afirka ta Kudu na neman kotun ta tilasta wa Isra'ila dakatar da hare-haren da take kaiwa inda ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa sama da 23,000 da suka hada da kananan yara kusan 10,000.

Dukkan bangarorin biyu za su gabatar da bayaninsu a gaban kotun ta Hague a cikin kwanaki biyu; Alhamis da Juma'a.

Ana sa ran alkalan kotu 17, da wasu biyu na jiran ko-ta-kwana za su saurari bayanan Afirka ta Kudu na kai karar Isra'ila a Kotun ta Kasa da Kasa.

Kwararre kan shari'a Nabil Orina ya shaida wa TRT Afirka cewa "Saboda batun babban ne a fagen siyasa, za a kalli kowanne bangare. Ana bukatar alkalai tara don tabbatar da hukunci."

To su waye lauyoyin da Afirka ta Kudu da Isra'ila suka zaba don fafatawa a kotun?

Tawagar lauyoyin Afirka ta Kudu

John Dugard, tsohon wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan kare hakkokin dan'adam a yankunan Falasdinawa da aka mamaye ne jagoran lauyoyin Afirka ta Kudu.

Ana yi wa Dugard kallon daya daga cikin kwararrun lauyoyin Afirka ta Kudu da ya shahara kan dokokin kasa da kasa, kuma yana da sanayya kan salon shari'a a Kotun Kasa da Kasa, saboda ya taba zama alkalin wucin-gadi a kotun a 2008.

Alkalai a Kotun Kasa da Kasa sun saurari bukatar da Afirka ta Kudu ta mika don daukar matakan gaggawa, kotun ta umarci isra'ila ta dakatar da kai hare-hare kan Gaza. Hoto: Reuters

Dugar ya yi kakkausan suka kan aika-aikar da isra'ila ke yi, inda ya ce "Firaminista Benjamin Netanyahu, abokansa na yaki, da wasu mambobin sojin Isra'ila ne ke da alhakin kisan kare-dangin da ake yi, suna aikata laifukan yaki, laifin da zai iya zama na kisan kiyashi."

Wasu daga tawagar lauyoyin na Afirka ta Kudu sun hada da babban lauya Adila Hassam, Tembeka Ngcukaitobi, lauyan Kungiyar Lauyoyi ta Johannesburg, da lauyan kasa da kasa Max Du Plessis.

Tawagar lauyoyin ta kuma kunshi Tshidido Ramogale, Sarah Pudifin-Jones da Lerato Zikalala, yayin da lauyoyin Ailan Blinne Ni Ghralaigh da lauyan Ingila Vaughan Lowe suke zaman matsayin lauyoyi daga wajen Afirka ta Kudu.

Tawagar da ke kare Isra'ila

Isra'ila ta zabi gabatar da lauya dan kasar Birtaniya Malcolm Shaw don wakiltar ta a Kotun kasa da Kasa.

Ana yi wa Shaw kallon daya daga kwararrun lauyoyi a duniya da suka san dokokin kasa da kasa, kuma ya taba bayyana a gaban Kotun ta Kasa da Kasa.

A yayin gabatar da ayyukansa, Shaw "ya yi suna a kasashen duniya wajen bayar da shawawarin warware takaddamar kan iyakoki; dokokin teku; rigar kariya ga kasashe; amincewa da kasashe da gwamnatoci na waje, hakkokin dan'adam, shiga tsakani a matakin kasa da kasa da kungiyoyin kasa da kasa," kamar yadda aka gani a bayanai game da shi a Kotun Essex.

Ya kuma bayar da shawara ga gwamnatoci daban-daban da suka hada da na Ingila, Ukraine da Sabiya.

Baya da Kotun Kasa da Kasa, Shaw ya taba zama lauyan shari'o'i a Kotun Kare Hakkokin Dan Adam ta Turai, Kotun Turai da sauran manyan kotuna na duniya.

An bayyana cewa Shaw na daya daga lauyoyi hudu da za su wakilci Isra'ila a Kotun Kasa da Kasa, amma ba a bayyana sunaye da bayanan sauran lauyoyin ba.

Alkalan Kotun

Kotun Kasa da Kasa na da alkalai 15 da aka zaba a Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Tsaro don su yi aiki na tsawon shekaru tara.

Alkalai da magatakardar Kotun Kasa da Kasa. Hoto: ICJ

A karkashin dokokin Kotun Kasa da Kasa, idan wata kasa ta shigar da kara kuma ya kasance babu dan kasarta a alkalan kotun, to za ta nada alkali na wucin gadi, shi ne aka samu guda biyu a yanzu, daga bangaren Afirka ta Kudu da Isra'ila.

A kan wannan, Afirka ta Kudu ta nada Dikgang Moseneke, tsohon mataimakin alkalin alkalan kasar wanda ya yi suna da kwarewa a Afirka ta Kudu da kasashen waje.

A nata bangare, Isra'ila ta nada Aharon Barak, tsohon Shugaban Kotun Kolin kasar.

Barak ya bayyana goyon baya ga yakin da isra'ila ke yi a Gaza, yana mai cewa hare-haren soji ba su take hakkokin dan'adam ba, kamar yadda jaridar The Times ta Isra'ila bayyana.

Ya kuma dinga kare matakin da Isra'ila ta dauka na gina katangar raba tsakani ta bangaren Yammacin Gabar Kogin Jordan.

Sauran alkalai 15 na kotun sun fito daga kasashe daban-daban. Joan Donoghue daga Amurka ne shugaban kotun, sai Kirill Gevorgian daga Rasha a matsayin mataimaki.

Alkalan kotun da suka fito daga Afirka su ne Abdulqawi Yusuf daga Somalia, Julia Sebutinde daga Uganda sai Mohamed Bennouna daga Morocco.

Sauran alkalan sun hada da dan kasar China Xue Hangin, Peter Tomka daga Slovakia, Ronny Abraham daga Faransa, Leonardo Nemer Caldeira Brant daga Barazil, Dalveer Bhandari daga Indiya, Patrick Lipton Robinson daga Jamaica, Hilary Charlesworth daga Australia, Nawaf Salam daga Labanan, Yuji Iwasawa daga Japan da kuma Georg Nolte daga Jamus.

Phillipe Gautier daga Beljiyom ne magatakardar kotun.

TRT Afrika