Daga Coletta Wanjohi
Ƙasashen Afirka da ke halartar taron diflomasiyya na duniya, na Antalya Diplomacy Forum wanda ake yi a Turkiyya, sun nemi samar da ƙarin dabarun diflomasiyya domin shawo kan rikice-rikicen da duniya ke fama da su.
“Diflomasiyya na da matukar muhimmanci ga kasashenmu,” in ji Leonard Boiyo, jakadan Kenya a Turkiyya da yake magana da TRT Afrika.
Boiyi ya kara da cewa, “Kenya tana taka rawa daban-daban a diflomasiyya, mun taimaka tsawon lokaci a yankinmu da ma duniya. Mun ba da taimako wajen wanzar da zaman lafiya saboda Kenya aka dora wa jagorancin tawagar kasashen masu tallafa wa Haiti kan tsaro”.
Taron Antalya Diplomacy Forum, wanda ke gudana shekara-shekara, a bana jigonsa shi ne: “Inganta Diflomasiyya a Lokacin Hargitsi.”
Taron wani fage ne da kasashen duniya ke tattaunawa ta keke-da-keke kan batutuwan da suka shafi cigabansu. Wannan shi ne karo na uku da ake gudanar da shi.
Ministan harkokin waje na Namibiya, Peya Mushelenga ya ce, "Idan muna magana kan kayan more rayuwa, ko ilimi da cigaban fasaha, yayin da mutane ke rayuwa a kangin talauci, hakan ba zai yi ma'ana ba".
Sudan ta Kudu ta janyo hankali kan amfani da takunkumi kan kasashe masu tasowa, inda ta ce hakan yana tauye damarsu ta cigaba.
Ministan harkokin waje na Sudan ta Kudu, James Morgan ya fada wa TRT Afrika cewa, “Akwai wasu cibiyoyi da ke da burin kakaba takunkumi kuma suna amfani da Majalisar Dinkin Duniya”.
A watan Mayun 2023, Majalisar Dinkin Duniya ta kara wa'adin takunkumi kan Sudan ta Kudu da shekara guda. Hakan ya hada da rike kadarorinta, da hana tafiye-tafiye ga wasu jami'an kasar, da hana sayar mata da makamai.
Sudan ta Kudu ta dora alhakin kasa samun cigaba kan irin wadannan takunkumi da aka kakaba mata.
Morgan ya kara da cewa, “A wajenmu muna ganin ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta kawo wadata ga duniya saboda dalilin kafa ta kenan. Ta'annatin yaki Duniya na Biyu shi zai tuna wa Majalisar cewa an kafa ta ne don kiyaye zaman lafiya a duniya".
Ita ma Sudan, wadda ke fama da yakin basasa tun Afrilun 2023, ta tabbatar wa mahalarta taron cewa za ta kawo karshen barin wuta a kasar.
Fada tsakanin rundunar sojin Sudan da rundunar tallafin gaggawa ta Sudan ya haifar da gagarumin yakin da ya tilasta wa kusan mutane miliyan takwas barin gidajensu.
Kusan 'yan gudun hijira miliyan 1.5 sun nemi mafaka a kasashe makota, kamar Chadi, Masar da Sudan ta Kudu.
Minista Ali Elsadig ya ce, "Har yanzu muna da aniyar kawo zaman lafiya. Yaki ba zai kawo mana komai ba. Na yi amanna da taken wannan taron, cewa diflomasiyya ita ce mafi alfanu".
Taron ya bayyana bukatar hada karfi da karfe wajen tunkarar matsalolin tsaro.
Verónica Nataniel Macamo Dlhovo, ministar harkokin waje ta Mozambique ta ce, "Ta'addanci ba batu ne da ya takaita ga Afirka ba, matsala ce ta duka duniya. Idan muna so mu shawo kan lamarin dole mu yi hakan a duniyance; idan ba haka ba, to ba za mu yi nasara ba."
Bineta Diop jakadar Tarayyar Afirka ta musamman kan zaman lafiya da mata da tsaro ta fada wa TRT Afrika cewa, “Akwai tarin rikice-rikice a duniya, a Ukraine, da Falasdinu, amma a cikin nahiyar Afirka muna da namu kalubalen”.
Diop ta kara da cewa, “Babbar tambayar ita ce ta yaya mata za su ba da tallafinsu? Wannan batu muna tattauna shi a nan Antalya. Don haka roƙona shi ne mu ɗauki mataki na bai-ɗaya don ganin mun cimma burinmu".
Diop ta bayar da shawarar kowace ƙasa ta ɗauki wani ma'auni da za ta duba da kanta don gani ta cimma kyawawan manufofin da aka tattauna a taron na Antalya Diplomacy Forum.
Ta kuma fada wa TRT Afrika cewa, “Ya wajaba mu auna kanmu don duba abinda kowannenmu yake don tabbatar da muna inganta rayuwar mata da zaman lafiya da tsaro, sannan mu ba da rahoton cigaban da muke samu."
“A wajena, taron Antalya taro ne mai alfanu, a badi ya kamata mu yi waiwaye kan abin da muka cim ma.”