Kungiyar AU ta ce har yanzu akwai sauran kasashe da dama daga nahiyar wadanda ba su saka hannun jari wajen shigar da maya cikin matakan samar da zaman lafiya./ Hoto: AP 

Daga Coletta Wanjohi

Tagwayen ƴaƴan Fatma Ibrahim sun yi ƙanana sosai wajen fahimtar irin wahalhalun da rayuwarsu ta faɗa a ciki tun bayan haihuwarsu a watan Disambar 2023.

Sai dai lamarin ya bambanta da na mahaifiyarsu. A kullum tana rayuwa ne cikin ɓacin rai da magiya kan cewa yaranta mata sun cancanci samun rayuwa mai kyau.

La'akari da rashin matsuguni da abinci mai gina jiki da kuma rashin tabbas a makomarsu, tagwayen yaran ba su taɓa sanin jin daɗin zama a muhallin gida ba.

Suna zaune ne a sansanin ƴan gudun hijira da ke Kalma a Kudancin Darfur mai fama da rikici a Sudan - sun kasance fursunoni a rikicin da ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF tun watan Afrilun bara.

Rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewa yaƙin ya yi sanadiyar raba mutane sama da miliyan takwas daga matsugunansu, yayin da mutane miliyan biyu suka tsere zuwa ƙasashe da ke maƙwabtaka.

Kazalika rahoton ya ce akwai ƴan Sudan mutum miliyan 6.2 da suke zaune cikin ƙasar cikin mawuyacin yanayi a cunkoson sansanonin da ke faɗin ƙasar.

"Ban iya shayar da ƴaƴana nonon uwa ba saboda rashin abinci mai gina jiki, sannan babu wasu dabarun kayan abinci na jarirai, don haka jikinsu ya koma irin na waɗanda ke fama rashin abinci mai gina jiki har sai da aka kwantar da su a cibiyar kiwon lafiya," kamar yadda Fatma ta shaida wa TRT Afrika.

Waɗanda suka fi fuskantar wahalhalu

Kamar yadda yake a sauran sassan duniya, rikice-rikice a Afirka sun fi shafar mata da ƙananan yara.

Bayan munanan rikicin da ya barke a Arewacin Habasha tsakanin shekarar 2020 zuwa 2022, mata da dama sun yi zanga-zangar neman zaman lafiya. / Hoto: AP

A watan Disambar bara ne, taron ƙungiyar Tarayyar Afirka AU kan mata da zaman lafiya da tsaro a Afirka ya yi nuni kan illolin rashin jinƙai da ke ƙara ta'azzara da rikice-rikicen da nahiyar ke ci gaba da fuskanta, daga cikin har da ƙasar Burkina Faso da Chadi da DRC da Nijar da Mali da kuma Sudan.

Muhimmin sakon da ya fi ɗaukar hankali a taron shi ne buƙatar sanya mata cikin tsare-tsaren samar da zaman lafiya a Sudan ta hanyar kafa ƙungiyar tuntuɓa ta mata wadda za ta goyi bayan ƙudurin tawagan AU ta musamman wajen fafutukar ganin an tafi da kowa ba tare da la'akari da jinsi ba.

Watanni bayan haka, har yanzu ba a kai ga soma shirin ba saboda duk ƙoƙarin da ake yi na samar da zaman lafiya a Sudan ya ci tura.

Fatma dai ba ta da masaniya kan dalilan da za su mata irinta su kasance cikin tsarin shirin samar da zaman lafiya, ita dai burinta shi ne ta koma gida.

Fatma ba ta san me zai sa masu irinta su kasance cikin shirin zaman lafiya ba. Abin da take so shi ne ta koma gida.

Illa ta dogon zango

A ƙasashen da ke cikin yanayin farfaɗowa bayan tashe-tashen hankula da suka fuskanta, kamar Habasha da Sudan ta Kudu, har yanzu mata da ƴan mata da dama ba su warke daga tabon rasa matsugunansu ba, da cin zarafi tsakanin jinsi da kuma mummunar illar yaƙi.

