Bayan wasu shekaru, yanzu kirkirar matashiyar mai shekara 26 ta fara kawo sauyi a bangaren kiwon lafiya. Photo: Rokhaya

Daga

Pauline Odhiambo

A lokacin da take karama, mahaifiyar Rokhaya Diagne ta sha fama da ita wajen hana ta buga wasannin bidiyo, bayan ta lura da yadda take mugun sabo da wasannin.

Da Rokhaya da mahaifiyarta din duk ba su taba tunanin wasannin da take yi din za su bude mata kofar amfani da kirkirarriyar basira wajen yaki da cutar maleriya ba.

"Kullum da na dawo daga makaranta, sai in yi sauri in shiga dakin dan uwana in fara buga wasannin bidiyo," inji ta a tattaunawarwa ta TRT Afrika.

"Haka na rika yi har lokacin da mahaifiyarmu ta ce za ta kai ni wajen likitocin mahaukata idan ban daina ba."

Bayan ta fara rage buga wasannin, sai Rokhaya ta fara tunanin yadda za ta yi amfani da basirarta wajen magance wasu matsalolin da mutane suke fuskanta. A nan sai bangaren kirkirarriyar basira ya dauki hankalinta.

Bayan wasu shekaru, yanzu kirkirar matashiyar mai shekara 26 ta fara kawo sauyi a bangaren kiwon lafiya.

Hanyoyin gano cututtuka

Kamfanin Rokhaya - Afyasense- "Afya" na nufin lafiya a harshen Swahili- ya samar da wata manhajar da ke tattara bayanai, inda ake amfani da kirkirarriyar basira wajen gwajin cututtuka da bayyana maganinsu.

Sha'awar Rokhaya ga 'zurfin ilmantarwa ya sa ta fara aikin kaddamar da manhajar gano cutar maleriya da AI mai suna Malaria Locator. Hoto: Rokhaya

"Kirkirarriyar basira ba ta zo ba ne domin ta maye gurbin kwakwalwar mutane. Tana taimakawa ne wajen saukaka wa mutane aiki, da kuma tabbatar da ana aikin cikin sauki da inganci," inji wani dalibin fasahar kwamfuta a kasar Senegal.

"Mutane da dama suna mutuwa saboda ba sa samun damar zuwa asibiti da rashin samun gwaji mai inganci, musamman a yankunan karkara a Afirka. Burina shi ne in magance wannan matsalar," in ji ta.

Da farko ta fara karatun biology ne a kwalejin kimiyya da fasaha a Dakar, sai ta watsar bayan ta je aikin sanin makamar aiki a wani wajen gwajin cututtuka a daya daga cikin manyan asibitocin birnin.

Burin da take da shi na samun kwarewa a amfani da kirkirarriyar basira ne ya sa ta fara kirkirar basirar gano cututtuka ta amfani da wata manhaja mai suna Malaria Locator ko kuma Maloc.

"Kasancewar kwamfuta na gudanar da aiki ne ta hanyar amfani da fasahar mutane suka kirkira, samun kwarewa sosai a fannin na bukatar cigaba da nazari da koyar da na'urori yadda za su gane abubuwa da fitar da sakamako ta hanyar cinke," in ji ta.

"A manhajar Maloc, an hada wasu na'urori ne da kwamfuta. An kirkiri wata fasaha a ciki da ke gano ko akwai maleriya a jikin mutum ko babu. Har yanzu ba a kammala fasahar ba, amma muna sa ran kwanan nan za mu fara gwajin."

Amfani da kirkirarriyar basira a Afirka

Har yanzu kirkirarriyar basira ba ta samu karbuwa ba sosai a yankin Afirka, kasashen kamar su Ghana, da Afirka ta Kudu da Nijeriya da Kenya da Libya da Zimbabwe da Togo da Habasha ne suke dan kokartawa wajen amfani da fasahar.

