Daliban Afirka a Gaziantep na koyon yadda ake ba wa kai kariya daga girgizar kasa. Hoto: AA

Daga Charles Mgbolu

Rana ce da ake tsananin sanyi a kudu maso gabashin Turkiyya, a yayin da Yahaya Hassan Labaran, mai karatin digirgir a fannin Injiniyancin gine-gine da ya zo daga Nijeriya, tare a wasu daliban 15 suka shiga wani gidan abinci a kusa da Jami'ar Gaziantep don yin addu'a da raba abinci.

Labaran ya yi murmushi a yayin da yake kallon gefe; bai sake ganin wasu daga wadannan abokan nasa ba tun 6 ga Fabrairun 2023.

Motsin kasar da aka samu sau biyu masu karfin awo 7.7 a 7.6 a ma'aunin Ritcher ta girgiza lardunan Turkiyya 11 - Adana, Adiyaman, Diyarbakir, Elazig, Hatay, Gaziantep, Kahramanmaras, Kilis, Malatya, Osmaniye da Sanliurfa. Alkaluman gwamnati sun ce mutane 53,537 ne suka mutu, yayin da 107 suka samu raunuka.

Labaran da abokansa na cikin dakunan kwanansu na Jami'ar Gaziantep a lokacin da bangwwaye suka fara karkarwa da misalin karfe 4.17 na dare.

A lokacin da girgiza ta biyu ta afku, Labaran ya iya tuna yadda ya rungumi kwamfuta da fasfo din sa tare da sauka kasa, ga kuma matattakalan benen bakikkirin.

"Na zo daga Nijeriya kuma ban taba shaida girgizar kasa a baya ba. Abin da ya afku a wannan safiya za ci gaba da kasancewa abu mafi tsoratar da ni a rayuwata," ya fada wa TRT Afirka.

Labaran a lokacin yana shekarar farko a Jami'ar Gaziantep. Photo: Labaran

Ranar 6 ga Fabrairun 2023 ta kuma zama bakar rana ga Aliyu Jigawa shi ma dan Nijeriya. Wannan dalibi da ke karatun digiri na biyu a fannin Injiniya a Jami'ar Gaziantep, kuma lamarin ya faru yana bacci a gidan kwanan dalibai a lokacin da ya ji ginin na rawa.

"Abin ya zama kamar wani shirin fim. Ban san cewa girgizar kasa ba ce. Ban san me ke faruwa ba.

"Na farka daga gadona tare da fara karanta addu'a," Jigawa ya zayyana haka ga TRT Afrika.

Gamayyar 'yan Afirka

Jami'ar Gaziantep, wadda ke da tsangayoyi 20 kuma kuma an yarda da makarantar saboda yadda take da fannonin kimiyya da binciken fasahar kere-kere, inda take kuma jan hankalin dubunnan daliban kasa da kasa. Kasancewar Turanci ne babban yaren koyo da koyarwa a Jami'ar, hakan ya anya daliban Afirka ke zuwa.

Ya zuwa watan Janairun 2023, kusan daliban Afirka 60,000 ke karatu a Turkiyya, da yawa sun samu tallafin karatun gwamnatin Turkiyya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito Ministan Harkokin Wajen lokacin Mevlut Cavusoglu na fada makonni kafin afkuwar girgizar kasar.

Gwamnatin Turkiyya ta taimaka wa daliban Afirka da dama da ibtila'in girgizar kasar ya rutsa da su inda suka koma wasu garuruwan don kammala karututtukansu, Dalibai irin su Labaran Aliyu sun hakura a ci gaba da zama a inda suke.

Gwamnatin Turkiyya ta taimaka wa daliban Afirka da dama da ibtila'in girgizar kasar ya rutsa da su inda suka koma wasu garuruwan don kammala karututtukansu.

"Na yanke hukuncin zama a inda na ke saboda ina son bayar da gudunmawa don ganin wannan mummunan yanayi ya koma wani babban karfi da darasi," Labaran ya fada.

Yana daya daga cikin shugabannin kungiyoyin dalibai a Turkiyya da aka samar bayan afkuwar girgizar kasar.

"Mun ga yadda girgizar kasar ta yi tasiri a kan daliban kasahen waje. An kafa kungiyar don saukaka sadarwa a tsakaninmu," in ji Labaran.

Zauren whatsapp na kungiya da ke da mambobi akalla 1000, na yada bayanai kowanne lokaci, musamman ga sabbin dalibai da ke zuwa wadanda ke samun bayanan yadda za su zauna kalau a kasar.

Sama da gidaje da wuraren sana'a 200,000 aka sake gina wa a yankunan da aka samu girgizar kasar. Hoto: Labaran

"Tare da kwarewa ta a matsayin injiniyan gine-gine, Ina wayarwa da dalibai kai game da girgizar kasa da matakan baiwa kai kariya, yadda gine-gine masu tsaro suke, da takardun da ake bukata daga masu gidaje, kamar takardun tabbatar da gini na da karfin bijirewa girgizar kasa." in ji :Labaran.

Aliyu Jigawa ma na cikin zauren na sada zumunta na daliban Afirka da ke Tukiyya.

"Mai kula da zauren na aiki sosai don sanar da kowa wani sabon bayani da aka samu. Ana yin hakan don taimaka wa wajen isar da sakonni, musamman ga sabbin zuwa da ba si iya yaren Turkanci ba," in ji Jigawa.

Ibtila'in da ya shafi kowa

Tunawa da ibtila'in bayan shekaru biyu, mazauna garuruwan da lamarin ya shafa sun taru da misalin karfe 4:17 na daren Alhamis don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu. An gudanar da tattaki cikin shiru a garuruwa da dama.

An gudanar da tattaki cikin shiru a daya daga cikin garuruwan da ibtila'in ya afku . Photo: AA

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa mutane 53,537 ne suka mutu a girgizar kasar.

"Tun daga farkon faruwar lamarin, mun hade kan mu a matsayin tsintsiya daya madaurinki daya, muna cewa 'A dunkule muke', kuma ba mu taba janye goyon bayan da muke baiwa yankunan da lamarin ya shafa," in ji shi, yana mai alkawarin ci gaba da gina yankunan har sai kowane dan kasa ya samu gidansa."

Labaran ya so halartar lacca da Kungiyar Daliban Afirka a Gaziantep ta shirya a matsayin wani bangare na tuna wa da ranar.

"Manufar ita ce a saukaka sadarwa a tsakanin daliban kasashen waje a lokutan bukatar gaggawa," in ji shi.

"Mun shirya assasa wannan tsari sannan mu zama masu jajircewa har ma bayan mun kammala mun koma kasashenmu."

Labaran na taimaka wa dalibai sabbin zuwa wajen saba da sabon muhallinsu. Hoto: Labaran

Har yanzu Jigawa na tuna girgizar kasar. "Lamari ne mai rikitarwa, wand aba zan iya bayyana wa da baki ba. Amma ina musu addu'a a ko yaushe (wadanda lamarin ya rutsa da su), kuma ina yaba wa kasar Turkiyya, musamman yadda na tana taimaka wa mutane don su ci gaba da iyalansu."

A yayin da suke cin abinci a dakin dafa abinci, Labaran ya tashi tare da yin addu'a, sannan kowa ya yi shiru tare da tuna wa da mamatan.

"Yana da wahala a fama da ciwo, amma wannan ibtila'i ya bayar da damar yaba wa rayuwa sosai." in ji Labaran.

TRT Afrika