Daga Firmain Éric Mbadinga
A matsayinsa na ɗan makaranta, Abdou Touré ya koyi darasi na rayuwa wanda yake yaɗawa ga duk wanda ya ba shi kunnen sauraro - kan cewa yanayi na buƙatar kulawa kamar yadda muma yake kula da mu.
"Ku je ku dasa bishiyoyi, gwargwadon iyawarku," mutumin wanda ya haura shekaru 40 ya shaida wa masu sauraronsa, yana mai isar da saƙonsa cikin sauƙi.
A tsawon shekaru da suka wuce, Touré ya kasance mai ba da misali wajen dasa bishiyoyi a duk sanda ya samu dama da manufa guda ɗaya ta hanyar sha'awa da kuma ƙarfafawa.
Dattijon wanda ake wa laƙabi da ''Green Uncle'' a kasarsa ta asali Senegal, irin soyayyar da Touré yake da ita a kan yanayi da kuma kishin da yake nunawa ya sanya shi daya daga cikin muryoyi masu ƙarfi a yankin Sahel a yanayin da ake ciki na ƙaruwar barazanar kwararowar hamada.
"A tafiye-tafiyen da na yi a cikin fadin Senegal da sauran kasashen da ke maƙwabtaka tun ina ƙarami ya ba ni damar gode wa yanayi da kuma bambance-bambancen da ke cikinsa.
A tsawon lokuta, na kuma lura da yadda yanayi ke canzawa, kuma lamarin na sanya ni cikin damuwa sosai," kamar yadda Touré ya shaida wa TRT Afrika.
Touré ya ɗaura damarar kiyaye muhalli ne bayan wani taron da kasar Finland ta shirya wanda ya mai da hankali kan yanayi a shekarar 2010.
Tun daga lokacin yake ta hada matasa a yankin Yammacin Afirka domin su ba shi haɗin kai wajen yaƙin da yake yi da sauyin yanayi.
Zabinsa shi ne dasa bishiyoyi a dazuzzuka.
A shekaru hudu kacal, Touré da kungiyarsa ta matasa masu fafutukar kare muhalli sun dasa miliyoyin itatuwa a busasshun wurare da kuma yankuna masu fadama, da nufin samar da daidaito da kuma sauya tsarin kwararar hamada a yankin Sahel.
A shekarar 2019, ya kaddamar da shirin "#QuartierVertChallenge", wani shiri na 'yan kasar wanda ya zaburar da matasa masu fafutuka daga kasashen Afirka 15, mussaman na yankin Sahel.
Bai yi kasa a gwiwa ba a kokarinsa, inda a cikin kwanaki biyu na ranakun bikin tuni da muhallin duniya, Camp Climat Senegal kungiyar da Toure ya kafa ta janyo masu sa kai daga ƙasashe 11 na yammacin Afirka.
"Kafin na fara soma aiwatar da shirin dasa itatuwa a dazuzzuka, nakan tattara shara a hanyoyi," in ji shi.
"Tun daga shekarar 2019, na mai da hankali kan dasa bishiyoyi. A Camp Climate Senegal, dukkanmu mun dauki shawarar taka muhimmiyar rawa a muhallinmu, hakan na nufin an daukar mataki. Bishiyoyi suna rage zafi da sinadarin CO2."
Haɓaka hamada
Duk da nasarorin da ya samu, Touré yana sane da kalubalen da ke gabansa, inda ya koka kan asarar korayen shuke-shuke a babban birnin Dakar na Senegal, yana mai kwatanta birnin da ''ginanen makabarta'' da komai ya koma launin toka''.
Kwararowar hamada a kasashe da ke yankin Sahel na haifar da gagarumin barazana ga rayuwar milliyoyin mutane.
Yankin wanda ya soma daga Senegal zuwa Sudan, yana da yanayin tsaka-tsaki na danshi, wanda ya sanya shi cikin hadari musamman ga sauyin yanayi da kuma takaita amfanin albarkatun kasa fiye da kima.
Yawan fari da ake fama da shi da kuma rashin dorewar ayyukan noma, sun taimaka wajen rage karfin ƙasa.
Tsarin wanda aka fi sanin sa da kwararowar hamada, yana rage yawan amfanin gona da kuma kara ta'azzara matsalar karancin abinci da talauci a tsakanin al'ummomin yankin wadanda galibinsu manoma ne.
Sai dai duk da hakan Touré bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya jajirce wajen neman karin magoya baya a nahiyar ta kafafen sada zumunta na intanet tare da fatan an kawo karshen barazanar kwararowar hamada a Senegal da Burkina Faso da Nijar da kuma Mali.
"Wurare daban-daban da kuke gani a taswirar Afirka sun nuna inda jakadunmu suka fi ayyuka''. kamar yadda Touré ya shaida wa TRT Afrika.
Ya kara da cewa ''waɗannan wurare su ne Yaoundé a Kamaru da Dakar a Senegal da Chadi da Nijar. A Senegal, inda na fi yawan gudanar da ayyukana, mun fi mayar da hankali wajen dasa bishiyoyi a azuzzukan da ke Dakar da kuma Yankunan Kaolack sai kuma yankin Matam da Podor da ke gefen hanyar kogin Senegal," in ji shi.
Murya mai ƙarfi
A shekaru kusan hudu kacal, shirin na QuartierVertChallenge ya samu gagarumin ci gaba a fannin kare muhalli, inda ya dasa miliyoyin itatuwa a yankunan fadama da kuma dubban wurare da ba fadama ba.
A gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka kammala kwanan nan a kasar Cote d'Ivoire, ya yi amfani da karfin da wasanni ke da shi wajen yada manufofinsa.
"Uncle Green's AFCON" ya karfafawa daidaikun mutane da su dasa bishiya daya akan kowace kwallo da aka ci a lokacin gasar.
Jarumtakar Touré bai wuce haka kawai ba. A watan Maris na 2023, sai da hukumar kula da ilimi da kimiya da al'adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO ta ba da shi dama a taronta mai taken "Cultivating our Humanity".
Kazalika shirin QuartierVertChallenge ya samu haɗin gwiwa da gundumomi, da jami'o'i da kuma manyan makarantu a ƙasashe da dama don haɓaka ayyukan kare muhalli da haɓaka sha'awar sake alkinta dazuzzuka.
Har ilau kungiyar ta samu karfin gwiwa daga Yacouba Sawadogo na kasar Burkina Faso, wanda ya mutu a shekarar 2023, ya bar tarihi kan kare muhalli da ya shahara a duniya.
Kamar Sawadogo, wanda aka karrama shi da lambar yabo ta Majalisar Dinkin Duniya ta Duniya a cikin 2020, Touré yana ba da buri da shawarar samun hadin gwiwa daga kowane bangare na al'umma a kasashen yankin Sahel don ƙirƙirar wani tsari na kare muhalli.
"Dole sai gwamnatoci su dauki kwararan matakai tare da kaddamar da yakin wayar da kan jama'a don kawo sauyi a yankin Sahel da gaske," in ji shi.