Hayaƙi ke nan da ya turnuƙe a yayin fafata faɗa tsakanin mayaƙan RSF da dakarun gwamnati a birnin Khartoum. / Hoto: Reuters

Daga Emmanuel Onyango da Susan Mwongeli

Duk wani fata nagari ya disashe, kuma iyalai na mayar da hankali kan yadda za su tsira a yayin da rikicin jin ƙai mafi muni a duniya ke ci gaba da wakana a Sudan.

Ana ta gwagwarmaya da lokaci don dakatar da ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka mafi girma daga rushewa baki ɗaya, kuma ana raina hatsarin da rugujewar ƙasar za ta janyo, kamar yadda ƙwararru suka yi gargadi.

"Ɓangarorin da ke rikici da juna sun duƙufa wajen ganin sun kammala komai a fagen daga, wanda na da matuƙar wahala," in ji Tighisti Amare, Mataimakiyar Darakta Mai Kula da Shirye-Shiryen Afirka a Chatam House kamar yadda ta fada wa TRT Afrika.

"Lamarin ya munana; halin jin ƙai da aka shiga ya wuce duk yanda ake tunani, kuma lamarin ba ya samun kulawar da ta kamata a ce ya samu daga ƙasashen duniya, duba ga tsananin rikicin," in ji ta.

Babu alamun za a kawo karshen wannan gaba a yakin da ya tarwatsa ƙasar tun watan Afrilun 2023. Farmakan baya-bayan nan da sojoji suka kai ya bayar da damar sake ƙwato muhimman garuruwa daga hannun mayaƙan RSF.

Rikicin ya yi ajalin rayukan dubban mutane tare da raba fiye da mutane miliyan 11 da mahallansu, ciki har da miliyan 3.1 da suka guje wa ƙasar, kamar yadda alkaluman Majalisar Ɗinkin duniya suka bayyana.

Mata na tafiya a garin Omdurman da yaki ya kacalcala a ranar 2 ga Oktoban 2024.

Rashin aminta da juna tsakanin shugabancin bangarorin da ke rikici da juna ya sha kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da ba ta yin nasara, inda duk wani yunkuri na shiga tsakani ya ci tura. Wannan na zuwa duk da kiraye-kirayen kasa da kasa na a kawo karshen yakin, da samar da hanyoyin isar da kayayyakin taimakon jin kai.

Matsin lamba

"Yana da matukar wahala a gano waye yake kan daidai, kasashen da suke da kan gaskiya da za su shiga tsakani. Zama na baya-bayan nan a Geneva ya rushe, wand aya dinga kira da a dakatar da adawa a fsadin kasar tare da bayar da damar taimakon jin kai." in ji Amare.

Har yanzu ba a gama gano hanyar da za a warware rikicin ba, amma kwararru na bayar da shawarar cewa muhimmin mataki shi ne a tsawatar wa da kasashen da ke bayar da makamai da talafi ga bangarorin da ke rikici da juna.

A watan Satumba, Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa "wasu ƙawayen ɓangarorin da ke rikicin na ƙara rura wutar rikicin na Sudan," amma ba ta ambaci sunan wata ƙasa ba ko wata ƙungiya da ke aika wa da makamai zuwa ƙasar.

"Akwai wasu abubuwa da za a iya cim ma wa, ɗaya daga ciki shi ne matsin lamba ga ƙasashen da ke sayar da makamai ga ɓangarorin da ke rikici da juna," Amare ta fada wa TRT Afrika.

"Haka zalika akwai buƙatar ƙara matsin lamba ga manyan masu ruwa da tsaki a yankin, waɗanda suke aiki tare da ɓangarorin biyu don ganin an tsagaita wuta da zama a teburin sulhu," kamar yadda ta ƙara bayana wa.

Yaƙi ya raba kusan rabin jama'ar kasar da matsugunansu.

Sakamakon gogayyar neman ƙarfin faɗa-a-ji a Sudan da ake yi, ƙwararru sun yi gargadin cewa ba a wani mayar da hankali sosai wajen tuntuɓar fararen hula don dawo da tsarin siyasa ba.

Rikicin jin ƙai

Rikicin ya janyo matsananciyar yunwa da cututtuka a faɗin ƙasar. Kusan mutane miliyan 26 - rabin jama'ar kasar - na fuskantar ƙarancin cimaka, abinda Majalisar Ɗinkin Duniya ta kira halin jin ƙai mafi muni a tarihin baya-bayan nan.

A yayin da adadin mutanen da aka kashe a arangama ya kai kimanin 27,000, kamar yadda ACLED da ke sanya ido kan rikicin suka bayyana, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta rawaito - masu sanya idanu kuma na cewa adadin na iya haura haka saboda rugujewar tsarin kula da lafiya a ƙasar.

Turkiyya na daga cikin ƙasashen da suke ƙoƙari wajen aika kayan agaji zuwa Sudan, tana kai muhimman kayayyaki ga kasar da yaƙi ya ɗaiɗaita.

‘Zaman Lafiya kawai’

"Muna godiya matuka ga Turkiyya, wadda ta dinga aika wa da kayan agaji. Sun aiko da ƙarin jiragen ruwa uku a ƙanƙanin lokaci, wanda yake ɗauke da sama da tan 8,000 na kayan abinci, da magunguna da kayan kwanciya," in ji Nadir Yousif ElTayab, jakadan Sudan a Turkiyya a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Hoton jirgin ruwan Turkiyya ɗauke da tan 2,408 na kayan jin kai zuwa Sudan.

"Amma har yanzu, Ina tunanin akwai giɓi, sama da mutane miliyan 8 da aka raba da matsugunansu."

Ya ce Gwamnatin Riƙon Ƙwarya ta Sudan ƙarƙashinJanaral Abdulfatah al Burhan "ce ta gaskiya kuma na da niyyar" kawo ƙarshen rikicin.

Amma dole matakin ya zama zaman lafiya "bisa adalci" wanda ke nuni ga za a dora alhakin rikicin kan mayakan RSF.

"Muna son ganin an samu zaman lafiya nan da wani dan lokaci. Amma ya zama dole ƙasashen duniya su la'anci wadannan 'yan ta'adda su kira su da sunan 'yan ta'adda, waɗanda suke aikata assha." in ji shi.

Mayakan RSF ma sun sha bayyana cewa suna son a yi sulhu da sojojin Sudan tare da kawo ƙarshen yaƙin.

Sai dai kuma, rikicin ya ci gaba da ta'azzara, yana sanya tsoro game da makomar jama'ar Sudan, ciki har da mata da yara ƙanana da ba su ji ba ba su gani ba, waɗanda su suka fi illatuwa sakamakon yaƙin.

TRT Afrika