Kazalika jarabar shan suka ya kuma haɗa ci gaba da shan sukari duk da mummunan illar da yake da shi ga lafiya ko yanayin jin daɗin rayuwa. / Hoto: Reuters  

Daga Mazhun Idris

Fitaccen littafin yara na Roald Dahl na shekarar 1964, Charlie and Chocolate Factory, cikin ba'a, ya bayyana illar shan zaƙi lokacin da Augustus Gloop mai yawan ciye-ciye ya faɗa cikin tafkin cakulan yayin da yake ƙoƙarin sha daga gare shi.

A zahirin gaskiya, makamin sukari da kuma shan sa a duk duniya na da matukar hatsari wanda da ƙyar yake samun kulawar da ya kamata, a cewar masana.

A lokacin da aka samu karancin sukari a kasuwannin kasar Tunusiya a watan Afrilun bara, hukumomin kasar sun yi rabon kayayyaki tare da kayyade yawan sayar da su kan kilogram biyu ga kowane abokin cikini a duk mako.

A birnin Nairobi na kasar Kenya, Fredrick Nzioka ya takaita yawan sukarin da yake sha a kullum zuwa cokali daya a kowane kofin shayi da safe. Sai dai yana damuwa game da yadda yaransa suke cin kayayyakin da aka haɗa su da sukari sosai, lamarin da yake sanya lafiyarsu cikin haɗari.

"Suna son kayan zaki, alewa da ire-iren su kek da dai sauransu,'' kamar yadda Nzioka, babban manajan gudanarwa a wani kamfanin fasaha a Nairobi ya shaida wa TRT Afirka.

Zainab Jumare, 'yar jarida a wani gidan rediyo da ke birnin Zaria a Nijeriya, ta kan sha kusan gwangwani uku na kayan zaki a kullum, amma ta dage kan cewa ba jaraba ce ke damunta ba. ''Idan ina so, zan iya tsawon kwanaki ba tare da na sha abu mai zaƙi ba,'' in ji ta.

Ba Jumare ba ce kaɗai take da irin wannan dabi'a ta dogaro kan sukari ba tare da sanin illarsa ba.

A tarihi, dabarun samarwa da kuma tallace-tallace kan abinci masu zaƙi da kuma abubuwan ciye-ciye da ake haɗawa da sukari sun ƙarfafa yawan sukarin da mutane suke ci.

Dabi'un jaraba

Bincike daban-daban sun nuna haɗuran kiwon lafiya da yawa kamar ƙiba da nau'in ciwon sukari na 2, da matsalolin da suka shafi hakora da cututtukan zuciya, da yanayin damuwar jiki a matsayin sakamakon kai tsaye na yawan amfani da sukari da ake iya fuskanta.

"Maganin yawan shan sukari da inganta halayen cin abinci masu kyau su ne abubuwan da ya kamata a sa a gaba a Afirka da ma duniya baki daya,'' a cewar Dr Musa Ibrahim Kurawa, wanda ya gudanar da bincike kan yawan jaraba son abubuwa.

Yawan dogaro kan sukari yana haifar da mumunar illar ga lafiyar hakora, a cewar masana. Hoto: Hotunan Getty

Ya bayyana jarabar sukari, wanda kuma ake kira da dogaro kan sukari ko sha'awar sukari, a matsayin wani "yanayin da mutum ke da sha'awar abinci ko abin sha da ke da sukari a cikinsa".

A mafi yawan lokuta, sha'awar ''takan yi tsanani kuma da wuyar iya takaita ta, wanda hakan kan haifar da yawan cin abinci mai zaƙi sosai,'' a cewar Dr Kurawa wanda ke koyar da ilimin halittar jiki ɗan'adam a Jami'ar Bayero da ke Kano a Nijeriya.

''Tasirin jarabar shan sugari na tattare da illar da yake da shi kan tsarin ƙwaƙwalwa, idan aka sha sukari, yana sakin ƙwayoyin halitta irin su dopamine, wanda ke alaƙa da yanayin tsari da walwalar ɗan'adam,'' kamar yadda ya shaida wa TRT Afirka.

