Kungiyar MSF ta ba da rahoton mutuwar jarirai 48 sakamakon kamuwa da cutar sepsis a asibitoci biyu a Kudancin Darfur tsakanin Janairu da Yuni na wannan shekara / Hotuna: Getty Images

Daga Sylvia Chebet

Kukan jarirai na ci gaba da karaɗe wani asibitin koyarwa na Nyala da ke yankin Darfur ta Sudan ta Kudu yayin da mutane da ma'aikatan jinya ke kai komo da fuskoki cike da damuwa.

A yayin da ake cikin wannan yanayi na fargaba a sahen yara na asibitin, akwai wata jaririya ɗaya ta yi shiru tamkawar tana jikin mahaifiyarta ne tana jin ɗumin jikinta. Sai dai tashin hankalin da ke cikin idanun uwar ya fi gaban hakan.

Ya bayyana cewa jaririyar na fama ne da mummunar cutar sepsis - cutar da ana iya magance ta da a ce tsarin kula da lafiyar Sudan bai ruguje ba sakamakon yaƙin da ake fama da shi.

"A cikin yanayi na yaƙi, babu sojojin da ba su ji rauni ba," in ji wani marubuci ɗan Arjantina José Narosky.

Rahoto ne da aka kwatanta da wahalhalun da jariran da aka haifa cikin rikice-rikice suka rutsa da su ta hanyar kamuwa da cutar sepsis, wadda take barazana ga rayuwarsu, inda tsarin garkuwar jiki yake rushewa, take kuma lalata sassan jiki.

Sassan kula da kananan yara na asibitocin Nyala da Kas Rural kadai sun ba da rahoton mutuwar jarirai 48 sakamakon kamuwa da cutar sepsis tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na wannan shekara, a cewar rahoton kungiyar agaji ta Médecins Sans Frontières (MSF).

Rahoton mai suna 'Driven to Oblivion: The Toll of Conflict and Neglect on the Health of Mothers and Children in South Darfur,' ya kuma ambaci mutuwar mata masu juna biyu 46 a cikin asibitocin biyu a tsakanin watan Janairu zuwa Agusta.

Dr Gillian Burkhardt, manajan ayyukan kula da lafiyar tsarin lafiyar haihuwa na MSF ya ce "Wannan rikici ne da ban taba ganin irin sa ba a tsawon shekarun aikina."

Lalacewar tsarin lafiya

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da rahoton mutuwar mutum miliyan 11 da ke da nasaba da cutar sepsis a duk duniya a cikin 2020, wanda ke nuna girman wannan ƙalubalen na lafiya.

Amma ana iya kauce wa kamuwa da cutar sepsis ta hanyar magance cututtuka a kan lokaci da kuma kiyaye muhallin da ba su da kyau, duka biyun a halin yanzu yanayin jin daɗi ne wanda iyaye masu ciki a Sudan za su iya fatan samu yayin da yaƙin da ake yi tsakanin sojojin da dakarun RSF ke ci gaba.

Ba tare da samun muhimman abubuwa kamar sabulu da tsaftatattun tabarmai da kayan aiki, cututtuka sun yi yawa.

Magungunan kashe ƙwayoyin cutar ba su da yawa, kuma iyaye mata da jariran da ke tsananin fama da cutar suna yawan zuwa asibiti amma ba sa samun magungunan da suke bukata cikin gaggawa.

"Ba su da inda za su koma," in ji Dr Burkhardt. “Sabbin jarirai da mata masu juna biyu, da kuma sabbin masu jego suna mutuwa sosai. Komai ya lalace”.

Cibiyoyin kiwon lafiya da ke aiki a Kudancin Darfur ba su da yawa kuma suna da nisa. Wannan, haɗe da farashin sufuri mai tsada, yana nufin mata da yawa ba sa samun magani har sai lokaci ya ƙure.

Maria Fix, shugabar kungiyar likitoci ta MSF ta ce "Wata mara lafiya mai juna biyu daga ƙauye ta jira kwanaki biyu don karbar kudin da ake bukata don samun kulawa. A lokacin da ta je cibiyar lafiya, ba su da magunguna, don haka ta koma gida," in ji Maria Fix, shugabar kungiyar likitoci ta MSF a Kudancin Darfur.