AU ta damu matuƙa kan rashin wakilcin mata a matsayin masu shiga tsakani a fagen sasantawa da matsayin masu sanya hannu da sa ido kan ayyukan samar da zaman lafiya a faɗin nahiyar.

"Muna cewa idan babu mata a kan teburin, damar samun zaman lafiya zai raguwa. Muna buƙatar gyara wannan matsalar," in ji Bineta Diop, wakiliyar AU ta musamman kan mata, zaman lafiya da tsaro, a yayin da hirar da TRT Afrika ya yi da ita.

A shekarar 2014, AU ta nada Bineta Diop domin ta samarwa ƴan uwanta mata na Afirka murya kan batutuwan zaman lafiya da sulhu. / Hoto: TRT Afrika

A shekarar 2014 ne, ƙungiyar AU ta naɗa Diop don ingantawa da kuma ɗaukaka muryar mata a fagen samar da mafita a tashe-tashen hankula da kuma warware rikici tare da ba da shawarwarin kan hanyoyin kare haƙƙinsu gami da kawo ƙarshen cin zarafin mata.

"Me ya sa muke saka jari kan waɗanda ke riƙe da bindigogi? Muna rashin nasara saboda muna zuba jari a ɓangaren da bai dace ba. Don haka, muna bukatar canjin yanayi da kuma tabbatar da cewa an dama da mata hanyoyin magance matsalolin," in ji Diop.

Anita Kiki, jami'ar Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan ta Kudu, ta ce yana da matuƙar muhimmanci ga abokan hulɗar ci gaba su saurara tare da bin ra'ayoyin matan da duk wani rikici ya shafa.

Ta yi tuni kan wata ziyara da ta kaiwa wasu ƙungiyoyin mata a yankin Darfur na ƙasar Sudan, inda ta dawo da tabbacin cewa mata suna da baiwar iya kawo ƙarshen duk wani tashin hanakali a cikin al'ummarsu.

Mata a Laberiya sun taka rawa wajen kawo karshen rikicin cikin gida da aka kwashe shekaru 14 ana yi. /Hoto: Wasu

“Wata shugabar ƙungiyar mata ta dube ta ce min, ‘Idan kina son yin wani abu, to ki yi abu ɗaya, akwai maza ɗauke da bindigogi a bakin manyan tituna, idan kika yi ƙoƙarin cire su, za mu ci gaba da harkokinmu. Ba mu buƙatar wani abu da ya fi hakan.' Irin fahimtar za a samu."

Tsare- tsare sun kasance a kan takarda

Akalla kasashe 30 na Afirka, ko fiye da rabin Nahiyar, sun amince da tsare-tsaren shigar da mata cikin ajandar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa.

Ko da yake, aiwatarwa ne ya zama babban ƙalubale.

MDD ta ce tsarin shigar da matan Afiirka hanyoyin zaman lafiya da siyasa na da nasaba da ka'idojin al'adu wanda a mafi yawan lokuta ke zama kalubale.

"Akwai bukatar karin hadin kai da hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki da ke aiki kan batutuwan da suka shafi mata da, zaman lafiya, da tsaro a matakin shiyya-shiyya da na kasa baki daya.

Kungiyoyin farar hula na mata da ke aikin samar da zaman lafiya da magance rikice-rikice na fama da rashin tallafi na kudi da kuma rashin damawa da su a fagen tattaunawa da ta shafi tsare-tsare."

Masana sun ba da shawarar a saka kason jari mai tsoka wajen ilmantar da mata da matasa don ba su damar ba da gudumawar samar da mafita daban-daban don sasanta matsalar rikice-rikice da ke neman gindin zama.

"Idan mata suka yi jagoranci, za a samu tasiri mai kyau sosai, sannan ba mata kadai bane lamarin ya shafa ba, Su ma wadanda suka tsira ne da rayukansu kuma wakilan canji," kamar yadda Diop ta shaida wa TRT Afrika.

TRT Afrika