A takaice dai, jarabar sukari ta ƙunshi yawan cin abinci mai zaƙi, musamman waɗanda aka sarrafa su da yawan sukari kamar sinadarin sucrose da kuma sinadarin fructose corn syrup masu yawa.

Masanan ilimin sassan jikin ɗan'adam sun bayyana cewa, a yayin da aka kwashe tsawon lokaci ana amfani da sukari, za a samu canje-canje a yanayin aikin ƙwaƙwalwa da kuma kewayawar jini, wanda hakan kan haifar da yawan dogaro kan sukari don jin daɗi.

Zainab Jumare ta bayyana dabi'arta ta shan kayan marmari masu zaƙi. "Suna tafiya sosai da abinci, kamar dai kayan ciye-ciye na zaƙi," in ji ta.

Wasu suna son irin kuzarin da suke samu daga cin wani mai zaki a yayin lokutan aikinsu.

Yaduwarsa a Afirka

Dokta Kurawa ya yi nuni da cewa, akwai takaitattun bayanai kan yawaitar shaye-shayen sukari a Afirka.

''Har ilau, babu shakku kan cewa nahiyar na fuskantar canji a ire-iren abinci mai gina jiki wanda ke nuna sauyin da aka samu na abinci masu yawan sukari da kitse mara lafiya da kuma abincin da aka sarrafa,'' in ji shi.

Ya dora alhakin hakan kan yawan birane da sauye-sauyen salon rayuwa da kuma saukin samun abinci da aka sarrafa da abubuwan sha a fadin nahiyar.

"Girman matsalar ta bambanta bisa ga abubuwa kamar yanayin tattalin arziki da al'adu, da samun damar kiwon lafiya," in ji Dokta Kurawa.

Mafi muni, sukari ya samu karbuwa a tsakanin al'umma da al'adu, kuma yawanci ana iya daidaita jarabarsa.

Galibi masu sana'ar abinci suna ƙara sukari ko kayan zaki don haɓaka ɗanɗanon abincinsu. Tun da sukari na da yanayin kara ɗadi kan abincin ɗan'adam, kana yana saurin haifar da halayen jaraba da kuma wuce gona da iri.

Haɗura masu alaƙa

Dr Kurawa ya bayyana cewa, har yanzu ba a ɗaukar yawan shan sukari a matsayin wata cuta da binciken asibiti ya gano a hukumance ba, sai dai yana iya taimakawa wajen bunkasa ko kuma ta'azzara wasu yanayin kiwon lafiya.

"Yanayin kwayoyin halitta da muhalli da kuma salon rayuwa duk suna taka muhimmiyar rawa," in ji shi.

An alaƙanta abincin da ke da yawan sukari da haɗarin cututtukan da suka shafi zuciya, waɗanda aka ƙidaya daga cikin manyan cututtukan da ke haifar da mace-mace a Afirka.

Yawan cin abinci mai sukari na iya haifar da rashin lafiyar hakori, kamar ruɓewar haƙori da kogo, wanda zai iya haifar da sakamako tsawon lokaci a kan lafiya da walwala mutum.

Dangane da karancin abinci mai gina jiki, yawan cin abinci da abubuwan sha masu sukari na iya kawar da aikin abinci mai gina jiki, wanda ke haifar da gazawa a cikin muhimman abubuwan gina jiki.

Yawanci, magance jarabar sukari ya haɗa da rage yawan shan sukari a hankali, da ɗaukar halayen cin abinci mai kyau ga lafiyar jiki, da kuma neman shawarwari daga masana ilimin abinci mai gina jiki da masu ilimin halayyar ɗabi'a.

Masana sun ba da shawara ga gwamnatoci kan su mayar da hankali kan kamfen na kiwon lafiyar jama'a da ilimin abinci mai gina jiki, tare da ɗaukar tsauraran ka'idoji kan masana'antun sarrafa abinci, tare da sanya haraji kan abubuwan sha masu zaƙi.

TRT Afrika