Daga Firmain Eric Mbadinga
Masoyansa suna kiransa da "Dan ruwa" domin kwatanta shi da wani gwarzo na fim ba fim din "Aquaman"
Amma Mamadou Diakhaté ba kamar na fim din ba ne, wanda yake da ikon a kan halittun cikin ruwa. Shi mutum ne kamar kowa wanda jini ke gudana a jikinsa.
Asalinsa malamin makaranta ne a Senegal, amma yanzu mai kimanin shekara 36 a duniyar ya sadaukar da kansa wajen zagayawa yana haka rijiyoyi a kauyukan kasarsa masu fama da karancin ruwa, domin sha da noman rani da kiwo.
Yanzu haka Mamadou ya zagaye yanki 10 cikin 14 na kasar a shekara hudu da yake wannan aikin.
A kasar, wadda ake samun karancin ruwan sama, samunsa ba karamin abin nurna ba ne ga dubban mutane, musamman a Arewacin kasar.
A Nuwanban bara, Shugaban yanki na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama da yanayin sararin samaniya, Philippe-Auguste Moundor Sene ya ce bana za a fuskanci karancin ruwan sama a kasar.
Karancin ruwan sama da kuma rashin samun ruwan famfo a wasu yankuna na kasar ne suka karfafa gwiwar Mamadou ya fara wannan aikin.
"Idan kai malami ne a Senegal, an fi kai ka aiki a yankunan karkara. A wani kauye da na je aiki ne na ga wani abu da ya ja hankalina na fara wannan aikin na agaji," inji shi a tattaunawarsa da TRT Afrika.
Aikin gayya
Nasarar aikin Mamadou ya karfafa gwiwar mutanen yankin Kaolack na Gabas ta Tsakiyar Senegal, inda aka tura shi aikin koyarwa a kauyen Darou Salam Mouride.
Sai dai kamar duk wani aikin gayya, samun kudin aikin shi ne matsalar da yake fama da ita. Sai Mamadou ya yanke shawarar amfani da kafafen sadarwa domin neman tallafi daga wajen mutane.
Da an tara kudi, sai ya sayo kayan aikin da ake bukata, sai shi da wasu kwararrun masu haka rijiya da suke aiki tare su shiga aiki.
Tun daga rijiyar farko da ya haka, zuwa ta karshe, duk mutanen yankin ne suke kawo masa bukatar.
Da zarar an kawo masa bukatar, sai Mamadou ya je ya duba wajen, idan ya cika sharudan da ake bukata, sai shi da abokansa su fara aiki.
A wajen Mamadou da abokan aikinsa, farin cikin da mutane suke shiga shi ne bukatarsu.
"Duka rijiyoyin da muka haka, mutane ne suke tara kudin tare da hadin gwiwar mutanen da za a wa aikin. Mun haka rijiya a Kaolack da Dourbel St Louis da yankin Matam da Zinguinchor da Sédhiou da yankin Fatick," in ji Mamadou.
Tsara rayuwarsa
Da farko, Mamadou ya sha fama da kalubale wajen hada aikinsa na koyarwa da aikin agaji.
Amma saboda dadewarsa da sanin makamar aikin koyarwa, sai Mamadou ya samar da daidaito, inda ya nema aka mayar da shi bangaren da ba ya bukatar tsayawa yana koyarwa a gaban dalibai.
Wannan ya sa yake samun damar gudanar da aikinsa na makaranta, da kuma ayyukansa na agaji, inda yake samun farin cikin da kudi ba zai iya saya masa ba.
"Ina yawan tafiye-tafiye. Wani lokacin baya da na yi tafiya, sai da na yi tafiyar kusan kilomita 1,600. Sai da na kwashe kwana 15 ba na Dakar, sai ranar Sabuwar Shekara na dawo. Nakan yi tukin mota mai tsawo, ga gajiya, amma haka nan muke cigaba da kokartawa," in ji shi.
Kamar duk wani aikin gini, Mamadou da abokan aikinsa sukan samu raunuka, musamman idan suka hadu da wurare masu tsauri.
Kasancewar aikin agaji na da cin lokaci, ayyukan suna shafar rayuwar Mamadou. Wani abu da ya koya shi ne tsara rayuwarsa. Amma shi da abokan aikinsa ba sa aikin dare domin guje wa hatsari.
Haka rijiyoyi masu inganci
Yawancin rijiyoyi da Mamadou yake hakawa zurfinsu suna kai mita 25, sannan haka rijiya kan kai su kwana 30 kafin a kammala.
Idan za su yi aikin, mutanen garin ne suke samar musu masauki.
Ayyukan Mamadou ba a haka rijiyoyi kawai suka tsaya ba. A kokarinsa na ganin gwamnati da daidaikun mutane sun mayar da hankali wajen magance matsalar karancin ruwa, Mamadou yakan halarci taruka domin yin jawabi a game da muhimmancin samar da ruwan sha.
"Dole masu rike da madafun iko su yi duk mai yiwuwa wajen rage karancin ruwa da ake fama da shi a karkara," in ji shi.
"Na je yankuna da kauyuka da dama. Na tattauna da shugabannin garuruwa da talakawa. Lallai mutanen wasu yankunan suna matukar bukatar a samar musu da ruwan sha."
Duk da cewa har yanzu Mamadou bai taba samun wata karramawa ba, wadda dama ko kadan bai taba tunanin wannan ba. Ya fi mayar da hankali a kan samun hanyoyin da zai rika samun kudaden da zai cigaba da gudanar da ayyukansa domin fadada aikin.
Kamfanoni da dama suna gudanar da wasu ayyukan taimako a karkashin wani shirin tallafi na al'umma. Wani kamfani ya taba bayar da Sefa miliyan 15 domin gina rijiyoyi 15 a kasar baki daya.
Mamadou yana yawan wallafa hotunan rijiyoyi da ya gina a kafofin sadarwa. Yana kuma bayyana yadda yake kokari wajen gyara makarantu a karkara, inda yake amfani da irin hanyar da yake bi wajen haka rijiya domin wannan aikin shi ma.
A kullum kaunar Mamadou karuwa take yi a zukatar mutanen kasar Senegal.