"Bayan kwana uku, yanayinta ya ƙara tabarbarewa, kuma sai da ta jira awanni biyar don samun abin hawa. A sume aka kawo mana ita."

Matar da jaririn da ke cikinta za su zama wani bangare na ƙididdiga don bayyana Sudan a matsayin wuri mafi hatsari a duniya wajen haihuwa saboda yaƙin.

"Ta mutu sakamakon cura wacce za a iya rigakafinta," in ji Maria.

A cewar rahoton na MSF, kashi 78% na mace-macen mata masu juna biyu suna faruwa a cikin sa'o'i 24 na farko na kwantar da su a asibiti.

"Na ga mutane da yawa sun mutu a cikin sa'a ta farko saboda sun riga sun shiga cikin wani mawuyacin hali a lokacin da suka isa wurinmu," Dr Burkhardt ya shaida wa TRT Afrika.

Mace-macen da aka rubuta a asibitocin Nyala da Kas tsakanin Janairu da Agusta sun ƙunshi fiye da kashi 7% na mace-macen mata masu juna biyu a duk cibiyoyin MSF a duniya a cikin 2023.

Ƙungiyoyin da ke gaba da juna suna ƙara tsananta ƙarancin wadatar kayayyaki, waɗanda ke ci gaba da toshewa ko hana samun agajin ceton rai. /Hoto: MSF

Rushewar tsarin lafiya

Dr Muddater Ahmed Yahya Basher, wanda ya yi ninkaya ta ruwa don isa asibiti don yi wa wata mace tiyatar haihuwa, wanda labarinsa ya yadu kwanan nan, ya ce tsarin kiwon lafiya a fadin Sudan ya durƙushe.

Lamarin dai bai bambanta ba a birnin Tokar da ke kusa da Tekun Maliya a arewa maso gabashin Sudan, inda likitan yake.

"Muna rayuwa ne a cikin lokaci mafi wahala, kuma ina fatan dukkan kasashe sun goyi bayan Sudan da al'ummarta. Muna bukatar mu dakatar da yakin, mu maido da zaman lafiya da mayar da mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa gidajensu," Dr Basher ya shaida wa TRT Afrika.

Dubban yara na gab da mutuwa saboda yunwa.

A watan Agusta, an yi wa yara 30,000 'yan ƙasa da shekaru biyu gwajin rashin abinci mai gina jiki a Kudancin Darfur. Daga cikin waɗannan, an gano kashi 32.5% suna fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki, fiye da matakin gaggawa na WHO na kashi 15%.

Rikicin na haifar da tarnaƙi ga iyalai cikin tsawon lokaci na rashin abinci mai gina jiki da cututtuka, da tabarbarewar kiwon lafiya a cikin zamanai.

Wasu ma’aurata da suka dauki riƙon yara takwas bayan sun rasa mahaifiyarsu sakamakon zubar jini mai tsanani a lokacin da take haihuwar tagwaye, sun shaida wa kungiyar MSF cewa suna fama wajen kula da yaran.

"Ba ma samun isashen abin da za mu iya ciyar da su. Yanzu mu 13 ne a gidan. Muna yin fate da 'yar miya tare da dan gishiri kadan ko babu mai," in ji iyayen riƙon.

Dr Burkhardt ya damu da rikice-rikicen da ke da alaka da juna da ke kara wahalhalun da jama'a ke fuskanta a fadin Sudan.

"Ayyukan gaggawa na kiwon lafiya da yawa suna faruwa a lokaci guda, ba tare da wani martani na duniya daga Majalisar Dinkin Duniya da sauransu ba," in ji ta.

"Bambancin da ke tsakanin manyan bukatu na kiwon lafiya da abinci da rashin martanin ƙsashen duniya akai-akai abin kunya ne."

Ƙungiyoyin da ke gaba da juna suna ƙara tsananta ƙarancin wadatar kayayyaki, waɗanda ke ci gaba da toshewa ko hana samun agajin ceton rai.

TRT Afrika