Botswana da ke tsakanin Zimbabwe da Namibiya tana da adadin giwaye mafi yawa a duniya inda yawansu ya kai 130,000, amma ba ta ɗauki shawarar kashe giwayenta don ciyar da al'ummarta ba. / Hoto: AFP  

Daga Sylvia Chebet

Babu wani abu da za a iya kwatanta haɗin kai tsakanin kowane nau'in halitta kamar samun abinci, duk wani rashin daidaito a wannan tsari ka iya haifar da rikici.

Yayin da ƙasar Namibiya ke fama da tsananin ƙarancin abinci sakamakon matsalar fari da ta lalacewar amfanin gona a mafi yawan yankunan ƙasar da ke kudancin Afirka, lamarin ya janyo shakku kan ka'idojin tsarin abinci a kasar.

Kusan rabin al'ummarta miliyan 3.03 da suka rage ba su da abinci, dole ne gwamnati ta ɗauki matakai masu tsauri kamar yanka namun daji don ciyar da iyalai masu fama da yunwa.

"Idan ba mu ɗauki wannan mataki na kashe dabbobin ba, za mu yi asarar rayuka da dama sakamakon matsalar fari da muke fuskanta," kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar kula da muhalli ta Namibia Romeo Muyunda ya shaida wa TRT Afrika.

''Za a samu karancin ciyayi da ruwan sha ga dabbobi da mutane. Wannan yanayin zai ƙara haifar da rikici tsakanin mutane da dabbobi, kuma idan aka samu irin waɗannan rikice-rikice, a ƙarshe dabbobi ne ake yawan asara.''

An soma yanka namun dajin, kuma ga yawancin iyalai da ke fama da yunwa, samun yanka ɗaya na nama na nufin kullum sai sun nemi abin da za su sa a bikinsu.

Masu rajin kare hakkin dabbobi sun yi gargadin cewa kashe wasu giwaye na iya lalata garken dabbobin baki ɗaya, /Hoto: Reuters

Makwabciyar Zimbabwe ita ma ta bi sahu, inda ta ɗauki matakin yanka giwaye 200,000 domin ciyar da mutanen da matsalar fari mafi muni da aka taba fuskanta a tsawon shekaru da dama ta shafa.

Gargaɗin masu kare dabbobi

Kamar yadda aka yi hasashe, shirin agaji na matsalar fari na Namibiya ya haifar da suka mai ƙarfi daga masu rajin kare hakkin dabbobi, waɗanda ke kallon matakin a matsayin na gajeran zango kana mara ɗorewa.

Masanin ilimin kimiyya Julian (ba ainihin sunansa ba ne) ya yi ƙorafin cewa shirin ba zai samar da mafita ba ga matsalar ƙarancin abincin da ake fama da shi. "A bayyane yake cewa za a gaggauta raba naman, kuma za a yi saurin cinyewa," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Matsalar ita ce: me za a yi a gaba?"

Ƙungiyar ƙare hakkin dabbobi ta PETA ta aika wata wasika ga Firaminista Saara Kuugongelwa- Amadhila, inda ta bayyana dalilan da suka sa matakin ''ya zama ba kawai iya na rashin tausayi ba har da rashin hangen nesa''.

''Matakin, ba zai yi wani tasiri na tsawon lokaci a waɗannan matsaloli masu sarƙaƙiya da ake da su a ƙasa ba,'' in ji babban mataimakin shugaban PETA Jason Baker a cikin wasiƙar, wadda aka wallafa ta shafin intanet ɗin ƙungiyar.

PETA ta bayyana damuwa kan cewa kashe dabbobi na iya haifar da katsalandan da rashin daidaituwa a yanayin muhalli, lamarin da ya sanya wasu masu kare hakkin muhalli barazanar ɗaukar mataki na shari'a.

