Daga Sylvia Chebet
A duniya da take da makoma ga kirkirarriyar basira, cigaban ya zama daya daga muhimman abubuwa da ke habaka cikin sauri kuma suke kawo sauyi a fannin kula da lafiya.
Na'urorin da a Turance ake kira 'Large multi-models (LMMs)' na da ikon nazari da nadar bayanai mabambanta - hotuna, rubutu da bidiyo - sannan su samar da sakamakon da za a iya amfani da shi a bangarorin kula da lafiya da dama.
Wadannan na'urori na musamman ne wajen kwaikwayon sadarwar dan adam wajen yin ayyukan da ba tsara za su yi iya yin su karara ba.
Amma duk da abubuwa masu kyau da makoma da ake gani, ka'idojin aiki na da matukar muhimmanci.
Hukumar Kula da Lafiya (WHO) ta kawo wasu ka'idoji da suka shafi aiki da wadannan LMMs.
Ka'idojin sun samar da wasu sharudda da shawarwari 40 don gwamnatoci, kamfanonin fasaha da masu kula da lafiya su duba yiwuwar amfani da su don tabbatar da kyakyawan amfani da LMMs don bayar da kariya da habaka lafiyar al'umma.
Dr Ishmael Mekaeel Maknoon, babban likita ne a lardin Kwale na Kenya, na da ra'ayin cewa Kirkirarriyar Basira na da babbar gudunmowar bayarwa a fannin kula da lafiya a Afirka.
Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Muna da karancin likitoci da malaman jinya sosai amma za mu iya amfani da fasahar zamani wajen cike gurbin."
"Fasahar kere-kere na iya taimaka mana wajen amfani da yan kayayyakinmu da muke amfani da su, ba wai a birane ba, har ma a kauyuka."
Wata babbar dama ga nahiyar ita ce samar da ingantattun hanyoyin sadarwar yanar gizo. A kauyukan Kwale, inda Dr Maknoon ke aiki, marasa lafiya da dama na rike da manyan wayoyin hannu.
Yana aiki tare da injiniyoyi da likitoci don samar da na'urar da ke aiki da Kirkirarriyar Basira don kula da lafiya yadda ya kamata musamman ga wadanda ke cikin mummunan yanayi kamar hawan jini, ciwo sukari da na koda.
Maknoon ya bayyana cewa ya kamata gwamnatoci su mayar da hankali ga damarmakin da ke tattare da Kirkirarriyar Basira, suna masu muhawarare cewa suna da saukin samarwa, ba kamar yadda ake zuzuta cewar ba za a iya samar da su cikin sauki ba.
Nazari kan kalubale
WHO ta lura da cewa an rungumi LMMs cikin sauri sama da wasu na'urorin hidimtawa mutane a tarihi, inda manhajojin Kirkirarriyar Basira da dama irin su ChatGPT, Bard da Bert ke shiga kwakwale da harkokin yau da kullum na mutane a 2023.
"Fasahar Kiekirarriyar Basira na iya inganta kula da lafiya, amma sai har idan wadanda suka samar da su, sun fitar d aka'idojin amfani da hatsarin da ke tattare da su," in ji Dr Jeremy Farrar, babban jami'in kimiyya na WHO.
"Muna bukatar bayanai na gaskiya kuma a fayyace, da manufofin tsara wa, habaka wa da amfani da LMMs don samun sakamakon kula da lafiya mafi kyau, sannan a shawo kan gibi da ake da shi wajen kula da lafiyar."
Sabbin ka'idojin WHO sun bayyana hanyoyi biyar na aiki da LMMs a fagen kua da lafiya: gano ciwo da kula da shi, binciken alamomin cuta duba ga marar lafiya, sannan da kuma aikin gudanarwa kamar ajje bayanan yawan zuwan mara lafiya zuwa asbiti.
Sun kuma hada da amfani da LMMs wajen ilimntar da likitoci da jami'an jinya, gami da bayar da horo d amarasa lafiya da aka kirkira da binciken kimiyya, da ma samar da magunguna.
