Ruwan najasa na kwarara ba tare da ana nuna damuwa da hakan ba a unguwarsu Adella Ngonidzashe ta Kuwadzana da ke wajen babban birnin kasar Zimbabwe, Harare.
"Hatta da ruwan famfon ma ya zama kore; ba ma shan sa. Sai dai mu yi amfani da shi a bandaki," kamar yadda matar mai shekara 43 ta shaida wa TRT Afrika.
Duk da cewa Adella tana yin duk abin da ya kamata don kare iyalinta daga illar rashin tsaftar muhalli a unguwarsu, sai da annobar cutar amai da gudawa wato kwalara ta kutsa gidanta.
Cutar da ƙwayoyin bakteriya ke jawowa, ta zama annobar da duk shekara sai ta ɓarke, wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutum 8,000 a Zimbabwe a bana kawai.
Ƴar Adella mai shekara takwas mai suna Kupashe na daga cikin waɗanda suka kamu da cutar a gidanta, inda wataƙila ta kamu da ƙwayar cutar a lokacin da take wasa a ƙofar gida.
"A lokacin da na lura da ƴata na zuwa banɗaki akai-akai, sai na gane lallai babu lafiya, sai na yi gaggawar kai ta asibiti," in ji Adella.
"Sannan kuma tana ta amai, Sai suka ba ta ruwan gishiri da siga da wasu magungunan na rage raɗaɗi da kashe ƙwayoyin cuta.
Wannan ne karo na biyu da iyalan Adella suka kamu da cutar kwalara a ƙasar da ke yankin kudancin Afirka.
A shekarar 2008 zuwa 2009 ma hakan ya faru, a lokacin da fiye da mutum 98,000 suka kamu da cutar a faɗin ƙasar. Aƙalla mutum 4,000 ne suka mutu a lokacin.
Tun watan Fabrairun bana, hukumomin lafiya suka ba da rahoton cewa fiye da mutum 150 sun mutu sakamakon cutar da ake zargin kwalara ce ta kashe su.
Cuta mai muni
Kwalara cuta ce mai sanya gudawa wacce ƙwayoyin cutar Vibrio cholerae da ke kama hanji ke jawowa. Kwayoyin cutar na shiga jiki ta hanyar cin gurbataccen abinci ko ruwa, kuma suna iya kisa cikin ƙanƙanin lokaci idan ba a kula ba.
Abu mai daɗaɗa rai shi ne cewa ana iya saurin shawo kan cutar kwalara, yawanci ta hanyar yi wa marasa lafiyan ƙarin ruwa.
Hukumar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Amurka CDC ta ce aƙalla mutum ɗaya cikin 10 da ke kamuwa da kwalara na fuskantar tsananin amai da gudawa da kartar ƙafafu, inda ruwan jikinsu kan ragu ya saka musu kasala da kaɗuwa.
A shekarun baya-bayan nan kwalara na yawan ɓarkewa a fadin Zimbabwa inda take jawo mummunar asara, kuma ƙazanta da rashin tsaftar muhalli a garuruwa da dama ke jawo hakan.
"Akwai kwatoci da shara barkatai ta ko ina inda yaranmu ke wasa. Ina zaton a can ƴata ta kwaso cutar," in ji Adella.
Yankunan da aka fi samun cutar kwalara
A yankin Kuwadzana da sauran wuraren da aka fi samun cutar kwalata, hukumomin lafiya sun yi gargaɗin cewa ko ruwan burtsatse da rijiyoyi waɗanda da su mazauna yankin suka dogara a kai don samun ruwa, a yanzu ba su da tsaftar da za a iya sha.
Kwalara ta yaɗu a gundumomi 10 na ƙasar, kamar yadda ministan lafiya Douglas Mombeshora ya faɗa, wanda yake ta kai ziyara yankunan da ke fama da cutar tun bayan ɓarkewar annobar ta baya-bayan nan.
An jere masu fama da amai da gudawa a cikin wani tanti na musamman a asibitin Kuwadzana, inda ake ba su ruwan gishiri da siga da zarar sun isa asibitin.
Duk da cewa Kupashe ta warke tas har ma ta koma makaranta, har yanzu bala'in annobar kwalara na zama babban ƙalubale da ke sa a'ummar Zimbabwe rayuwa cikin ƙunci.
Tarin bola da shara da kwatoci da najasa da ba a kula da su sun zama tamkar ruwan dare a unguwanni a faɗin birnin Harare.
"Ba wani abu da yawa da za mu iya yi don shawo kan wannan annoba baya ga wanke hannayenmu sosai da sabulu," kamar yadda Tecla Bomba, wata mai sayar da kaya a garin Chituinguiza na Harare, ta shaida wa TRT Afrika.
"Ba ko yaushe muke samun ruwan famfo ba. Sau ɗaya muke samun ruwa a mako, kuma a wasu lokutan sai mu yi kusan wata uku zuwa huɗu ma ba mu da ruwan," in ji Tecla, wacce ɗanta ya yi fama da cutar kwalara a shekarar 2015.
"Muna ɗiban ruwan sha daga rijiyoyin da ba su da tsafta. Ina ga a nan ɗana ya kamu da cutar.
Chituinguiza na ɗaya daga cikin gundumomi 17 da ke fama da cutar kwalara a kasar Zimbabwe. A wannan shekarar ta 2023 cutar ta fara ɓarkewa ne a gundumar Buhera, wani wuri da ake yawan fama da ita, yayin da aka samu ƙarin ɓullar cutar a gundumomi 45 daga cikin 64 na ƙasar a bana.
Ƙalubalen yanki
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ana ci gaba da samun ƙaruwar cutar kwalara a Afirka, a daidai lokacin da cutar ke ƙamari a duniya.
Kashi 21 cikin 100 na masu fama da cutar da kuma kashi 80 cikin 100 na mace-macen da aka samu a duniya tsakanin shekarar 2014 zuwa 2021 duk a Afirka ne, kamar yadda alƙaluman WHO suka nuna.
Hukumomin birnin Harare suna yawan rarraba magungunan tsaftace da tace ruwa don yaƙi da cutar kwalara. Sannan gwamnati ta fara sanya dokoki a wuraren taruka da ma fannin sayar da abinci, baya ga sanya ido da take yi a yayin jana'iza a dukkan yankunan da ake fama da kwalara.