"Kashe ko da wasu giwaye 'yan kadan ne na iya lalata garkensu baki ɗaya, wanda hakan na iya haifar da karuwar mace-mace a tsakanin sauran da suka tsira tare da kara rikice-rikicen mutane da dabbobi'' kamar yadda Baker ya yi wa Firaministan kasheɗi a cikin wasikar.

Wata ƙungiyar masu rajin kare hakkin dabbobi ta Afirka, ita ma ta fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa, inda ta bayyana damuwarsu game da kisan-ƙare dangi na dabbobi da ake yi a Namibiya, tana mai cewa yin hakan ya kafa tarihi na bai wa gwamnatoci dama '' inda za suna fakewa da amfani da namun daji da wauraren ajiye dabbobin ƙarkashin buƙatu na jinƙai.''

Sanarwar ta aza ayar tambayoyi, kan ko an gudanar da bincike kan tasirin matakin kan muhalli kafin a zartar da shi.

Tashin hankali a dazuka

Gwamnatin Namibiya ta ce duk wani nau'in namun daji da aka ware don yanka su dabbobi ne da al'ummarta za su iya ci. /Hoto: AFP

Gwamnati ta ware wasu ƙwararrun mafarauta don gudanar aikin kashe dabbobin.

A karon farko dai ma'aikatar muhalli ta ba da izinin kashe dorinar ruwa guda 30 da ɓaunaye 60 da barewa 50 giwaye 83 da kuma jakin dawa guda 300.

Mafi yawan waɗannan dabbobi sun fito ne daga wuraren ajiye dabbobi na ƙasar da aka samar musu kariya.

''Kan batun sukar da gwamnatin Namibiya ke sha game da matakinta na kai ɗauki, akwai yiwuwar waɗannan ƙungiyoyi masu zaman kansu daga Yammacin Duniya ba su fahimci tasananin halin da ake ciki ba ne a ƙasar'' in ji Muyunda.

“Daga ƙarshe dai, Namibiya kasa ce mai cin gashin kanta. Kuma muna yanke shawararmu ne bisa ga abin da muke ganin ya fi dacewa ga al'ummarmu, kuma waɗanda ke sukarmu - a zahiri, mafi yawa - sun riga sun shafe namun daji da suke da su."

Sai dai Julian na fargabar wannan mataki na iya haifar da karin matsaloli ga al'ummar Namibiya.

"Matakin na iya dan rage matsalar yunwar da mutane suke fama da ita na wani ɗan lokaci amma zai haifar da matsalar yawan dogaro. Mutane za suna sa ran gwamnati za ta ci gaba da samar musu da abinci ko da bayan an wuce yanayin farin," in ji shi.

To, wacce hanya ce ta fi ɗacewa a bi idan aka yi la'akari da illar yanayi na fari da aka fada ciki?

Julian na son gwamnati ta fara tunanin ɓullo da matakan da za su rage radaɗin yanayin na dogon lokaci tare da samar wa mutane dabarun dogaro da kansu ta yadda al'ummar ƙasar za su iya ci gaba da ciyar kansu, a lokacin matsalar fari irin wannan da bayansa.

Namibiya ta ayyana ɗokar ta baci a watan Mayu sakamakon farin da ya addabi ƙasashen kudancin Afirka.

Yanayin ranin dai na daga cikin iftila'in sauyin yanayi da duniya za ta ƙara ɗaura ɗamarar shawo kansa, ya haifar da raguwar albarkatun noman hatsi da kashi 53 cikin ɗari, kana an samu raguwar ruwan dam da kashi 70 cikin 100 idan aka kwatanta da bara.

Ƙungiyar raya kasashen kudancin Afirka ta yi kiyasin cewa kimanin mutane miliyan 68, wato kashi 17% na al'ummar yankin ne suke bukatar agaji.

Kungiyar ta nemi taimakon jinƙai na dalar Amurka biliyan 5.5 don tallafa wa waɗanda matsalar fari ta shafa.

TRT Afrika