Daga Pauline Odhiambo
Seitebogo ta daina damuwa da tabon da yake lebenta na sama - tana kallonsa a matsayin wani bangare na kamanninta. Aikin tiyata na sauya halitta na karshe na iya kawo karshen tabon ciwon da aka sha wahala da shi tun yarinta, amma ta fi yarda ta yi murmushi mai kyalli, wanda ta amince cewa "wani bangare ne na rayuwata".
An haife ta da ciwon noma - rashin lafiyar da leben jariri na sama yake a yage - Seitebogo ta fuskanci tiyata a lokuta da yawa don samun damar yin murmushin da ya cancanta.
'Yar Afirka ta Kudu mai shekaru 32 ta yi fama da matsalar irin kallon da mutane suke yi wa wadand ke fama da matsalar. Amma hakan bai hana ta gwagwarmaya kamar sauran mutane irin ta ba.
Sakamakon ayyukan Seitebogo Peta da aka fara a 2017, matasa nagari na taimakawa wajen dawo da murmushi a fuskokin sauran mutane da ke fama da cutar ta noma.
"A lokacin da kungiyata ta fara ayyuka, na fara da niyyar sauya tunanin mutane su," in ji Seitebogo, yayin tattaunawa da TRT Afirka. "Bayan na samu juna biyu, sai ra'ayina ya sauya zuwa ga yara kanana da ke fama da wannan ciwo."
Seitebogo ta damu sosai tana tsoron kar jaririn da za ta haifa ya zo da wannan ciwo saboda zai iya gada daga mahaifiyarsa, daya daga cikin abubuwan da ke janyo ciwon noma shi ne gadar sa daga iyaye, kamar yadda Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana.
"Abu na farko da na fara yi a lokacin da likita ya miko min jaririyata shi ne na duba lebbanta," in ji ta.
"Na ji dadi da na ga ba ta da wannan ciwo na noma, duk da cewa na ci gaba da tunanin halin da iyayen yara da ke dauke da ciwon suke shiga."
Alakar iyaye
Binciken WHO na nuni da cewa babu wani dalili guda daya da ke janyo cutar noma. Tun da dai dalilai na kwayoyin halitta da aka gado daga iyaye da na muhalli na iya janyo cutar, yana da wahala a ce ga takamaiman abin ke janyo ta.
A wasu lokuta, akwai alaka da iyaye kai-tsaye. A wani lokacin kuma, abu ne da ake samun mutum daya a dangi dauke da shi.
WHO ta bayyana cewa daga cikin dalilai na muhalli da ke janyo ciwon shi ne shan wasu magunguna na musamman a lokacin da mace ke dauke da ciki, shan taba sigari ko kuma ma yadda yaro ya kwanta a cikin mahaifiyarsa.
Amma kuma, juna biyun da aka kula da shi sosai ma na iya haifar da yara masu dauke da cutar noma.
Seitebogo ta ci gaba da cewa "Wasu mutane a Afirka ta Kudu sun yi imani da cewar maita ko wata ukuba daga Ubangiji ga iyaye ko daya daga cikin su ce ke janyo wannan cuta."
"Ina kokarin koya wa mutane cewa dalilan da ke janyo ciwon noma ba daga wani dan adam suke ba."
Tabo mai sosa rai
Jariri na iya samun wannan cuta a lebensa daya kawai. Amma ita kuma Seitebogo a dukkan bangarorin leben nata ne.
Ciwon noma na iya zama a leben sama kawai, ko kuma a dukkan lebban guda biyu. An haifi Seitebogo da na biyun, kuma an yi mata tiyata a karon farko tana jaririya.
Da an yi mata aiki a asibiti da yawa to da an rufe dukkan lebban nata, sannan a yi wani aikin ga hancinta ta yadda za a hade hancin nata da sauran sassan fuskar.
An zalince ta a makaranta
Seitebogo ta sha wahala sosai lokacin da take yarinya tana fama da wannan ciwo, wanda hakan ya sanya yara da yawa suna kyarar ta.
"Na sha kokarin zama yarinya mai karfin zuciya da za ta dinga magana a koyaushe," in ji ta. "A makarantar firamare, na yi mujadala da wani yaro dan ajinmu, wanda ya doke ni a baya saboda na yi kama da wani mai gabatar da shirin talabijin da ke da kamannin kare."
Yawan zagi da cin fuska ya bar babban tabo a kwakwalwar Seitebogo wanda hakan ya sanya dole ta nemi hanyar mayar da martani ga yara.
Ta ce "Bayan na haifi jaririyata, na fara tunani game da yadda 'yata za ta kubuta daga cin zali, da a ce an haife ta da wannan ciwo na noma."
Abin ya yi yawa
Baya ga cin zalin ma a makaranta, an dinga kai yarinya Seitebogo zuwa asibiti.
"Zama da wannan ciwo na nufin yawan ganawa da manyan likitoci," in ji ta. "Za ka samu likitan kula da halittar fuska wanda zai mayar da hankali kan mukamikinka da sauran bangarorin fuska, ga mai bayar da magani, likitan hakori da sauran likitocin yin tiyata. Yanayin na da wahala sosai."
Seitebogo na kallon kan ta a matsayin wadda ta yi nasara saboda yadda iyayenta suka iya daukar dukkan wadannan nauye-nauye.
"'Yan Afirka ta Kudu da yawa da ke da ciwon noma ba su da kudin zuwa asibiti, ballantana a yi maganar tiyata."
Wannan gibi na rashin kudin kula da lafiya ne ya sanya Seitebogo ta karfafa kungiyarta wajen mayar da hankali kan taimakawa masu karafin karfi su samu sararin zuwa asbiti.
"Na hadu da iyaye mata da maza da suke korafin kula da yaro mai wannan ciwo na noma abu ne mai wahala sosai," in ji Seitebogo. "Wasu na barin yaran nasu saboda kalubalen kudade."
Murmushi kyauta
Ya zuwa yau Seitebogo ta taimaki sama da mutane 50 da suka samu tiyatar fuska.
Ta zayyana cewa "Mutane na zuwa daga kusa da nesa don samun taimako. Na ga marasa lafiya daga Gabashin Cape Town, Kwazulu Natal da Arewa maso yamma. Na taimakawa wata mai shekara 25 wajen yin tiyata a fuskar ta, sannan ta yi farin ciki bayan samun labarin za a a iya yi mata tiyatar hakora daga baya."
"Babban abun farin ciki shi ne yadda na ke aiki da marasa lafiyar da suka fitar da ran za su iya iya samun sauki, amma sai ka ga suna murmushi bayan samun waraka. Wannan murmushi ne da babu kudin da zai iya sayensa."
Seitebogo na fatan za ta fadada ayyukan kungiyarta inda za su kara da samar da cibiyar murmurewa ga dukkan wadanda ke fama da cutar bayan an yi musu tiyata.