Babban kalubalen da ke gaban Rokhaya shi ne tattara bayanai, wanda a cewarta yake ba ta matsala. Photo: Rokhaya

Kasashen Afirka da dama har yanzu ba su da cigaban da ake bukata wajen dabbaka kirkirarriyar basira kamar kayayyakin samar da nagartaccen intanet da sauran ci gaban zamani. Ga kuma karancin ilimin kimiyya da fasaha da lissafi wato (STEM) wanda ke cikin abubuwan da suke kawo tsaiko wajen cigaban kirkirarriyar basira.

Rokhaya tana alfaharin samun damar zuwa karatu a Jami'ar American University of Science and Technology, da ke Dakar, inda ake koyarwa ta hanyar aiki da abin da aka koya a aikace, wanda ya taimaka wajen dabbaka burinta na yin iyo a kogin kirkirarriyar basira.

"Gwaji da jarabawa duk a aikace ake yi. Sannan binciken kammala karatu a bangaren lafiya ake yi," in ji Rokhaya, wadda ta kammala jami'ar a shekarar 2025.

"Da darasin Physic da lissafi da sauransu duk a aikace ake koyonsu, wanda hakan yana taimakawa wajen kara ba mutane sha'awar bangaren kirkirarriyar basira."

A irin wannan yanayin na koyo a aikace, malamai suna ba da aikin gida, sannan su taimaka wa dalibi wajen kammalawa.

An taba ba Rokhaya aikin kirkirar fasahar da za ta aika cikin ruwa domin dauko bayanan kifi da sauran tsirrai da suke karkashin ruwa da shakar sinadarin carbon.

Ana ba su aikin ne domin koya musu yadda za su rika magance matsalolin da suke damun mutane. An taba ba wani dalibi aikin hada karamin jirgin da zai iya daukar nauyin kilogram 100 kuma ya yi tafiyar kilomita 10 domin rage cunkoson manyan motoci a tashar jirgin ruwan Dakar.

Tuni wasu ayyukan jami'ar da ake ba dalibai ya fara samar da sakamako mai kyau wajen cigaban kananan 'yan kasuwa, kamar Solar Box, wanda asali aikin gida ne da aka ba dalibai su kirkiri babur mai amfani da zafin rana.

Babban kalubalen da ke gaban Rokhaya shi ne tattara bayanai, wanda a cewarta yake ba ta matsala.

An taba ba Rokhaya aikin kirkirar fasahar da za ta aika cikin ruwa domin dauko bayanan kifi da sauran tsirrai da suke karkashin ruwa da shakar sinadarin carbon.. Photo: Reuters

"Wasu manhajoji suna iya tattara bayanai, amma wasu lokutan manhaja takan yi kuskure. Wannan ya sa a wasu lokutan dole ka nemo wasu hanyoyin na tattara bayanan da kake bukata," inji ta, sannan ta kara da cewa, "wani lokacin ma yana daukar lokaci mai tsawon kafin ka shigar da bayanan cikin kwamfuta."

Samun kyaututtuka

Fasahar Molac ta Rokhaya na cigaba da samun nasara duk da kalubalen da take fuskanta, inda ta fara samun lashe kyaututtuka ciki har da kyautar Orange Social Venture na Afirka da ta Gabas ta Tsakiya da kyautar 'yan kasuwa ta kasar Senegal wato national social entrepreneurship award, da kuma tallafin Dala $8,000 na Amurka. Ta kuma samu kudin Switzerland 10,000 ta shirin Lafiya Innovator a Dakar.

Yadda ta fara samun nasara tun a farko-farko ya karfafa gwiwar Rokhaya. Yanzu haka ta kara zage damtse wajen ganin ta kawo sauyi a bangaren kiwon lafiya a Afirka da ma duniya baki da daya.

A daidai lokacin da kirkirarriyar basirarta ta maganin maleriya ke gab da shiga kasuwa, tuni har Rokhaya ta fara tunanin me za ta yi a gaba. Yanzu haka ta fara tunanin kirkirarriyar fasahar gano cutar kansa.

"Burina in cigaba da kirkirar hanyoyin samun kiwon lafiya cikin sauki ta hanyar tabbatar da cewa duk abin da na kirkira ya kawo sauyi mai kyau a bangaren," in ji ta a tattaunawarta da TRT Afrika.

TRT Afrika