Nasara da kalubale
Yayin da ake amfani da LMMs wajen manufofi da suka shafi kula da lafiya, ana tsoron samar da bayanai na karya, nuna bangaranci, kuskure da wadanda ba su cika ba, wanda hakan na iya cutar da mutane idan aka yi amfani da bayanan wajen kula da lafiyarsu.
Ka'idojin na WHO sun kuma zayyano hatsarin da ake da shi ga tsarin kula da lafiya, kamar samu da saukin farashin LMMs da suka fi inganci.
Wadannan na'urori na LMMs za kuma su iya taimaka wa wajen magance 'sauya bayanai na na'ura' da ya shafi ma'aikatan lafiya da marasa lafiya, inda zai zama an kasa gano kura-kuran da ya kamata a ce an gano su, ko kuma a sanya zabuka masu wahala ga LMMs.
Amma Dr Maknoon na da ra'ayin cewa tare da mayar da hankali ga tsantsar bayanai, Kirkirarriyar Basira kan iya taimaka wa wajen kawar da wasu kura-kurai da dan adam kan iya yi wajen kula da lafiya.
Ya fada wa TRT Afirka cewa "Idan na cike bayanai daidai, to tabbas zan samu sakamako irin wadda na ke bukaya, bayanai na gaske sosai."
LMMs, kamar sauran nau'ikan Kirkirarriyar Basira na da iya fuskantar hatsarin kutsen yanar gizo wanda zai iya jefa bayanan mara lafiya cikin hatsari ko kuma ingancin bayanan kula da lafiya.
Domin samar da LMMs masu tsaro da inganci, WHO ta bayyana bukatar shigar da masu ruwa da tsaki daban-daban - gwamnatoci, kamfanonin fasahar kere-kere, masu kula da lafiya, marasa lafiyar da kungiyoyin farar hula - a dukkan matakai na cigaba da kuma yayin aiki da wannan fasaha, wanda ya hada da sanya idanu da tabbatar aiki da dokoki.
"Dole ne gwamnatoci a dukkan kasashe su hada kai su jagoranci kokarin da ake yi na sanya dokokin samarwa da aiki da Kirkirarriyar Basira," in ji Dr Alain Labrique, daraktan kula da lafiya a zamanance na WHO da ke sashen kimiyya.
Shawarwari
Ka'idojin WHO na da manufar taimaka wa gwamnatocisu gano tare da fahimtar amfani da hatsarin da ke tattare da amfani da LMMs wjen kula da lafiya, baya ga tsara manufofi da ayyuka don samarwa da amfani da su.
A karkashin sabbin ka'idojin, dole ne gwamnatoci su samar da kayan more rayuwa da suka hada da na'urori masu kwakwalwa da ma'ajiyar bayanan jama'a da bangaren gwamnati da mai zaman kansa zai samu damar amfana da su, amma ta hanyar da doka ta tanada.
WHO sun kuma bayar da shawarar gwamnatoci su samar da dokoki, manufofi da ka'idoji don tabbatar da LMMs da amfani da su wajen kula da lafiya sun dace da rukunnan wajibi da ka'idojin kare hakkokin dan adam don kare martaba, 'yanci da sirrin mutane.
Dole ne wadanda za su yi amfani da su, da dukkan masu ruwa da tsaki na kusa da na nesa, ciki har da masu kula da lafiya, masu binciken kimiyya, kwararrun kula da lafiya da marasa lafiya, su zama sun shiga tsarin tun da fari, a lokacin da ake habaka Kirkirarriyar Basira.
Ana tsammanin masu samar da Kirkirarriyar Basira su baiwa masu ruwa da tsaki damarmakin kawo batun aiki da dokoki, su bayyana damuwarsu, da samar da gudunmowa a yayin samar da Kirkirarriyar Basirar da ake magana a kai.
Baya ga tabbatar da aiki daidai ba tare da kuskure ba, ka'idojin na bukatar masu samar da wannan abu su iya hasashe da fahimtar mai ka iya zuwa ya komo.
Dr Maknoon ya yi amanna cewa tare da dokokin da suka dace, zuba jari yadda ya kamata da daukan matakan da ke mayar da hankali kan marasa lafiya, Kirkirarriyar Basira na da ikon kawo babban sauyi ga tsari da harkokin kula da lafiya.